1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » Mijin Haya Part 18

Mijin Haya Part 18

By Abdul Mk
Add Comment
Friday, 30 September 2016
Bilal ya juya ya dubeta da kyau ,amma ya kasa cewa komai ya kad'a kansa a sanyaye ya fice daga d'akin... * * * a bangaren meera a daren jiya ta raya darenta da salloli,ta kai kukanta ga Allah bisa wnn lamari in har aurenta da bilal akwai alkhairi toh Allah ya tabbatar da hakan,in kuma akasin hakane toh Allah ya tarwatsa lamarin ya kuma za6a mata mafi alkhaira bangaren meera a daren jiya ta raya darenta da salloli,ta kai kukanta ga Allah bisa wnn lamari in har aurenta da bilal akwai alkhairi toh Allah ya tabbatar da hakan,in kuma akasin hakane toh Allah ya tarwatsa lamarin ya kuma za6a mata mafi alkhairi! Misalin karfe 7:00am meera ta fito daga wanka zuciyarta fes,ta shirya cikin wani material,tayi light make up,a kitchen ta tadda umma ,bayan sun gama kamalla had'a breakfast sun jera a dinning,alhaji ya fito shima ya samesu a dinning ,suka hadu sukayi b/fst ,bayan meera ta kwashe kwanukan ta wanke,ta dawo ta samu iyayenta a falo,gefen abba taje ta zauna ,kanta a sunkuye,abba ya dubeta fuskarsa dauke da murmushi yace 'ameera lafia,meyafaru' ,meera tayi jim tare karanto addu'oi a ranta sannan tace 'abba na samu mijin aure,kuma yana son a bashi dama ya turo magabatansa','toh toh masha Allah,wanene shi,d'an gidan waye,kuma aikin me yake?' alhj ya tmby ,meera kanta a sunkuye ta tattaro kalamai da kyar tace 'bilal ne ,maigadin gidannan' ,umma me zatayi in ba salati ba tana tafa hannaye tace 'ameera ! Bilal mai gadi zaki aura ,wato mijin hibbatu,wannan i cin amana ne da tsantsar son kai,haba ameera me hibbatu ta tare maki da zaki saka mata da aure mata miji',alhji ya katseta yana cewa 'meye haka hjy,menene a ciki,laifi ne idan ta aureshi naga yana damar ya auri mata hud'u,ku fa mata tunaninku karami ne wlh wani zubin,in dai sun aminta da juna ,i shikenan! Ke ameera kina son shi,kuma kun aminta da junanku?' 'eh abba' ,'toh tashi ki tafi ,zamuyi magana da bilal d'in ,sum sum meera ta tashi ta bar falon ,hjy ta rakata da harara,alhaji kuwa kishingida yayi tare da yabawa da za6in 'yarshi a zuciyarsaa ,domin ya yaba da halayen bilal! * * * meera tana shiga d'aki ta ji wayarta na ringin,sabuwar number ta gani ,tana d'auka taji muryar hibbatu tana cewa 'ameera yaya,kin gayawa abba kuwa?' ,meera ta labartawa hibbatu yadda suka yi da iyayenta,hibbatu tace 'toh shikenan zanzo gdan anjima,ki bar ni da hajiya kawai zata sauko ne....
Bilal zuciyarsa a kuntacce ya gama shiryawa ya fito zai tafi gidansu meera,kicibus sukayi da mutum a kofar gda ,mutumin yayi wa bilal sallama tare da mika masa carkey yana cewa'wai gashi abawa haj.hibbatu ,angama yiwa motar komai' bilal ya koma cikin gda ya gayawa hibbatu ta fito ana nemanta ,hijab ta saka ta fito ganin mutumin yasa ta washe baki ta amshi mukulli tana cewa 'komai is ok ko',sannan ta koma cikin gda ta d'auko kudi ta bashi,bilal da ya gama tsinkewa da lamarin hibbatu,kawai sai ya kada kansa ya tafi gdan aikinsa...
¤ ¤ ¤
Bilal zaune akan benci ,ya zabga tagumi, duk abin duniya ya isheshi,saboda hibbatu tagama shayar dashi ruwan mamaki,alhaji ne ya karaso yana mai masa sallama da sauri bilal ya amsa yana mai russunawa,alhaji ya amsa tare da bashi umarnin ya tashi ya zauna zasuyi magana,bayan alhaji ya zauna akan bencin , gyaran murya yayi sai ya dubi bilal yace 'mal.bilal ameera tazo min da wani batu d'azunnan da safe,wai kunyi amanna da junanku ,kuma kana neman ixinin ka turo magabatanka a yi maganar aurenku' bilal sai da ya had'iyi wani mugun yawu ,kanshi a 'kasa ya fara labartawa alhaji yadda sukayi da hibbatu da safen nan da kuma duk abinda ta gaya masa akan batun MIJIN HAYA! 'MIJIN HAYA?' alhaji ya maimata ransa a 6ace 'ni ameera zata mayar abokin wasanta,wato ni zata rainawa wayo ko?,imad ya gama hure mata kunne ko,toh me marabar wannan aure da auren kisan wuta ' alhaji ya cigaba da masifarsa ,bilal dai shiru kawai yayi ,alhaji ne ya ja numfashi sannan ya dubi bilal yace'zan so ka gayamin asalinka da labarinka?' bilal bai ji ko d'ar ba ya labartawa alhji labarinsa daga A har Z, bai rage komai ba ,alhaji wanda tuni idanunsa yayi ja don tausayi,ya dubi bilal yace 'kana nufin kai surukine ga alh.shoaib,hibbatu kuma 'yarsa ce da yake cewa ta rasu?' 'kwarai da gske,hakane alhaji',alhaji yasa hannu ya dafa kafad'ar bilal yace 'bilal kar ka damu,rayuwa ta gaji kalubale daban daban,amma zan taimaka maka ,kuma zan baka aiki a kamfanina,ka kawo min takardunka gobe' bilal ya durkushe yana zabgawa alhaji gdy,alhaji yace 'kar ka damu bilal ,ynxu ni da kai mun zama d'aya,domin a yau na kara tabbatar da cewa kai mai ri'ko da gaskiya ne,alfarma d'aya nake son kayi mini bilal in babu takurawa',da hanzari bilal yace 'haba alhaji kafi karfin neman alfarma a guna,sai dai kabani umarni in bi' alhaji ya ja fasali sannan yace 'zan baka sadaki,zan baka kud'i ka had'a lefe,zan baka gida da mota,kuma zan baka ameera a matsayin matarka ta aure,bana fatan saki ya shiga tsakaninku da ita,ita matar taka ka barta kawai ka bita a haka,tunda hakan ta za6awa kanta,ka barta ta ci kud'in uban ta,nima nan baxan nunawa ameera cewa nasan gskyr manufarsu game da wannan auren ba,zan koya masu hankali duk su ukun(hibbatu,meera da imad),ka shirya nan da sati biyu zan aura maka ameera!.....
  Murna!,kuka!,farin ciki!,suma!,shid'ewa! Bilal dai ya rasa wanne zai yi,kawai sai ya kama yiwa alhaji godiya ,sannan yace 'amma alhaji,wani hanzari ba gudu ba,kakata kafin ta rasu ta yi min wasiccin da in rike hibbatu amana ,kar na kuskura in musgana mata ta hanyar yi mata kishiya ',alhaji ya murmusa yace'bilal kar ka damu da wannan,naga ita matar taka ce ta bada HAYARKA ,wato dai ita ce tayi ma'karkashiya wajen had'a wannan aure ,ka kyaleni da ita kawai,sai dai kuma in ameerar ce ba kaso,sai a fasa auren ,domin baxan so in tilasta maka ba',a hanzarce bilal yace 'ko kad'an alhaji ba nufi na kenan,ko da ameera ba ta kasance jininka ba,matar so ce ga duk namijin da ya san ciwon kansa .....! Alhaji yace 'shikenan Allah ya tabbatar mana da alkhairi,kar ka manta gobe kazo da takardunka' ,sannan ya tashi ya shige cikin gida ya bar bilal da farin cikin zuciya! Hibbatu ce ta turo gate d'in ,tana sanye da doguwar hijabi,kallo d'aya bilal yayi mata ya d'auke kansa,karasowa tayi gareshi tana cewa 'sannu da duty,alhaji yayi maka zancen?,kunyi magana da shi?,ganin bai bata amsa ba,sai ma tashi da yayi ya d'auko radio yana kokarin kunnawa,hakan yasa juya 'keyarta ta shige cikin gidan ,a falo ta tadda alhaji da hajiya a zaune,bayan tayi sallama sun amsa,sai ta zube tana kwasar gaisuwa,alhaji ne yace ta zauna zasuyi magana ,hibbatu kuwa tuni ta tsure tazata asirinsu ne ya tonu ita da meera,haka dai ta xauna a kasan carpet,alhaji yayi gyaran murya yace 'hibbatu ,ina son kiyi hakuri ,ki yarda kaddara ,domin ko wanne bawa akwai tashi kalar kaddara,ina son ki yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi' ,sannan ya cigaba da cewa 'mijinki ne ya ke son ya 'kara aure' ,a razane hibbatu ta d'ora hannayenta a kan kirjinta ta maimata 'aure?' ,hajiya tace 'dole ki razana mana ,ana son an ci miki dunduniya',hibbatu tace 'tirkashi,namiji ledan guduwa,yanzu bilal aure zai 'kara,lallai ya nuna min halin maza tsirararsa' ta cigaba da surfa maganganu,hajiya ita ma tana tayata [hibbatu tana sane sarai, tayi hakan ne kawai dan kar ta nuna zalamarta! Shima alhaji yana sane ya biyo mata ta hakan],can alhaji yace 'ku dakata haka,ya isa haka' ya dubi hibbatu yace 'shikenan zan sa bilal ya janye maganar auran,daman ameera ce taxo min da zancen wai yace xai turo magabatansa,domin sunyi amanna da junansu,na kuma tuntu6eshi da zancen,yace hakane,amma ke yake jiyewa,ni kuma nace in har baki amince ba,toh sai dai su hakura da junansu' ,hibbatu tayi sauri tace 'alhaji kana nufin ameerar gdan nan bilal yake son ya aura ,wallahi na amince,i dana san itace matar da bazan ki ba,haba i ameera yar uwata na d'auketa' hajiya sororo ta tsaya kallonta sannan tace 'hibbatu wato kin amince ameera ta zama kishiyarki' ,'yar uwa dai hajiya ba kishiya ba,domin tunda har ta iya son mijina kuma ta amince ta aure shi ta zauna damu,ba tare da tayi duba ga talaucin mu ba,toh ni saboda me zan 'ki ta,hajiya kar ki damu wllh na amince',alhaji yace 'toh shikenan masha Allahu,ALLAH yayi maku albarka ' kanta a sunkuye tace 'amin'...  Alhaji ya d'auko waya ya bugawa direba waya ya bashi umarnin da ya turo masa bilal, bayan wasu 'yan mintuna sai ga bilal ya shigo palon da sallama ,ya nemi gu ya zauna daga gefen hibbatu bayan ya gaishesu,alhaji yayi gyaran murya yace'toh mal.bilal,matarka ta amince,nima na amince,sai ka shirya nan da sati biyu za'a d'aura maku aure kuma ta tare,gobe kuma zaka fara aiki a kamfanina na saida motoci,kuma zaka za6i gida daya daga cikin gidajena,amma dai kawai tunda kace gidan da kuke zaune a ynzu na gadonka ne,za'a fara gyaransa gobe in yaso gobe kai da matarka ku dawo gidannan da zama in an gyara sai ku koma' hibbatu ta fara washe hakora tana zabga godiya tana cewa 'kaga aure mai kashin arziki,ni alhaji ko zaka aurawa bilal mata uku,in dai jininka ne nasu ba damuwa wllh banida haufi',murmushi kawai yayi,hajiya itama tace 'toh Allah ya tabbatar da alkhairi,daman ke nake jiye mawa,amma tunda kin amince,nima ina murna da wannan aure,domin ameera tayi dacen miji' ,bilal yayi gdy ya tashi ya fice,ita ma meera tayi godiya ta wuce d'akin meera,tana shiga ta tarar da meera tana danne dannen waya,hibbatu tayi tsalle ta dire akan gadon tana cewa 'ameera kina kwance a d'aki ba kisan 'kosan da ake toyawa a gidan nan ba,burin mu ya cika,(nan ta kwashe yadda sukayi da alhaji ta labartawa meera),meera wani sanyin dad'i ne ya kwarara a zuciyarta ,amma a fuska sai ta ta6e baki ba tare da tace uffan ba,sai ma juyawa da tayi tana danna wayarta,hibbatu ta gama soki burutsunta ta tashi tana cewa bara naje in fara had'a kayanmu'...ta tashi ta fice,tana fita meera ta tashi ta d'aga hannayenta sama tana cewa 'ALHAMDULILLAHI',sannan ta nufi toilet,ta cire sim d'in wayarta ta karyashi ta kora a masai tana cewa 'imad ba ni ba kai har abada , zuciyata ta zama mallakin bilal!....' * * * Washegari ko da bilal yaje gida,a shirye ya tadda hibbatu ta gama had'a kayansu(tufafinsu data sayo masu ,sai kuma takardunsu) ta saka a motarta,jiranshi kawai takeyi,yana shigo ta tashi ta rungumeshi ta manna mai sumba tana cewa 'mijina gatana,kaga yadda Allah yayi damu ko,ta silar bada HAYARKA ,gashi munyi bankwana da talauci,mun tako arziki mai lasisi da garanti',bilal yayi murmushi yace 'amma kina ganin ya dace mu sakawa alhaji alkhairinsa gare mu da sakin 'yarsa a duk lokacin da kaninki ya bukaci hakan' ,'eh mana bilal,i ba zawarci xatayi ba in an saketa,aurenta fa imad d'in zai yi,kaga mu bar maganar nan,taho mu tafi kawai in munje can gidan kayi wankan',bilal yace 'toh sauran kayan fah?',hibbatu tace 'in masu gyaran gidan sunzo sa san yacca xasuyi dasu,domin ni dai akwai kud'in da zan sai mana kayan furnitures da sauransu idan mun dawo,kuma nasan itama ameera za'a yi mata kayan daki ,kila muma suyi mana','uwar son banza kenan' bilal ya fad'a a zuci,suka fice daga gidan,motarta suka shiga,hibbatu ta bata wuta sai gidan alhaji,bayan sunyi parking a kofar gate,sai bilal yace 'da kud'in HAYAR kika sayi motar nan ?' ,'eh mana' ,'toh in mun shiga me zamu ce game da motar nan in an tambaye mu','ka kyaleni dasu,ni nasan me zance masu,fita ka bud'emin gate in shiga' 'toh' bilal yace mata tare da fita ya je wangale mata gate ta harba kan motarta ciki...... Hakkin mallaka:abdulaziz ililee Hakkin mallaka:abdulaziz ililee
Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 10:53
In Hausa Novels
Mijin Haya Part 18 Title : Mijin Haya Part 18
Description : Bilal ya juya ya dubeta da kyau ,amma ya kasa cewa komai ya kad'a kansa a sanyaye ya fice daga d'akin... * * * a bangaren meera a...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Mijin Haya Part 18"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ▼  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ▼  September (199)
      • Graphic Photos: Sojoji Sun Ceto Wasu Mata Da Aka Y...
      • An Damke Mahaifi Da Yima Diyar Sa Fyade
      • Mijin Haya Part 18
      • Photos: Sunlight Laraba's World Tv Drama Series Hu...
      • Photos: Sheik Isa Aliyu Pantami Ya Shiga Ofis A Yau
      • Buhari Ya Taya Zababben Gwamnan Edo Murna
      • Photos: Jami’an Tsaro Sun Kulle Ofishin Abdulmumin...
      • Dan Takarar Gwamnan Na APC A Jihar Edo Ya Lashe Zabe
      • Photos: An Haifi Wani Jariri Mai Kama Da Tsoho
      • Photos: Mutane Shida Sun Rasa Ransu A Wani Gidan K...
      • Abdulmumini Jibrin Ya Kai Kara Majalisa Wakilai Kotu
      • MIjin Haya Part 17
      • Majalisar Wakilai Ta Dakatar Da Abdulmumini Jibrin...
      • Kaine Sirri Na Part 23{END}
      • Photos: El Rufai Ya Sanya Danshi A Makarantar Gwam...
      • Al'ajabi: An haifi Jariri Mai Iyaye 3 A Kasar Mexico
      • Wani Yaro Dan Shekara 11 Yayi Fyade A Kasar Ingila
      • Mijim Haya Part 16
      • Buhari Ya Umarci Tambuwal Ya Sulhunta Tinibu Da O...
      • Kaine Sirri Na Part 22
      • Bankin Afirka Zai Tallafa Wa Najeriya Da $10b
      • Video: I LOVE YOU By CLASSIQ FT AVALA starring Rah...
      • Mijin Haya Part 15
      • Ban Yi Tsufa Da Auren Zahra Buhari Ba - Gwamnan Za...
      • Wani Kurma Ya Yi Fyade Wa 'Yar Wata Shida A Yobe
      • Na Hakura Da Mukamin Shugaba A Jam'iyyar APC. Bana...
      • Kaine Sirri Na Part 21
      • Kaine Sirri Na Part 20
      • Photos: Hanun Wani Matashi Ya Makale A Jikin Kur'a...
      • Photos: Sojojin Nijeriya Sun Kashe 'Yan Boko Haram...
      • Mijin Haya Part 14
      • Video: Rahma Sadau Ta Ziyarci India
      • Ina Nan Garau Da Raina - Abubakar Shekau
      • An Kashe Marubuci Da Yayi Ridda' a Jordan
      • Photos: Aisha Buhari Ta Ziyarci Ingila
      • Kaine Sirri Na Part 19
      • Wani Ma'aikacin EFCC Ya Karbi Cin Hancin Miliyan 15
      • MIjin Haya Part 13
      • Kaine Sirri Na Part 18
      • Photos:Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Wa Yarsa F...
      • Tsagerun Niger Delta Sun Kai Hari A Garin Bonny
      • Mijin Haya Part 12
      • [Daga Jama'a] Dalilai Goma (10) Da Yasa Nake Son A...
      • Kaine Sirri Na Part 17
      • ISIS Sun Hana Yan Kasar Iraqi Sa Rigar Kwallon Kaf...
      • Naga Rayuwa Part 2
      • Naga Rayuwa Part 1
      • Yar Amana Part 3
      • Yar Amana Part 2
      • Wani Lauya Yakai Karan BuhariI A Kotu
      • [New Music] KU TARE BURGU YA GUDU By RARARA
      • Gwamnoni Da Ministoci Sun Amince Da Sayar Da Kadar...
      • Mijin Haya Part 11
      • Photos: Sabin Hotunan Nafisat Abdullahi
      • Zan Siya Kungiyar Kwallon Kafan Arsenal Nan Da She...
      • Kaine Sirri Na Part 16
      • Wani Dan Aikin Turai Yar’adua Ya Sace Mata Naira M...
      • Sabuwar Girgizar Kasa Ta Sake Faruwa A Kaduna
      • Mijin Haya Part 10
      • Kaine Sirri Na Part 15
      • Photos:An Kama Wani Tsohon Na Shirin Lalata Da Wat...
      • Photos: Barayin Shanu Sunyi Hadari Da Shanun Da Su...
      • Mafarki A Lokacin Jinin Haila
      • Yar Amana part 1
      • MIjin Haya Part 9
      • Photos: Sarkin Kano Ya Halarci Taron Sulhu Na Duni...
      • Kaine Sirri Na Part 14
      • Photos: Aisha Yayin Bada Lacca A New York
      • Mijin Haya Part 8
      • Photos: Sabin Hotunan Sadiya Gyale
      • Photos: Yan Bindiga Sun Sace Wata Malama Makaranta...
      • Photos: Yau Ranar Murna Haihuwa Yar Sarkin Kano Sa...
      • Kaine Sirri Na Part 13
      • Buhari Ne Matsalar Kasar Najeriya - Ayo Fayose
      • Mijin Haya Part 7
      • Photos: An Nada Wata Budurwa A Matsayi Shugaban Ka...
      • Photos: Sabin Hotunan Jaruma Nollywood Tonto Dikeh
      • Ya Kamata A Haramtawa Barayin Gwamnati Shiga Harka...
      • 'Yar Najeriya Saheela Ibrahim Ta Shiga Sahun Matas...
      • Kaine Sirri Na Part 12
      • Graphic Photos:Anyi Rikici Tsakanin Matasa Da Yan ...
      • Photos: Halima Da Zahra Buhari Sun Halicci Wani Bi...
      • MIjin Haya Part 6
      • Ibrahim Shema Ya Mika Kansa Wa EFFC
      • Kaine Sirri Na Part 11
      • Saeed Nagudu Na Shirin Waka Da Wizkid
      • Fatima Part 1
      • Fatima Part 2
      • Photos: Sojojin Najeriaya Sun Mika Iyalan Boko Har...
      • Sojojin Nijar Da na Chadi Sunyi Nasara Akan Boko H...
      • Photos: Dangote Da Yarsa Halima A Bikin Ranar Murn...
      • Mijin Haya Part 5
      • Photos: Halima Atete Da Fati Nijar A Makka
      • Za A Yi Afuwa Da Tsagerun Niger Delta Sama Da Dubu...
      • Kaine Sirri Na Part 10
      • Photos: Ku Ga Babba Maciji Da Wani Mutum Ya Kashe ...
      • Mijin Haya Part 4
      • Photos: Yan Sanda Sun Cafke Yan Fashin Da Suka Yi ...
      • An Dakatar Da Limamin Masallacin Juma'a Na Sultan ...
      • Kaine Sirri Na Part 9
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger