1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » Kaine Sirri Na Part 1

Kaine Sirri Na Part 1

By Abdul Mk
Add Comment
Wednesday, 7 September 2016


Ahankali nake tafiya cikin wani babban wuri wanda aka radama suna THE ATTORNEY ‘S WORLD. Office din lawyoyi ne sunfi dari aciki,an kawata su da fulawowi da wasu irin madubai da wutan lantarki masu kyau daban shaawa, koni m shakur na shigo wurin ne Dan neman lawyer dazan bude company a wurin shi. Tafiya na cigaba dayi harna kai gaban wani office sai naji ana hayaniya dariya nadanyi nace nafasa bude kampanin dole na daukoma matsoyana wanga rahoto lol.
Bismillahi Rahmanir Raheem.
“RA’AYINA ne MUZZAMIL bazan auri wacce batai graduating ba,bazan auri under graduate ha, nafison na auri wacce ta gama school,ta waye, duk inda zan shiga zan iya zuwa da ita batare dajin ko darr araina ba”…da sauri dayan ya tari numfashin shi yace “B maisa kakeda tsatsauran RA’AYI? Kaga niko Kullum burina na auri yar sacandari, wacce zan koyamata komi,soyayya,girmamawa, biyayya, tsorona everything B,duk yanda naso tayi zatayi,zan lankawasa na tankwara ta zuwa kowani position danaga dama, kai mesa ka banbanta da sauran mutane?” Dan murmushi B yayi yace “RA’ AYINA kenan”, daukan  keys din motarshi dake kan table yayi ya dago yana gyara buturan gaban rigan shi daya bude idanunshi nakan bituran dayake makalawa  yace “dama na shigo ne nafada ma gobe zan shiga minna,Niger state, akwai wasu case danakeda shi akasa, 3 days zanyi in sha Allah”. Muzammil yadan zaro ido yace “garin da akai earthquake(girgizan kasa) jiya ne zaka?” Yakarasa maganan yana kallon B dake kokarin makala neck tie dinshi batare da wani damuwa akan fuskarshiba, Muzammil yace “badakai nake magana ba,earthquake akayi fa koyau saida nakara karantawa a news kuma daga  site wanda basa sa karya wato Vanguard news…” B ya dafe kanshi murya chan kasa yace “God!” Dago kanshi yayi ya kalli Muzammil yace “will you just listen to me, ba earthquake akayiba, Wani babban ginin bene ne ya rushe mutane 5 sun mutu Allah ya jikansu, Gobe nidai zanje nai abunda yakaini”  Muzammil yaraka shi har wurin mota, shiga motar yayi ya zauna zaro taba kwara daya yay ya makala a bakinshi, lighter ya dauko zai kunna yaji an fizge taban Muzammil yace “Allah nakusa fadama mum kanashan taba,kasan baida kyau amma kaitayi niba gashi nadena ba amma kai kaki”… B na ganin zai batamai rai yaja motan yay gaba batare daya ce mai komiba.
Su uku aka zakulo daga ginin daya rushe ayau ranan jumma’a, inda jiya aka samo biyar matattu,wurin gabaki daya bama ka iya ganin kona kusa dakai saboda kura dake tashi,sai kukan mutane kakeji wayanda yan uwansu suka mutu sakamakon rushewan da gidan benen yayi. Daya daga cikin Daktan da gwamnati ya kawo wurin dan bama wayanda sukaji rauni taimakon gaggawa. duba mutane ukun yayi wanda da alamu baba Mata da yarsu ne, ya dago ya kalli sauran yan uwanshi dasuka zageyeshi cikin rashin kuzari yace “parent din are already  dead yarinyar kuma ta bugu but tanadai rai, yanzu ai informing government mutane 7 suka mutu, wayanda suka samu injury 35 hade da yarinyar nan”.
Wani irin ihu yarinyar tasaki ta zabura tafado daga gadon, wurin iyayen nata tayi tana kuka sosai babu wanda yahanata zuwa inda suke, tsayawa tayi tana kallonsu idanunta sunyija sosai, tai shiru ganin haka likitan yabada umarni a wuce dasu asibiti inda ake ijiye gawawwaki idan aka nemo yan uwansu sai abasu suje su burne. Itakuma aka daurata kan gado ganin yanda jikinta ke rawa, aka bata magani sanan suka cigaba da duba sauran wayanda sukaji ciwo. saukowa tayi daga gado batare da kowa ya lura da itaba tafita daga barandan da gudu.
Gudu take iya karfinta tana share hawaye bata ganin na gabanta bata ganin na bayanta ita tadaisan tana daga kafa tana gudu iska na kadata kwakwalwar ta abu daya kawai take hango Mata lokacin da suke kan dining suna breakfast da Abba da Umma da ita, sai sukaji Kara sukaji ginin na rawa ji tayi Abban ya janyota ya turata cikin jikinshi ya daura bayanshi kan nata daganan saitaji jikin Abba yay Kara kaman ballewan kashi, ahankali ya furta laa’ilaha illallah, tadaiji nauyi sosai ajikinta takumaji abu nabin jikinta kaman ruwa, ihu ta dingayi tana neman taimako tana kiran umma harta sume. Saikuma yanzu data farfado taji Abba da Umma sun mutu. Kara gudu tayi na bala’i hawaye na tsiyaya daga idanunta Abba maisa baka bari ginin yafadomin ba nima dukanmu mu mutu tare Maisa? Kummmm kakeji tabugu dawani gini block tafadi a wurin sumammiya jini nafita daga goshinta.
washe gari*
11 na safiya tamai cikin garin Minna ahankali yake Jan motarshi ganin yakusa kaiwa inda zaije.  dan gajeren tsaki yaja awahale “mtswww” ya paka motar a gefen hanya,juyowa baya yay ya mika hannunshi yadauko goran ruwan polar water dake back seat, sanan yay amfani da dayan hannun ya bude motar yafita yafara waige-waige, wurin shiru babu mutane dayawa sai kwarori dake wucewa, tafiya kadan yayi ya shiga wata yar karaman hanya haka jikin wani dan gini inda yaga babu mai wucewa ya tsaya yay abunda zaiyi ya maida zip yaja sanan ya juyo zai koma wurin motarshi yaji alumun numfashin mutum, cigaba da tafiya yayi dan atunaninshi wani naman daji ne, kaman ance ya kalli kasan wurin saiya ga jini, tracing dige digen jinin ya dinga bi haryakai bakin  wani gini da anfara ba’a karasa ba, tsayawa yayi shi bai shiga ba shikuma bai juyaba waigawa ko ina yayi yaga babu kowa awurin yakara kallon kasan yadaiga ga jinin da alamun koma wanene yana cikin ginin, bismillah yayi ya shiga kai tsaye yafarabin sahun jinin harya kai bangon karshe, ganin mutum yay akwance shame shame baya ganin fuskan daga inda yake saidai yaga zanin atampa ajikinta, karasa wa yayi ya tsugunna gabanta yana kallonta sama da kasa, numfashi yaji tanayi ahankali awahale  hakan yasa yakai hannu ya juyo da ita yana mai karema fuskan ta kallo “Subhanallah” ya furta ganin yanda goshinta ke fitar da jini da sauri yasa hanunshi a aljihun wandon shi handki yaciro yadaura akan goshi yafara kallon ko ina ko akwai any clue dazai gane daga ina take Kokuma yan uwanta,ko waya kowani abu, dawo da idonshi kanta yayi jin tafara numfashin tana fito da harshe hakan yasa yagane ruwa takeso rike kanta yay yadau ruwan yana bata ahankali ta shanye tass sanan jikinta gabaki daya ya saki a hanunshi da sauri ya dagata yafito da ita daga wurin har bakin titi yasata cikin motarshi sanan yaja da sauri dan nemamata lpy, agaban wani babban hotel yay horn aka bude ya shiga ciki yay parking a wurin paka motoci wasu mutane uku dukansu maza kowananen su rike da wata yar karaman littafi a hannu suka budemai motan da sauri daya  daga  cikinsu yace “is already 12:PM, and case din damuke dashi 12:10 za’a shiga” Fuzar da iska yayi ya dafe kanshi batare dayace komiba, daya daga cikinsu yace ” your breakfast is ready ” da sauri na ukun yace ” you have visitors sir” gajeren tsaki yasaki yay gaba, sai kuma yajuyo akasalance yace ” akawai yarinya a mota, Johnson take her inside,and u Solomon ka kira Dr ya dubata” yajuya  yahau bene, dakin da aka tanada mussamman saboda duk lokacin daya sauka ya shiga direct bayi yaje yay wanka ya chanza kaya suwa suit baki da wandon shi sai takalmin min baki cover mai sheki, ya cire tabaran idonshi da ruwan wanka ya tsalla akanshi ya goge ya mayar, ya fesa designers turare mai suna  kingdoms ya mike tsaye ya daura necktie sanan yafito daga dakin. dakin dake kusa da nashi ya shiga yaga Dr Faruk yana dubata, kallon agogon hanunshi yayi sanan ya kalli Dr Faruk yace “am late, anjima I will see yhu” ya bude kofa yasakai yafita saikuma ya juyo kallon fuskan yarinyar yayi nadan tsawon sakonni sanan yasakai yafita daga dakin P.A na binshi abaya da jakan laptop dawasu takardu a hanunshi.
Karfe 4 na yamma yagama abunda zaiyi shida P.A a high Court na Minna suka fito, saida yay sallan la’asar sanan suka dauko hanyar gida. yay wanka ya chanza kaya zuwa na Shan iska ya zaro taba yana zuka anishadan ce wakan awww na tashi, idanunshi a lumshe yaji anyi knocking bude idonshi yayi sanan yabada izinin shigowa P.A ne ya shigo yace “kanada baki sir, tunna dazu ne basu tafiba” wani kallo yama P.A tareda busar da hayakin taban sanan yace ” waiba nace karku fadama kowa zan zo Minna ba, cases dake kaina are enough, banason anymore wahala” da sauri P.A yace “ka gafarce ni, wasu couple s ne for d past one month sukeson ganinka kullum suna kira nace musu bakanan, saisa nafada musu yanzu kazo”  batare daya kalleshi ba yace “sujira ni, ina zuwa”, saida yagama Shan taban sanan ya mike yadau lemon mint yajefa abaki, yafito zuwa  office dinshi nacikin hotel din yabada izinin ashigo  dasu, yana zaune aka bude kofa aka shigo Babban magidan cine  da matarshi  fara kakkyawa mai kama da balarabiya, da sauri ya mike ya mikama mutumin hannu suka gaisa ya nuna musu kujera suka zauna Alhajin yay magana da murmushi yace “BARRISTER BARRAQ,tun randa mukaga firan da akayi dakai a African independent television (AIT) my wife here, ya nuna hajiya tace dole mune meka,kallo daya mukaima mukasan kanada gaskiya, kallo daya mukaima mukasan zamu iya fadama matsalan mu,haka kuma kaji kakuma taimaka mana, kanadaga cikin lawyoyin kasar Nigeria masu tsayawa kan gaskiya,da bima talakawa hakkinsu ga yawon taimako,kafin mu sanka muke jinka da alkhairan ka ga jama’a” yakarasa maganan yana kallon fuskan B da kanshi ke kasa baka gane yanayin dayake ciki, Alhaji ya cigaba ” yace aranan ashirin ga wata agusta ta shekara 2015 muka wayi gari bamuga yarmu tilo maisuna RUFAIDA ba,munsan agidan ta kwana tare mukaci abincin dare komi tare amma muna tashi bamu gantaba, saidai mukaga dakin ta abude da alamun tafita, tundaga ranan babu inda bamu shiga nemanta ba, mun sanar a kafafan sanar wa amma babu ita babu alamunta gashi shekara na neman tafiya batare da munga yarmu ba har polisawa mun sanar mawa amma shiru,tunda mukaji kana Minna yasa mukataho tundaga legas dan sanar dakai komi” Matar da idonta yaciko da kwalla tace “Barrister shekaran yata 16 kacal a duniya,dan Allah ka taimake mu ka nemo mana ita”  takarasa maganan bakinta na rawa, B ya sauke ajiyan zuciya yace “am sorry but aikin polisawa ne neman wanda yabata baniba… Da sauri matar tace “Barrister ni nasan wani abu akaima yata amma Alhaji yaki yarda,inaji ajikina wlh batun yauba dan Rufaida banda makaran babu inda take zuwa”, Alhaji ya kalleta yace “zaki farako” tafashe da kuka sosai B ya saukar da kanshi kasa dan ya tsani yaga manya na kuka, Alhaji yace ” Barrister wato tanada abokiyan zama ne,sai jiya taji abokiyan zaman tana waya tana fadin suda ganinta har abada wlh tariga ta shiga duniya kaman yanda tsuntsun ya shiga duniya… Shine fa tunda taji take cewa itace tama yarta wani abu ta bace” B yadade yana nazarin zancen, daga bisani ya kalle matar yarasa dawani suna zai kirata sai kawai yace “Umma” ta dago tace “naam Dana” yace “zanyi nazari,zan kuma nemeku akaro na biyu in sha Allah yarku takusa bayyana”, ya yagi wata paper yace “gashi komi kan yarku Ku rubutamin, nadaga shekarun ta, yanayin ta,makaran ta datayi kawayen ta dadai komi” Alhaji shiya rubuta sanan yabashi ya karba, Alhaji ya yaga check yarubuta kudi mai yawa ya mika mai B ya girgiza kai yace “ganinta shine farko kafin payment Alhaji nabarku lpy” yarakasu suka shiga mota matar nata godemai tana yaba halinshi na kirki saida sukabar haraban hotel din sanan yakoma ciki, dakin yarinyar daya tsinta ya wuce kai tsaye dan duba lafiyarta.
Tsayawa yayi akanta yana kallonta, ansa mata Karin ruwa ga  bandeji a goshi, sai ciwukan jikin ta da hanunta an wanke su,tai wani fayau da ita tai haske kaman Mara jini. Murmushi yadanyi tunawa da duk inbaida lafiya Mum na zama taita Karanta mishi English novels masu dadi tun yana Yaro,duk in yatambayeta maisa takeyi mai haka in baida lafiya, saita cema Karanta ma Mara lafiya stories yana sa ya warke da wuri. Murmushi yadan karayi yace ” O mother I missed yhu dayawa dayawa” yace “nima bari na karantama dis little lady stories, yadan tabe baki yace who knows maybe itama ta warke da wuri takoma wurin iyayenta dan anywhere dey are suna nemanta suma” yajuya dan zuwa dakinshi ya dauko novel ya karanta ma yarinyar haryasa hannu zai bude kofa yafita yaji tana magana” Mami tsuntsun mai dago baki yana Jana,zai tafi…Mami dani zai tafi…Mamina “.
Dawowa cikin dakin yay ya tsaya gaban gadon, addu’oi ya tofa mata saiyaji tai shiru ta sauke ijiyan zuciya ta cigaba da bacci. Ya tsaya akanta nadan sakonni  sanan ya juya yabar dakin. ya dauko novel yana karanta mata a natse.
Karfe 10 na safiyan washegarin ta farka da addu’a a bakinta,ahankali take bude ido bataga kowa a dakin ba, sai wani bakin akwati a gefen gadon,da katon littafi akan drawer, mikewa tayi tadan zauna dudda batajin karfi ko daya a jikinta tana karema dakin kallo komi pink. ruwan dataga yanabin hanunta ta cizge tareda wata yar Kara “wayyo umma zafi” fadin sunan Umma yasa ta tuna da sun rasu fa yanzu, ta fashe da matsanancin kuka.
Tsagaitawa tai da kukan tafara  kalle-kallen dakin “to ina nake? Inane nan?wanan hadadden daki fa?” Dakyar ta tashi tsaye taje gaban kofan data gani tana jijjigawa amma taji arufe bayama girgiza,zama tayi a wurin ta dasa sabon kuka na rashin iyayenta,masu sonta,masu walahan neman kudi dan suga tai karatu,wayanda suka mutu ta sanadiyya ta tafashe da wani kukan toni maisa ban mutuba, banda kowa banda DUDUWA.
Haka tacigaba da kuka sai Wuraren sha biyu sanan ta share hawayen, ta mike tsaye tana neman makewaya dan fitsari takeji sosai, ganin wani kofa yasa tafada ciki takoga bayine batasha wahalan bude shawan ba saboda inda Abba yasamu aiki irin bayinne a wurin, wanka tayi tai brush ta wanke kayan data cire, sanan ta daura sabon towel din data gani tafito tana dingisawa, akwatin kayan data gani gefen gadon tabude, kaya tagani aciki kala biyu da hijabi baki,  daguwan rigan ciki ta dauka tasa tadau hijabin tasa ta kabbara salla, da kyar take sallan saboda jirin datake gani, tana idarwa ta tashi zata koma gado, saidai tana mikewa ta zube a tsakar dakin saboda jirin daya dibeta, adaidai lokacin ya bude dakin da sauri ya shigo yana sanye da kayan Shan iska yakaraso da ya dagata ya daurata kan gado. Juyo da fuskanta tayi dan taga Wanda taji yadaga ta, idanuwanta suka sauka kan kakkyawan namiji, shiba saurayi ba shikuma ba Babban mutum ba,farine tarr kana ganinshi kasan akwai jinin bature tattare dashi,idanunshi dauke da farin glas maikama Dana masu ciwon ido.
Dago kanshi keda wuya sai idanunsu suka hade,  kulle idonta tayi da sauri ta kankame jikinta ganin yanda yacika mata ido,dakuma yanda kwayar idonshi ke bata tsoro.
Baice mata komiba,ya komar da kanshi ga wayan dayake dannawa. Bude kofa taji anyi, saikuma taji ance thanks Johnson, saitakara jin an bude kofa anfita. kara kankame jikinta da idanunta tayi dan tsoron shi taji Allah ya saukar mata shikenan gidan yan yankan kai!  Cikin natsatsiyar murya taji ance “tashi kici abinci”, ko motsi batayi ba, takarayin lamo, ahankali yakai hanunshi bakin katifar yadan bubbuga ” Hi tashi kici abinci ” da sauri ta tashi zaune ta bude idanunta ahankali ganin abinci tayi agabanta mai rai da lafiya,tea mai kauri saikuma faten wake dake dauke da hanta da green vegetable  sai aka zuba soyayyen plantain a sama,Satan kallonshi tadanyi taga news paper yake Karantawa.  zamo jikinta tayi ta zauna akasa dan ita ko agida saidai Umma a Abba su zauna a dining ita akasa takeci, data zauna ta sauko da Trey din abincin a gabanta, tadau tea din tafara sha harta shanye tass, sanan ta jawo faten waken tana wasa dashi, tun tana yar karama batacin wake, sai kallon waken take ita bataci ba ita batai magana ba,bude kofa taji anyi an shigo yace “gani sir” batareda ya kalleshi ba yace “take d Beans away,ka kawo mata wani abinci batacin beans” da sauri ta kalleshi saikuma ta sauke kanta tana mamaki ya akayi yasan batacin wake?
Shinkafa Johnson ya kawo mata ta karba tadanci kadan tasha ruwa ta tura gefe taci gaba da wasa da yatsunta. kaman daga sama taji yace” kina bukatan wani abu kuma” girgiza mai kai tayi, bai Kara cemata komiba yacigaba da karatun news paper dayake yi.
Karfe 6 ya linke newspaper ya kalleta yaga har yanzu tana zaune a kasa da zumbulelen hijabin tai wani iri kaman marainiya, tausayi kawai yaji tabashi yakaraso gaban gadon ya tsugunna kusa da ita da sauri ta kulle idonta gam, dan murmushi yayi sanan yace “ya sunanki?” Batace komiba, akaro na biyu yace “bude idonki” ahankali take budesu tadan kalleshi ganin ita yake kallo yasa ta kauda kanta ta kalli gefe, hannunshi ya daura akanta ya juyo da fuskanta suka fuskanci juna yace”I said ya sunanki?”
Kukan datake kokarin hadiyewa ya kufce mata ta fashe da kuka sosai ko ina na  jikinta na rawa,ganin haka yasa yacire hanunshi daga kanta yadan ja baya. a natse yay magana ganin ta tsorata dashine”Hi am not going to hurt yhu, taimakon ki zanyi karki tsorata dani kinji? dazaran kin warware zan maidake,don’t be afraid of me” shiru yadanyi ganin ta tsagaita kukan tana share jajayen idanunta tana kallonshi adan firgice,yakara kwantar da murya irin na lallaba wanda ya tsorata yace ” ki kwantar da hankalin ki kinji,zanje masallaci kinason na siyo miki wani idan zan dawo?” Ta girgiza kai tana share hawaye, yace “ok,oya tashi kije kiyi sallan kema” da sauri ta mike kaman jira take tayi hanyar bathroom tana kallonshi kaman zaibita kumm! ta bige kanta da kofan bayi garin kallonshi rike goshin tayi ta shiga bayi da sauri ta Danna key. Girgiza kanshi yay yatashi yafita daga dakin.
Bayan sallan isha ya bude kofa ya shigo dakin tana zaune kan dadduma da sauri ta mike tsaye ta make ajikin bango, ajiye abunda ya shigo dashi yayi yajuya yafita daga dakin. sauke ajiyan zuciya tayi sanan tacire hijabin jikinta ta zauna abakin gado ta bude ledan, lemun kwali ne da kaza,dayan ledan kuma chocolates ne da cingums, ajiyesu kawai tayi tafada kan gadon ita kadai tasan yanda takeji.
Kwananta uku tana jinya harta warke tai ras,tsawon kwana ukun nan magana baitaba hadata da mai gilashi ba( sunan data rada mishi) saidai abunda tagane game dashi “mutum ne mai tausayi gashi da lallaba Mara lpy, kullum haka yake riritata yana tambayan metakeso yakawo mata,kayan kwalama kala kala yake kawo mata kaman baby, amma bazata taba bashi amsaba, yacika tausayi danta lura ya tsani yaga tana kuka. Itadai har yanzu mai gilashi tsoro yake bata saisa ko eh bai taba hadata dashiba baitabajin ya muryarta takeba”.
Tana cikin tunani taji anbude kofa, da sauri ta gyara hijabin jikinta, kallonta yadan yi wani abu yadan gitta zuciyarshi me yar yarinyar nan ke nufi? Maisa duk lokacin dazata  ganni sai tawani sa hijabi? Mezanyi da ita? Mezan gani? Metake dashi? Abun yadan batamai rai amma saiya basar yakaraso ya zauna akan kujera.  kanta na kasa yace ” petient naga kin warke ko?” Ta girgiza kai,yace “to Alhamdulillah, inaso nasa a komar dake gidanku ne dama  saboda nasan duk inda iyayenki suke suna neman ki, and also maiya faru dake harna ganki a wurin nan a sume?”
Dago kai tayi zatai magana saitaga ita yake kallo. kaman kullum jikinta yahau bari ta fashe da kuka, kuma takasa daina kallonshi, mamaki take bashi wai yarinyar nan is she alright, anya batada matsala, da sauri yadan ja kujeran shi ya matso kusa da gadon ahankali yace “ke kurma ce?”  Da sauri ta dagamai kai, tausayin ta yaji sosai yace “to ai basaikinyi kuka ba idan namiki magana kinji?”  ta girgiza kai, yace “to share hawayen ki” ta share da gefen hijabin jikinta, “Kinyi iya rubutu?” Yakara jefo mata wani tambayan, ta girgiza kai alamun eh. mika mata byro da memo yayi “rubutamin inda iyayenki suke” kallonshi tayi ta kalli memo dayake mika mata da fararen hanunshi, kasa karba tayi, ganin haka yasa ya ajiye mata akan cinya “oya rubutamin na Karanta” ahankali tadau memo tafara rubutu kaman haka
    “Abba na da umma na sun ra..
Kasa karasawa tayi ta kifa kanta a book din tafara kuka dan mutuwar takara dawo mata, tashi yayi ya daga kanta ya zari memo ya karanta sanan ya kalleta yace “sun rasu??” Dagamai kai tayi cikin kuka, yakara jefo wani tambayan “ance wani gida ya rushe mutane sun mutu dayawa kune,iyayenki na cikine?” Da sauri ta girgiza mai kai,  “dis morning naji a news ana neman wai young lady iyayenta sun mutu amma ita an nemeta an rasa,cos gamnati nason bata tallafi,kece yarinyar?” Ta girgiza kai cikin kuka,  dafe kanshi yadanyi sanan ya zauna akan gadon ya dago kanta yakai hanunshi ya share mata hawayen “is OK,in sha Allah nai alkawarin I will help yhu  kinji” ta dagamai kai tareda matsawa baya. “Kinada yan uw… Bai karasa maganan ba saboda jin ana knocking, bada izinin shigowa yay Johnson ya shigo Sir kanada bakuwa? Yace waye?  Is Nana sir” dan karamin tsaki yayi yace ina zuwa ”
Baikara cewa komiba, yay shiru tadan kalleshi taga kaman ranshi abace yake hakan yasa takara makewa a jikin gadon, kusan minti 5 sanan ya mike ya kalleta idan kinason zuwa waje kisha iska dakina shine agaban naki ki shigo kifada min zansa akaiki yajuya yafita.
Shiga dakinshi yayi ya mugun daure fuska ganin wacce ke tsaye cikin wani arnen kaya wanda dashi gwara babu, kakkyawar budurwa ce ajin karshe,tana zaune kan gadonshi.
“u again!  Nana maiya kawoki wurina? Nafada miki stay away 4rm me”Fari tayi da ido ta langabar dakai “haba My B,maisa kakemin wulakanci dan kaga kanada kyau na mutu a kanka,ina sonka?” Tsaki yay yadafe kanshi kafin yadago yace “kitashi ki fita, get out kafin nakira securities su fitarmin dake” kada kai tayi “ok shikenan inkasan wata bakasan wataba, kakosan wacece mac.. “I said get out Nana” ya daka mata razanan nan tsawa batare da yabari ta gama magana ba.  mikewa tsaye tayi tana kadamai jiki da kayan dasuka mugun matseta, matsawa gefe yayi dan ta wuce, saida tazo daidai kusa dashi cikin kyaftawan ido batare daya luraba yaji ta zare glass din idonshi, tasa cikin jaka da sauri takoma gefe tana dariya.
Cikin fushi yace “kiban glas dina,wai wot is ur problem Nana” “ai wlh My B kafin nabar dakinan saina tabbatar nadau cikinka Kota yayane sai Inga idan ka isa kace bazaka aureniba bancin inada cikin ka”  ahankali yake daga kafa yana mika hannu kokarin shi shine ya gano saitin datake magana, dariya tayi ciki ciki ta koma gefe tana cire kayan jikinta.
Masu karatu makaho ne wai?ko matsalan ido gareshi?

                  7
Ya dakamata tsawa Nana! “Kiban glass kafin na saba miki wlh,nace kiba..”bai karasa maganan ba saboda jin bakinta acikin nashi tana wani shasshafa bayanshi, jikinshi yaji yamutu yakasa tureta, yakasa aiwatar da komi. yana kokarin magana takara tusa harshenta cikin nashi…
Ahankali take tura kofan dakin  tanadan hawaye, yatsanta na jini saboda yankewan datayi da nail cutter dabata taba ganin irinshiba. Shiganta dakin keda wuya tasaki wani razanannen ihu wanda saida yasasu firgicewa Nana tasakeshi da sauri tana kokarin jawo abu tarufe jikinta, ihu tacigaba dayi ta kukkulle ido dan ita bata taba ganin mace ba kaya a jikinta ba. Nana takoma baya dan kallon aljana take mata dan bataji alaman shigowan mutum ba saidai ihu, Barraq ne yadan tattaro karfin magana yace “ban eyeglasses dina” da sauri Nana ta dauko jakanta taciro glass din jikinta na rawa ta sakamai a hannu, sawa yayi  yajuyo yana kallon yanda take ihu ta kulle idanu tsugunawa a gabanta yayi yace” lafiya ” Kara fasa ihu tayi tana cukuikuye hijabin jikinta tana Kara matsawa jikin garu, ganin kaman ta zare yasa ya juyo da kanshi ya kalli Nana datake tsaye tana kallonsu kauda kanshi yay yace “malama kisa kaya kificemin daga daki,believe me inna dawo na ganki u will see my other part” ya tashi ya dagata chak yafita da ita daga dakin, Kara kurma ihu tayi tana wunsula kafa ya bude dakinta ya wurgata kan gado tacigaba da ihu. ” keep quiet! Ya dakamata tsawa Idanunshi sukai jajir “one more ihu saina zaneki wlh, spoiled brat” ya fice daga dakin tareda bugo kofan yakoma dakinshi dancin uban Nana, saidai yaga batanan tariga ta tafi, zama yay gefen gado ya zaro taba ya kunna yafara zuka saida yasha Kara 4 sanan yaji bacin ran dayake ciki yaragu, bayi ya shiga yakarayin wani wanka yasake kaya.
Wayanshi tayi Kara ganin sunan mai kiran yasa ya dau wayan da sauri tareda zama akan kujera.
” Barrister Barraq! I just got ur email, so yanzu yarinyar natare dakai?” Ya amsa “eh tana tareda ni,u can come over ka ganta,badai tagama warkewa bane,tunda tamin bayani itace wacce parent dinta suka rasu shine nace is better na sanar daku dan adaina nemanta,but plan dina sir zan riketa I will train her and sponsor her education, inajinta kaman sister na,zanyi signing everything gobe inmun hadu a Court, tadawo under my custody,mace ce abu kadan ne zai iya lalata mata rayuwa,idan ban dauketaba bansan ina gawmnati zata turataba,orphanage?gidan marayu? Who knows, zan dauketa kawai” dayan yace “ok,I trust yhu Barisster, nasan u will take good care of her,come over later ka karbi kudin da government yabata” Barisster yadan yamutse fuska “no need of dat sir inada enough money dazan kula da ita” Minister yace “but still gawmnati yabata,kazo ka karban mata is her right” Barisster yace “ok,anjima zanzo na karba, thank yhu sir,I appreciate”
Tashi yayi yadau 1st aid box yafito ya wuce dakinta ganinta yay zaune kan gadon, tana ganinshi taja baya, baice mata komiba dan yasan yanda taganshi da Nana ne yajawo haka, “ban yatsan” Kalmar daya fada kenan, ahankali ta mika mishi tana matsar kwalla  sai alokacin yagama karamin ciwone, yadan wanke jinin sanan yace “dena kukan ki kwanta kiyi bacci” kwanciya tayi ta lumshe ido shikuma yakoma kan sofa ya zauna yana karanta newspaper.
Ajiye newspaper yayi ya dafe kanshi yana cije lips, kwata kwata ya rasa natsuwarshi,Nana ta dagulamai lissafi tsaki yayi yazaro taba daga aljihun rigan dayasa ya kunna yafara zuka. Jin warin taba yasa ta bude ido ta juyo da kanta da kalleshi gabanta yay mummunan faduwa ganin yanda yakeshan taba, lumshe ido tayi tana maganan zuci na shiga uku,wlh bazan kwana anan ba yau,gwara na koma wurin Duduwa koda kasheni zatayi, wanan mutumin dan iskane, malam ma yace Annabi yahana zaman mace tareda namijin daba muharraminta ba a wurin daya. wayyo umma na maisa kuka mutu? Yanzu waye zaitaba rikeni?? hawaye take sharewa tana tausayin rayuwar ta, jin anbude kofa yasa ta juyo da kanta taga fita yayi.
Daki yakoma ya chanza kaya zuwa suit mai ruwon toka ya fashe jikinshi da turare yafita yaja mota zuwa gidan Minister.
kallon kujeran daya tashi tayi taga wallet dinshi akan kujeran daya tashi, ahankali ta mike tsaye tana gyara hijabin jikinta takarasa wurin wallet din ta dauka hanunta na rawa budewa tayi taga yan dubu dubu ne sababbi hannu ta rawa yafara  da kyar ta iyakai hannu ta zaro dubu daya guda biyu ta maida ta ajiye jikinta na rawa tajuya tafita daga dakin da gudu, waige-waige tafara dan batasan hanyaba bene ta hango tai gudu tabi benen har ta sauka kasa tafito compound din sai alokacin tagane hotel ne danga sunan anrubuta Barraq’s aroyal hotel. Saidai inda tafito taga bangarene daban da fannin hotel din, gate tabi tafita da gudu tana share hawaye “dan Allah kayakuri, in sha Allah zan biyaka kudinka,wlh bana sata,niba barauniya bace, bazan iya zama da dan iskaba” takara gudu dan taji anfara kiraye kirayen  mangariba,  tana kaiwa titi ta tare adaidaita ta shiga wuf yace “malama ina za’a kaiki?”tace “tashan shiga mota”.

Isansu tasha keda wuya tabiya mai adaidaita kudinshi dari biyu, sanan ta shiga motan daizai kaita garin Jigawa! Ta biya kudi 1500.
Kuka sosai take acikin mota tana tuna farkon ranan dasuka zo daga kauyen gunjugu itada Abba da Umma zuwa nan garin Minna, wai yanzu shikenan Abba da Umma sun tafi? Duniyar kenan cewar wani bangaren zuciyar ta,addua kawai zaki dinga musu. matar dake gefenta tace “lpy baiwar Allah  kike kuka?ko tsoron tafiyan dare kike?” Girgiza kai tayi tace “a’a Mama kaina ke ciwo”, “Allah sarki Allah sawake, ya sunanki?” Cewar matar, lumshe ido tayi tabude sanan tace sunana “RUFAIDA”!.
Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 19:30
In Hausa Novels
Kaine Sirri Na Part 1 Title : Kaine Sirri Na Part 1
Description : Ahankali nake tafiya cikin wani babban wuri wanda aka radama suna THE ATTORNEY ‘S WORLD. Office din lawyoyi ne sunfi dari aciki,an ka...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Kaine Sirri Na Part 1"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2026 (1)
    • ►  January (1)
  • ►  2025 (5)
    • ►  December (5)
  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ▼  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ▼  September (199)
      • Graphic Photos: Sojoji Sun Ceto Wasu Mata Da Aka Y...
      • An Damke Mahaifi Da Yima Diyar Sa Fyade
      • Mijin Haya Part 18
      • Photos: Sunlight Laraba's World Tv Drama Series Hu...
      • Photos: Sheik Isa Aliyu Pantami Ya Shiga Ofis A Yau
      • Buhari Ya Taya Zababben Gwamnan Edo Murna
      • Photos: Jami’an Tsaro Sun Kulle Ofishin Abdulmumin...
      • Dan Takarar Gwamnan Na APC A Jihar Edo Ya Lashe Zabe
      • Photos: An Haifi Wani Jariri Mai Kama Da Tsoho
      • Photos: Mutane Shida Sun Rasa Ransu A Wani Gidan K...
      • Abdulmumini Jibrin Ya Kai Kara Majalisa Wakilai Kotu
      • MIjin Haya Part 17
      • Majalisar Wakilai Ta Dakatar Da Abdulmumini Jibrin...
      • Kaine Sirri Na Part 23{END}
      • Photos: El Rufai Ya Sanya Danshi A Makarantar Gwam...
      • Al'ajabi: An haifi Jariri Mai Iyaye 3 A Kasar Mexico
      • Wani Yaro Dan Shekara 11 Yayi Fyade A Kasar Ingila
      • Mijim Haya Part 16
      • Buhari Ya Umarci Tambuwal Ya Sulhunta Tinibu Da O...
      • Kaine Sirri Na Part 22
      • Bankin Afirka Zai Tallafa Wa Najeriya Da $10b
      • Video: I LOVE YOU By CLASSIQ FT AVALA starring Rah...
      • Mijin Haya Part 15
      • Ban Yi Tsufa Da Auren Zahra Buhari Ba - Gwamnan Za...
      • Wani Kurma Ya Yi Fyade Wa 'Yar Wata Shida A Yobe
      • Na Hakura Da Mukamin Shugaba A Jam'iyyar APC. Bana...
      • Kaine Sirri Na Part 21
      • Kaine Sirri Na Part 20
      • Photos: Hanun Wani Matashi Ya Makale A Jikin Kur'a...
      • Photos: Sojojin Nijeriya Sun Kashe 'Yan Boko Haram...
      • Mijin Haya Part 14
      • Video: Rahma Sadau Ta Ziyarci India
      • Ina Nan Garau Da Raina - Abubakar Shekau
      • An Kashe Marubuci Da Yayi Ridda' a Jordan
      • Photos: Aisha Buhari Ta Ziyarci Ingila
      • Kaine Sirri Na Part 19
      • Wani Ma'aikacin EFCC Ya Karbi Cin Hancin Miliyan 15
      • MIjin Haya Part 13
      • Kaine Sirri Na Part 18
      • Photos:Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Wa Yarsa F...
      • Tsagerun Niger Delta Sun Kai Hari A Garin Bonny
      • Mijin Haya Part 12
      • [Daga Jama'a] Dalilai Goma (10) Da Yasa Nake Son A...
      • Kaine Sirri Na Part 17
      • ISIS Sun Hana Yan Kasar Iraqi Sa Rigar Kwallon Kaf...
      • Naga Rayuwa Part 2
      • Naga Rayuwa Part 1
      • Yar Amana Part 3
      • Yar Amana Part 2
      • Wani Lauya Yakai Karan BuhariI A Kotu
      • [New Music] KU TARE BURGU YA GUDU By RARARA
      • Gwamnoni Da Ministoci Sun Amince Da Sayar Da Kadar...
      • Mijin Haya Part 11
      • Photos: Sabin Hotunan Nafisat Abdullahi
      • Zan Siya Kungiyar Kwallon Kafan Arsenal Nan Da She...
      • Kaine Sirri Na Part 16
      • Wani Dan Aikin Turai Yar’adua Ya Sace Mata Naira M...
      • Sabuwar Girgizar Kasa Ta Sake Faruwa A Kaduna
      • Mijin Haya Part 10
      • Kaine Sirri Na Part 15
      • Photos:An Kama Wani Tsohon Na Shirin Lalata Da Wat...
      • Photos: Barayin Shanu Sunyi Hadari Da Shanun Da Su...
      • Mafarki A Lokacin Jinin Haila
      • Yar Amana part 1
      • MIjin Haya Part 9
      • Photos: Sarkin Kano Ya Halarci Taron Sulhu Na Duni...
      • Kaine Sirri Na Part 14
      • Photos: Aisha Yayin Bada Lacca A New York
      • Mijin Haya Part 8
      • Photos: Sabin Hotunan Sadiya Gyale
      • Photos: Yan Bindiga Sun Sace Wata Malama Makaranta...
      • Photos: Yau Ranar Murna Haihuwa Yar Sarkin Kano Sa...
      • Kaine Sirri Na Part 13
      • Buhari Ne Matsalar Kasar Najeriya - Ayo Fayose
      • Mijin Haya Part 7
      • Photos: An Nada Wata Budurwa A Matsayi Shugaban Ka...
      • Photos: Sabin Hotunan Jaruma Nollywood Tonto Dikeh
      • Ya Kamata A Haramtawa Barayin Gwamnati Shiga Harka...
      • 'Yar Najeriya Saheela Ibrahim Ta Shiga Sahun Matas...
      • Kaine Sirri Na Part 12
      • Graphic Photos:Anyi Rikici Tsakanin Matasa Da Yan ...
      • Photos: Halima Da Zahra Buhari Sun Halicci Wani Bi...
      • MIjin Haya Part 6
      • Ibrahim Shema Ya Mika Kansa Wa EFFC
      • Kaine Sirri Na Part 11
      • Saeed Nagudu Na Shirin Waka Da Wizkid
      • Fatima Part 1
      • Fatima Part 2
      • Photos: Sojojin Najeriaya Sun Mika Iyalan Boko Har...
      • Sojojin Nijar Da na Chadi Sunyi Nasara Akan Boko H...
      • Photos: Dangote Da Yarsa Halima A Bikin Ranar Murn...
      • Mijin Haya Part 5
      • Photos: Halima Atete Da Fati Nijar A Makka
      • Za A Yi Afuwa Da Tsagerun Niger Delta Sama Da Dubu...
      • Kaine Sirri Na Part 10
      • Photos: Ku Ga Babba Maciji Da Wani Mutum Ya Kashe ...
      • Mijin Haya Part 4
      • Photos: Yan Sanda Sun Cafke Yan Fashin Da Suka Yi ...
      • An Dakatar Da Limamin Masallacin Juma'a Na Sultan ...
      • Kaine Sirri Na Part 9
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • MAGANIN KARYA SIHIRI DA IZININ ALLAH
    TAMBAYA TA 1606 ********************* Assalamu alaikum, Malam barka da aiki ya hidima da mutane Allah ya saka muku da mafificin alkairi. ...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Yayin Da Ake Zanga-zanga Rundunar Ƴan Sanda Jihar Sunyi Nasara Cafke Sha...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Zanga-zanga A Bauchi-Gwamnatin Ta Saka Dokar Hana Fita Da Zirga-Zirga Ac...
  • The Missing seven-year-old boy found dead in Kano
    Seven-year-old Khalifa Saminu Saleh was tragically found deceased six days after he was reported missing in the Kuruma community...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger