1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » Kaine Sirri Na Part 11

Kaine Sirri Na Part 11

By Abdul Mk
Add Comment
Saturday, 17 September 2016
                    Fitowa sukayi daga cikin motar Amma ta rike hannu Rufaida datake shirin kuka tana kallon Mum, Mum ta girgiza mata kai alamun kartayi da kyar ta iya hadiye hawayen suka cigaba da tafiya auta ce tafara artowa aguje ta rungume Mum tana ihu”big Mummy oyoyo” bama tajira amsan Mum ba tasake ta ta rungume Rufaida da saida takusa faduwa Amma ta sakin mata rankwashi zaki fadar da itane Mara natsuwa,Auta ta bare baki Mum tarike ta tana lallashin ta tace muje ciki nakawo miki tsaraba Auta tace to amma bari naje nafadan ma Anty Hafsat (amaryar Muzammil) matar Uncle B tazo dan tana kitchen kafin Mum ta amsa tayi ciki da gudu. Kan Rufaida akasa harsuka shiga mai falo suka zazzauna ana hira Auta da wata kakkyawar mace doguwa tana sanye da brown dinkin doguwan rigar shadda taji aiki hanunta dauke da tray na drinks tana murmushi tajawo center table ta daura drinks din tana gaishe da Mum,Mum ta amsata sosai da faraa dan tasan Muzammil. Amma tace sannu da aiki Hafsat tun safe kinki hutawa kinata aiki,da sauri tace laaa Amma bakomi Uncle B yace nakula da Mum da amaryar shi da kyau kafin yadawo ta dawo kusa da Rufaida ta zauna tana kallonta Rufaida ta dukar da kai taki bari suhada ido,Mum tai dariya tace daughter na tacika kunya dauketa Hafsat Ku shiga ciki tayi wanka tagaji. Hafsat ta rike hanunta tana murmushi tace to muje,Rufaida ta mike ahankali ta daga kanta karaf suka hada ido da Hafsat da sauri Rufaida ta dukar da kai,dariya Hafsat tayi tace aita boyemin fuskar Nanda sati biyu dole muga fuskar da kyau,suka fara tafiya wani bangare daban da Amma ta nuna mata takaita,ta ajiyeta a hadadden bedroom kafin tace to bari na dauko miki kayanki ko Kai akasa tace to” Hafsat tai murmushi takoma shashin Amma wayarta ta dauko ajaka ta kira number Mijinta ringing daya Muzammil ya dauko yace baby na ya? ” da sauri Honey sun iso, Muzammil yace da gaske baby na sun iso?” Barraq dake gefenshi yana duba wasu takardu Zane ya ajiye da sauri ya matso kusa da Muzammil yana kallonshi “su Mum ne suka iso?” Muzammil ya ballamai harara tareda juyamai baya yace “baby na kinaji ki kula da ita,jeki zauna da ita kartai kewa…” Fisge wayar yaji anyi daga kunenshi Barraq jikinshi har wani bari yake yace”madam kikace sun iso?”dariya Hafsat tayi tace eh Uncle B, da sauri yace tana ina?” Tana daki,Barr yace babu wani abu dake damunta ko?,taci abinci?,tai wanka? Tagaji sosai ko halan,Abba ya ganta?” Hafsat ta rike kai o Uncle B ko kunyana bakaji wanan tambayoyi haka,yadan Sosa keya yana murmushi, nabarta zata shiga wanka saita fito ne zataci abinci ” Barr yace “ok,plz nabaki amanarta kinji madam,da zaran mun gama binciken damuka zoyi zamu biyo flight mudawo” Hafsat tai dariya sosai tace naji bama honey tabe baki yayi ya mikama Muzzamil dake kallonshi Hafsat tace Honey Allah dawo daku daga Lagos din lafiya.yace Amin takatse wayan takoma sitting room tadau jakar da Mum ta nuna mata na Rufaida ta wuce shashin da Rufaida take.
Samunta tayi a zaune daure da towel

Kuka tafara sosai harda shesheka tana mammatse kafa kaman tanajin fitsari. yadade yana kallonta kafin ya zaro Biro daga aljihun gaban rigarshi ya ijeye mata akan table  ya kalleta yace”ki tayani solving. Naje makarantu da wuraren Zane a Lagos yau, anyway kiduba zakiga komi saikimin lissafi” hannu tasa ta share hawayen idon nata tadau biron ta bude littafin tafara Mai lissafin,yayinda shikuma yadau remote ya kunna TV yana kallon channel news ganin taki sakewa.
Wuraren 10:30 tagama ta dago kai ta kalleshi amma takasa mai magana,haka tai shiru ga bacci na kamata. kwantar da kanta tayi a kan center table din ahaka har bacci yay gabada ita.
Karfe shadaya yagama kallon news din,ya kashe kafin yazo inda take ya tsugunna yana kallon fuskarta,ahankali yakai bakinshi goshinta ya sumbaceta kadan sanan yadago yana murmushi”I luv yhu Rufaida with all of my heart” ya sumbaci hanunta “ina sonki sosai matata sama da yanda kike zato”bakinshi yakara sakin wani tattausan murmushi,fararen hakoranshi suka bayyana. Rike kanshi yay”duk lokacin Dana ganki konake taredake jinake kaman zuciyata zata fashe saboda irin son danake miki Rufaida” jin ana kokarin bude kofa yasa yasaki hanunta yadau memo da Biro ya Mike tsaye da sauri Mum ta kullo kofan tana karemai kallo”what are yhu doing here?bakaga tai bacci ba?” Yadan Sosa keya “news NA kalla” yabata amsa atakaice yabita gefenta yafita daga dakin. Mum tai murmushi takada kai tana mamakin dannata,kamar mafarki yaron da bayason auren kananun yara shine yau ya mutum ma Rufaida.

Da sallama suka shiga falon Dad ya amsa Hafsat ta gaishe da Dad sosai kafin ta fice daga dakin,Rufaida ta zauna kusada kafar Mum murya Chan kasa tace”ina wuni Daddy ” da tattausan muryarshi yace”lpy lau yata,ya lesson din da ake miki hope kina ganewa kuma kina kokari?” Ta dagama Dad kai, Daddy yace to Alhamdulillah, in sha Allah bazaki taba nadamar zamanmu iyayenki ba,in sha Allah bazaki taba Dana sanin saninmuba,Allah zai albarkaci rayuwar ki kinji yata?” Ahankali tace”Ameen nagode Daddy”.
Yace Rufaida inaso nahada ki aure da dana dan yazomin da maganar yana sonki,a tsarina da tsarin dayake raina tun kafin nama haifi ya mace shine duk Randa Allah yabani mace zan aurar da ita tana shekara16-17 saboda aure shine gatan dazakama yarka mace. Tunda yanzu Allah ya banike Rufaida zanso na aurar dake yanzu inyaso bayan anyi aure kya cigaba da karatun ki but dudda wanan dogon burin nawa bazan iya bama Barraq keba saida yardar ki da amince warki,kin yarda zaki auri Barraq? Dukar dakai Rufaida tayi ita batason yanda suke tambayar izininta saikace tafi karfinsu,wlh banda kowa daya wuce Ku aduniya bantaba sanin bayan rasuwar Abba da Umma zan sami wayanda zasu soni kaman kuba,kowa kuka bani zan aura,zanmai biyayya zanmai komi inhar hakan zai baku natsuwa da farin ciki kwatankwacin irin wanan dakuka bani ayau.
Muryar Dad taji yace”to Alhamdulillah yata,Allah ubangiji yamiki Albarka,sati biyu za’a dauka kafin a daura muku aure Allah miki albarka kinji tashi kitafi kunya taji yakamata ta chusa kanta a cikin cinya tana kuka sosai. Mum ta mikar da ita suka fita daga dakin.
Daki Mum ta kaita takawo mata abinci ta tasata agaba taci daidai cikinta kafin tabar dakin Hafsat na janta da hira sunayi sama-sama. 9:30 PM suka shigo gidan agajiye,Muzammil yace”gaskiya gobe ne zan dawo nagaisa da Queen of ur heart dan right now I need a hot shower, kuma baby nace zatamin” Barraq ya kalleshi batare dayace mai komiba yafito daga motar Driver yafito yamika ma Muzammil key. Muzammil yay murmushi kafin ya Sosa gemu yace”jimana” Barraq yajuyo hanunshi na aljihu fuska a daure “wot?” Muzammil yay dariya kafin yace haba abokina ainace gobe zanzo ko,ko kafiso naje haka duk munyi datti,yanzu dai dan kiramin baby na tafito mutafi gida”Barraq ya ballamai harara” I be ur messenger? ” yajuya yayi ciki Muzammil yafashe da dariya yaciro waya daga aljihu yay dailing number Hafsat ta dauka yace ina waje kimusu sallama kifito mutafi dare yayi sai gobe zamu dawo mu gaisa,Hafsat tace to kafin ta katse wayan. Ta kalli Rufaida dake kallon TV tace”zan tafi gobe zan dawo,hope zaki tattaro hirarraki dazamuyi ko?” Rufaida tasaki mata tattausar murmushi tareda dukar da kai tana wasa da yatsun ta”eh Anty Hafsat” Hafsat tai murmushi “kunyar nan taki na burgeni, gashi idan Kinyi murmushi sai dimple dinki su lotsa,anyway natafi saida safe” Rufaida ta mike tsaye tace”Bye nagode, Allah kaiku lpy” Hafsat tajuya tafita daga dakin ta rufo kofar,ahankali Rufaida ta zauna kan kujera tacigaba da kallon walking dead din daya dauke hankalin ta,dudda film din nabata tsoro amma kuma tanajin dadinshi.
Shiga motar Hafsat tayi ta zauna bayan tafito daga shashin su Amma yimusu sallama,kallon hanunta tayi ta fade kai” God! Namanta ban bataba. Muzammil yace me baki bataba?” Wlh wani abu gashinan ajakata nakawoma Rufaida na manta ban bataba,Muzammil yace yi sauri kije kibata mutafi gida danyau I need yhu badly baby” dariya tayi taja hancinshi”Allah dan albarka?” Kokarin chafketa yayi tafita daga motar da gudu  tana mishi gwalo, shashin da Rufaida take ta tsaya agaban kofa ta kwankwasa hankalin Rufaida nakan kallo taji ana buga kofa mikewa tayi tatafi kofa ta bude ganin Hafsat yasa tai murmushi “Anty Hafsat” Hafsat ta shigo dakin ta kulle kofa ta mikama Rufaida wata yar karaman koriyar leda tace”ga wanan ki dinga cin abubuwan ciki kullum sunada amfani kinji” Ganin Rufaida batada shirin amsa yasa ta saka mata a hannu tajuya tafita da sauri, kullo kofan Rufaida tayi takoma ta zauna kan kujera tana kokarin bude ledar, idanunta suka sauka kan wani hadadden kwaku meti shi taciro daga ledar ta ijeye saura abubuwan a gefe tanacin kwakumetin tana kallon walking dead ta zame dan kwalin kanta gashin kan ya zubo har baya.
Knocking data karaji yasa tadan tabe fuska dan kallon yafara mata dadi,debo kwakumeti tayi a hannu ta mike tsaye tana tafiya tana waigen TV bude kofa tayi da dayar hanunta batare datama kalli kofan ba hankalin ta nakan kallon,Takara bude baki ta zuba kwakumetin tana taunawa ganin wani bakin dodo yazo Zai cinye wata hakan yasa ta sandara ihu “wayyo Allah na Mummy” Kara bude ido tayi ta kalli TV ganin dodon nacin mutum taga kaman ita yake cinyewa yasa tafasa ihu zata tajuya zata fita daga dakin karo taji taci da mutum tai baya-baya zata fadi da sauri ya riketa,kwalalo ido tayi kalleshi ganin dai tabbas shine yasa ta kulle idonta gam tai lamo a jikinshi tareda kara kankameshi jikinta na rawa.
Chak ya dagata yazaunar da ita akan kujera,ya maida kofan yarufe kafin yadau remote ya kashe kallon duk kanta na kasa tana Sosa kai,”karki Kara kallon irin film dinan tunda firgita yake saki”. Kai kawai tadaga mai kafin ta tashi tayi hanyar bedroom da sauri harda tuntube “ina zaki?” Juyowa tayi kanta akasa muryarta na rawa sosai kaman mai shirin kuka tace ” ai,ai bacci nakeji” zoki zauna anan sai 1 zakiyi bacci yau.
Ta dawo ta zauna jikinta na rawa. “Ya karatu?” Kallon fuskarshi tadanyi da sauri ta juyar da kai tasa bayan hanunta ta goge Hawayen dake shirin zubo mata.  Ya dade yana kallonta kafin yay murmushi yace “coconut chips(kwakumeti)din harsun ishe kine? Naga kinata ci dazu”girgiza kai tayi hawaye ya gangaro zuwa kunncinta, shida yarasa maisa takejin tsoronshi haka anywayno insun hadu da Muzammil ya fadamai maybe yasamu solution daga wurinshi. Wani dan karamin book ya ajiye mata akan center table” help me.                         maman Abd  Shakur ðŸ˜˜
Ina mai alfahari da zamanki matata,and I promise zan kula dake,namiki komi ,I will be d best husband kinji” hannunshi yasa ya kamo hanunta ya rike da sauri tadan zaro ido tana kallonshi tattausan murmushi ya sakar mata. yadau ko wata yar karaman akwatin dake kan tray ya bude wani farin zobe mai kama da azurfa anmai ado dajan zanen zuciya ajiki  ya ciro ya zura mata a yatsa ya dago kanshi yaga Rufaida na kallonshi idanun na gab da zuboda ruwa, girgiza mata kai yayi ta hadiye hawayen. yasa hannu ya shafa zoben “u are special Baby”yafada yana kallon kwayar Idonta. ahankali ya zare hijabin jikinta, ta zaro ido jikinta na bari. Champagne ya dauko daga kan tray din ya bude ya zuba a glass cups guda biyu ya mika mata daya takasa karba,da kanshi yakai bakinta saida ta kalleshi ya lumshe mata ido sanan ta kurbi kadan. ya ijiye kofin akan table ya kwanto da ita a jikinshi yana sauke ajiyan zuciya a natse  yana shafa bayanta. jikin Rufaida yafara rawa tafashe da kuka sosai dago kanta yay “nadena bakiso?” Girgiza kai tayi a tsorace tace”zan tafi,bacci nakeji,dama Mummy ce tace nazo nama sallama gobe zamu tafi” ganin yanda jikinta ke bari hawaye na tsiyaya yasa ta mugun bashi tausayi yaji yafasa abunda yay niyyan yi. Mikar da ita tsaye yayi yadau hijab dinta yasa mata, wasu jajajen fulawowi da aka daure a wani irin leda(red roses) yasa mata a hannu ya kawo bakinshi kunenta “symbol of my luv”taji ya ambata  sanan ya koma gefe. da gudu ta juya zata fita daga dakin, chak taji an rike hanunta,a tsorace ta juyo ta kalleshi bakinta na rawa, ahankali ya sanya hannayen shi ya rike bayanta yana kallon kwayar idonta kafin  yadan rage tsawo yakai bakinshi yahada da nata.

Tun daga ranan Rufaida bata sake ganin Barraq ba,hakan yasa hankalinta ya natsu bata tunani. Saidai taga an mayar da ita wani bangare daban a gidan babu Wanda ke shigowa daga mummy said Amma sai Hafsat matar Muzammil. Saikuma wata mata da suke kwana tare dataji Mummy na kiranta da  buzuwa.  kullum tana bata wasu abu taci,Tasha,Dana wanka dana tsarki, Rufaida dukta gaji dan har asalin abinci ma andena bata Saidai na magani.  Kullum idan Mummy ta shigo ganinta saita mata kuka tana cewa ita batason abunan da ake bata Dan yana sata kiba tanajin wani iri Mum saidai tai dariya ta lallabata ta tafi.
Yau takama Friday ranan da za’a fara sha’anin biki,tana zaune tanacin wani indomie da buzuwa ta dafa mata da magani tana kuka hanunta da kafafunta sunsha hadaddun baki dajan lalle na amare,gashinta yasha gyara wanda duk buzuwa ce taimata. Hafsat ta shigo dauke da wani katuwar akwati a  hanunta da sallama “wow!” Ta furta tana kallon Rufaida dataga gabaki daya ta chanza bakin fatarta na wani irin sheki,ta chiko sosai kirjin nan ya ciko daidai ita, karaso wa tayi ta zauna kusa da Rufaida da murnanta “anty Rufaida kinyi mugun kyau Wlh, idan uncle B ya ganki saiya rude”ta daga hanun da akamata zanen lalle tana kallo tace”waya miki wanan lallen?harda gyaran gashi” Rufaida ta turo baki idanunta yakawo ruwa tace”ba buzuwar nan dasu Mummy suka kawo bane,kullum saitabani magani wasu da dadi wasu da shegen daci,taita shafamin wani black and yellow-yellow(kur-kur da dilka) things on my sick. takara fashewa da kuka muryarta na rawa”and am sure they have side effect, cus they have one kind of  disgusting odor yayanya,huum” tana maganan tana turo da tabe baki. Hafsat ta rike kuncin ta tana kallon Rufaida dariya ke neman subuce mata amma batason tayi hadiye dariyan tayi tadanyi murmushi kafin tace “kai amma buzuwa bata kyauta mana ba,yanzu tashi ga kayan dazaki sa nakawo miki yaune walima kinji”Rufaida tadan zaro ido “waliman bikin wai haryazo ba sati biyu akasa ba?ai batayi ba saigobe ne  fa anty Hafsat “Hafsat tai dariya mujeto kiyi. ahankali ta mike suka shiga bayin, Buzuwa ta shigo tahada mata wasu abubuwa a ruwan Rufaida ta zumburo baki Hafsat tafito tana dariya bata wani jimaba tafito Buzuwa ce tai mata wani irin hadadden make up, Hafsat saibin buzuwa da kallo take tana mamakin yanda ta iya komai gyaran jiki,lalle,gyaran gashi gakuma make up.  Sai bayan angama tasa mata kayan doguwar rigace har kasa ja,sai kuma dige digen baki ga takalman ta hill aka samata, tai kyau sama da tunanin mai karatu Hafsat tarike mata hannu suka fara tafiya,juyowa Rufaida tayi ta kalli Hafsat tace”anty bantaba sa Hill ba ya akayi naga na iya tafiya dashi?”  Hafsat zatai magana Mum takaraso wurin tabama Rufaida kakkyawan runguma ta kalli Buzuwa tace “thanks for everything friend” Mum tarike mata hannu har gaban wata hadaddiyar mota tasa hannu tabude tasa Rufaida aciki ta kullo,su da wasu manyan matayen turawa suka shiga sauran motocin da akayi layi dasu a wurin suka wuce wurin walimar.
Wa’azi sosai wasu manyan malamai sukayi mai ratsa jiki,da ilmantar wa,Rufaida tasha kuka bana wasaba. Karfe 7:00pm aka dawo gida, bayan sallan issha dad ya aika aka kiramai Rufaida.
Wa’azi da nasiha da uba yakamata yayma yarshi dad yayma Rufaida. Rufaida tasha kuka a wurin anan yake sanar mata da Barraq yace a Russia yakeso tai karatu,dan dazaran yagama wani case dake gabanshi yanzu na neman wata yarinya zai koma Russai da zama. so saisa na nema miki makaranta a Chan ranan Monday zasu koma keda Mum kinji yata? Rufaida tamai godiya ta karbi wani akwatin da yabata tafita daga dakin.
Washe garin ranan aka daura Auren BARRISTER BARRAQ da RUFAIDA akan mafi karancin sadaki Barraq yarasa Inda zaisa kanshi saboda murna burinshi daya kawai yaga Rufaida.
Sosai zazzabi yarufe Rufaida idanunta sukai ja sosai jikinta zafi. Amma takira family Doctor yadubata aka bata magunguna. Mummy ta zauna ta daura kanta akan cinyarta tana shafa cikinta dataji ba nauyi. Tea Hafsat takawo mata da kyar tasha kadan tana kuka. Mum dukta damu tace”for godsake Daughter meke damunki? Tell me kinji banason kina ciwo” Rufaida takara narkema Mummy tana kuka”Mummy promise me dake zan zauna,wlh Mummy ni banason akaini wurin Uncle B,tsoronshi nakeji Nafison zama dake” takarasa maganan tana kuka, Mum tai murmushi “OK naji,only if u cooperate kika warke dan baki sun cika gida anason ganinki” ta share hawayen to muje naji sauki.

                44
Duk shagalin da aka hada Rufaida bata halarta ba saboda zazzabin dake damunta. Da kyar Mum ta lallabata tai bacci ta lullubeta tafito daga dakin lokacin ma haryan biki sun watse.
Dakin Mum ya shiga ganinta tareda wata bakuwa suna magana yasa ya zauna a gefen gado yana danna waya. Mum taraka bakuwar tareda rufo kofa tazo kusada Barraq ta zauna tana kallonshi”Muzammil na nemanka dazu,Hafsat nata amai zai wuce da ita hospital “Barraq ya daura kanshi a kafadarta “ya ganni lokacin ina falon Daddy ina magana da Alh nan dana fada miki yarshi tabace” Mum tace”ayya,har daurin auren saida yazo,yanada kirki, Allah yasa yaga yartashi” Barraq yakara wani narke mata “son am very tired, me kakeso saboda wanka nakeson shiga yanzu” Barraq yay shiru baice komiba. “O ur wife, tana wurin buzuwa,tana bacci karka tasheta” murmushi yama Mum ganin ta kafeshi da ido. mikewa tsaye yayi yafita daga dakin da sauri Mum ta girgiza kai “sarkin kunya”.
Hango Buzuwa dayayi a dakin zaune tana kallo ta window yasa yaji wani haushi yakamashi dan yaso yaduba lafiyar matarshi. haka yawuce side dinshi yafada kujera ya dauko taba yafara zuka.
washe gari yakama lahadi taji sauki sosai saidai tai zuru zuru gashi batada abokin hira dan Hafsat batazoba Mum tace batada lpy.
Wuraren 9:00 Na dare Mum tafito daga side din Buzuwa ganin Barraq tsaye a wurin yana leken windo yasa Mum tace”wot are yhu doing son?” Da sauri ya juyo ya kalli Mum “nothing “yaba Mum amsa atakaice yajuya yabar wurin da sauri. Ajiyan zuciya Mum tayi tajuya  takoma ciki. Rufaida dahar ta kwanta ta tashi da sauri ta yaye bargon jikinta “Mummy na kindawo ki karanta min story ne?” Mum ta zauna gefen gado ta girgiza kai “no,kije kima Son sallama,kinga gobe zamu koma kinji daughter “Rufaida ta gyada kai”to Mummy” tadau hijab tadaura kan kayan baccin jikinta tajuya zata fita Mum tace “come”  tadawo Mum tadau turarurruka masu cool kamshi ta shafa mata sanan tabata izinin tafiya.
Knocking tayi “who?” Taji yafada,muryarta na rawa tace”Ni…ni…nin..nine..” bata karasa maganar ba yabude kofar da sauri taja da baya tana kuka hanunta na rawa ta kulle idonta gam”.
Wani sanyi yaji a ranshi ganin Matarshi ce aranshi yace luv yhu Mummy.
Tattausan hanunta yakama ya shigar da ita cikin dakin. zaunar da ita yay akan kujera ya maida kofar yarufe ahankali yadawo ya tsugunna a gabanta ya daura hanunwanshi akan cinyarta ko ina na jikinta rawa yake murya chan kasa yace”relax luv!u are with me, open ur eyes “kankame jikinta tayi tana sosa idanunta dake fitar da ruwa. zame hanunshi yayi daga cinyarta yatashi ya shiga bedroom yay kusan minti biyu kafin yafito sanye da white singlet da gajeren wando baki,hanunshi dauke dawani dogon silver tray ya ijiye kan center table yadawo kusa da ita ya zauna jikinshi na gogan nata, jawota jikinshi yay yarungume. ihu tasaki tana kokarin kwace kanta takasa, ahankali yace”shiii!banason kuka, keep quiet and open ur eyes kinji baby na “girgiza mai kai tayi,sanan  yasaketa ta zauna tana share hawayen da bayan hanunta “Rufaida “Taji ya kirata hakan yasa ta daga kai ta kalleshi “I luv yhu, ina sonki sosai”.

Da kyar ya iya sakin bakin nata yana kallon yanda take kuka yasa yatsa ya share hawayen murya chan ciki yace”shiii,banason kuka, abunda nai miki is normal, haka miji kema matarshi kinji baby na ” ta dagamai kai jikinta na rawa. harshen shi yasa yadan lashi lips dinta dasukai ja yace”good girl,ina kara sonki ne saboda kinajin magana,muje naraka ki ki kwanta dare yayi” hanunta yarike suna tafiya ahankali tana binshi luuu dan gabaki dayan jikinta ya saki.
Saida ya bude kofar dakin Buzuwa sanan yasaki hanunta yana mata murmushi”sleep like an angel Baby”ta shiga ciki da sauri ya kullo kofan yajuya yatafi side dinshi cike da tunaninta. Da kyar bacci ya kwashi Rufaida dan takasa manta yanda taji yanata tsotsan bakinta.
Washe gari da wuri Mum tasata ta shirya dan jirgin karfe tara zasubi. Buzuwa tahada mata kayanta gabaki daya da wasu gangariyar magani. Rufaida ta shirya cikin wani dogon brown skinny jeans da light brown armless shirt ta daura brown boyfriend jacket a saman su, ta yane kanta da gyalle, kafarta na cikin wani hill browm mai shegen kyau. tafito daga part din Buzuwa ahankali take takunta mai daukan hankali harta bude kofan dazai sadata da dakin Mum da sauri ta juya zata koma “karki koma ki shigo I missed yhu” ahankali ta shigo kanta akasa tana watsa da yatsun hanunta ta tsaya, jawota jikinshi yayi ya daurata akan cinyarshi yana kare mata kallo,ahankali yasa hannu yana warware gyalen da ta nade kanta  “Baby dis kand of dressing is for me only,bakisan inada kishi ba” hawayen ta ya diga akan hanunshi,murmushi yay ya daga hanunta yana kallon zanen lallen hanunta”I luv dis,yama hanunki kyau “ahankali yasa hannu a kafadarta yana sabule boyfriend jacket din jikinta harya cire duka ya ijiye a gefenshi yana karema jikinta kallo batare daya mata komiba. Rufaida tacigaba damai kuka ahankali tana shesheka,kanta akasa taki hada ido dashi  “Mummy kike nema?” Ta dagamai kai,”Mum na wurin Dad tajemai sallama”.
“Mesa kike tsorona?ni dodo ne?” Ahankali tace”uhm uhm”ya leko da fuskarshi zai kalleta da sauri ta juyar da kanta gefe,juyo da fuskarta yay ya kwanto da ita kirjinshi yana shafa bayanta ahankali ya sauke ajiyan zuciya”I will miss yhu idan kun tafi,but dazaran nagama case din dake gabana nanda 3 or 4 weeks zanzo,just take good care of ur self for me Baby, I luv yhu” takara kulle ido jikinta na rawa dago ta yay yahada goshin shi da nata murya Chan ciki yace “duk lokacin dakike wanan tsorace tsoracen,da koke koken da kulle kullen idon, karajin sonki nake a zuciyata cus I luv it,everything fits yhu Rufaida my little Baby ” yakai bakinshi kan nata yabata light kiss “Ina sonki matata” chusa kanta tayi sosai a kirjinshi tana mutsu mutsu saboda kunya, abun yabashi dariya sosai yadan dara “nacigaba da kissing dinki ne baby na ? ” ta boye fuskarta a kirjinshi tana shesheka bude kofa da akayi yasa ya dago kanshi Mum ce da sauri Rufaida ta sauka daga jikinshi ta koma gefe Mum tai kaman bataga komiba tace”Daughter kin shirya?” Barraq ya tashi yana sosakai Mum ta bishi da kallo harya fita ya dawo ciki da sauri Rufaida ta sadda kanta akasa kallon Mum yayi kafin yace”kisa Hijab,karki fita ahaka ” ya juya yafita da sauri yana murmushi.

Kimanin sati  3 uku kenan da komawarsu Russia. Tuni Rufaida tafara makaranta mai suna KINGSLEY DAISY’S  SCIENCE SCHOOL. aka mata interview taci sosai hakan yasa suka sata a class 2(SS2 a Nigeria ). Karatu take sosai tana da kokari daidai ita,batada kawa ko daya dazaran lokacin tashi yayi Mum zata turo Driver yadauko ta. Mum nabata kulawa bata sakaci da magungunan da buzuwa tahada mata dakuma na asibiti da aka bata saboda yawan ciwan maran datakeyi kowani wata.
Bangaren Barraq kuwa ya dukufa neman Rufaida, saboda yanda yaga Umma da Ahj na wahala danko haihuwar datayi saidai aka mata aiki aka ciro baby boy.  Gashi yanzu kusan sati uku kenan yanabin makarantu gidan marayu na garuruwa daban daban yana neman Rufaida da aka mishi kwatance. Aikin da yansanda yakamata suyi amma tausayin su Alhj yasa shiyake yi dakanshi. Matsalanshi daya yakasa samun kishiyan Umma suyi magana duk inyaje Lagos Alh yakaishi gidanta basa samunta har abun yasoma bashi mamaki. Yafadan ma Alhj zai dakatar da binciken yaje yaduba matarshi a Russia. Alh yamai addu’a Umma tahada tsaraba dayawa tabama Barraq yakaima matarshi da kyar suka samu ya karba Alh yakaishi Airport yabi jirgi yakoma Abuja.
“What are U saying murtala (PA)?Danme nake biyanka da bazaka sanar dani wanan babban maganar ba? Har saida tai tsami harma tafara wari kafin naji?” PA yace “haba Nana ai kyamin uxuri ,har gidanku naje danna fada miki amma akace kinje Dubai toya zanyi?” Nana ta  dafe kai tana huci “yanzu Barraq dinane yay aure? Ya auri wata batare da nasani ba. Nooo!” Ta buga glass cup din hanunta akasa yafashe TASS. “Wlh bazai yuwu ba,Bazata sabuba bindiga a ruwa, nikadai ce matar Barraq bai isa ya auri wataba, am d only one dat is  meant for him”. PA ya gyara neck tie din wuyarshi yace “better do something, dan gobe zai tafi Russia ganinta,zai kuma  Dade,and d worse part is bantaba ganin Barr in luv kaman yanda naga yakamu dana yar yarinyar nan ba,gashi kowa nason yarinyar barinma Mum dinshi,wlh I can tell you tafison yarinyar kan Barraq her own son”. Da sauri Nana tace”flight din karfe nawa zaibi?” PA  ya balla mata harara “biyani kafin nabaki information, kinsan yanda kike biyana”. Nana takai mishi kiss abaki “just tell me I promise zamu hadu a hotel anjima kafadan min”. PA yace “flight din karfe 2:30 zaibi na rana ” Nana ta suri jakarta tafita daga dakin da sauri.
“Nariga nasan matsalar ki,maikike so yanzu ama Barraq abin kaunar ki?” Nana tai shiru tana tunani kafin ta sauke ijiyan zuciya “Bokana inaso ama Barraq abunda zaisa Mamarshi ta koroshi daga Russia, matar tashi ta tsaneshi,ta tsorata dashi,ya shiga cikin damuwa, sanan yazamto mai yawan bukata yanda zan samu shiga a wurinshi  da wuri takuma sauki”
Boka yay ihu ya bugi kasa maiyake zuciyarki ayanzu dakikafi so amishi,dannaga akwai abunda ke ranki ?” Nana tarike haba tana tunani kafin tace “Mamar Barraq babbar mace ce a garin Russia, itace shugabar kwatar ma mata hakkinsu da yancinsu,tana fighting child abuse, dakuma issues din yima mata fyade. A garin Russia idan aka kama namiji yama mace fyade zaa kulleshi,a hukuntashu,kokuma aka kama wani namiji ya shiga mace harya yagata yay mata illa sai an hukuntashi. To plan dina anan shine karka manta inaso Mum taji haushin Barraq harta koreshi, sanan inaso yar iskan yarinyar ta wahala takuma azabtu sosai” tama boka fari da ido kafin tace”Bokana nakaina abinda nakeso shine a gusar min da hankalin Barraq, ya haukace, to a  haukacen zai afkama Rufaida ta sanadiyar wata muguwar shaawa dazaka samai,idan ya afka mata inaso ya barkata,ya zagata ta azabtu ta wahala sosai yanda zatai nadaman auren wanda nakeso, kai idan zaka iyama ka aikamin da ita lahira alokacin, ta mutu kawai sai bayan yagama hankalinshi zai dawo,to  dazaran Mum taga abinda yama yarinyar ranta zai baci, zata tsani Barraq har hakan yay sanadiyyar tace yabar mata gida kagane Bokana, karka damu biya biyu zanma dana jikina dana kudi”. tamai fari da ido boka ya washe jajayen hakoranshi angama tawan.
Yafara wasu surkulle cikin karamin lokaci wani hadadden chocolate ya bayyana a hanun Boka gwanin ban sha’awa mai kyau an rufeshi dawani irin jan Leda da akama ado da jan fulawowi  ya mikama Nana yace”ki tabbata yasha,dazaran yasha zai haukace saiyama yarinyar illa zai dawo hayyacin shi” Nana ta mika hannu ta karba tanamai shu’umin murmushi tasaka acikin jaka kafin su shige daki dan mishi biya na farko.

Barr Barraq tsaye a haraban gidansu yana magana da Dad. bayan sun gama maganan yakaraso inda PA ke tsaye rike da jakarshi Barr yabude mota ya shiga  “mutafi” PA yasa jakar a boot yadawo gaban mota ya xauna yana kokarin kunna mota  Barr yace”Oops  na manta wani Abu, abunda nasaima matata bari na dauko”. PA yay murmushi Barr yafita daga motar. fitarshi keda wuya PA yaciro wayarshi yay dailing number Nana ringing daya ta dauka yace “kina ina dan gashinan harya shirya zan kaishi airport sai wani murna yake dan iskan tuzurun ?” Nana ta tabe baki tana taunar cingam “ina Airport mana ina jiranku” kashe wayan yay da sauri hango Barr na tahowa yana shigowa yaja motar sai Airport.
Parka motar PA yayi a parking space da aka tanada a airport Barr ya fito yana gyara eyeglasses dinshi ya karbi jakarshi  yanama PA murmushi ya mikamai hannu suka gaisa yace”thanks,I appreciate everything dakakemin,shawarwarin ka,da taimakona da ayyuka dakeka thanks,saina dawo” yazaro sabuwar check din dubu dari biyar ya mikamai PA ya karba yay godiya yaja mota yatafi. ahankali Barr ke tafiya cike da natsuwa jin ance “Barrister “yasa ya juyo da kanshi ganin Nana tsaye cikin kayan arna da gashin doki yasa yajuya da sauri yacigaba da tafiya. Tasha gabanshi ta tsugunna tana haki tahade hannayenta tana rokanshi  “Barr dan girman Allah ka saurare ni, kadena wulakantani plz” Barraq ya kalli agogon hanunshi da yanda mutane ke kallonsu yace”wot?Me kikeyi anan bazaki rabu daniba am married,so no chance and no  space 4 yhu  ” Nana tafara kuka sosai “I know nasan kai aure,nasan ka tsaneni nakuma hakura dakai amma son danake ma yasa naimaka chocolate da kaina a matsayin gudunmawana na auren ka. “And who d heck told you I need ur chocolate, look Nana am sick of ur drama, ki matsamin daga hanya na wuce” yabi ta gefenta zai wuce ta kama rigarshi tana kuka sosai mutane suka soma taruwa a wurin “Dan Allah ka karba,idan harka karba kaci at least zanji dadi dudda baka soniba amma kaci wani abu da hannuna yahada Barraq” tafashe da kuka sosai wanda hakan yadan taba zuciyan Barraq mutane suka taru ana kallonsu ahankali Barraq ya juyo ya mika mata hannu “kawoto” da sauri ta share hawaye ta dauko daga jaka  ta bashi “nagode Barr, zakaci ko?,dan Allah kaci”. Barraq yadade yana kallonta kafin ya gyada mata kai “zanci”ya bude jakar laptop ya saka ciki yay maza ya bada ticket dinshi yay sama.
Karfe 4 narana ya sauka agarin Russia. Mum tai mamakin ganinshi dan baifada mata zuwan shiba, sai kalle kalle yake kozaiga Rufaida Mum tai murmushi tace”O ur wife,bata dawo daga school ba,Driver yaje daukota” ya tashi bari naje nai wanka” Mum ta kalli agogo “am going out son,inada meeting  sai 6 zamu fito, ga lunch dinka a dining ” akasalance yace”ok Mummy, bari nafara wanka nahuta xanzo naci saikin dawo” tareda Mum suka fito Mum ta shiga mota shikuma ya shiga dakinshi.
Fitan Mum keda wuya motar kai Rufaida school ta shigo. fitowa tayi ahankali dauke da jakarta abaya tana tabe baki dakinta ta wuce direct ta cire kayan makarantar ta shiga bayi ta watsa ruwa. tana fitowa ta zira wata yar shimi iya guiwa pink ta ta kama bakin jekar all back din da aka mata guda biyu da pink rubber band tafito tana kwallama Mum kira tun kafin takai dakinta. Lidya tace Mum tafita taje meeting. Fadawa kan kujera tayi ta zauna “am hungry ni Wlh” Lidya tai dariya toga abinciki chan a dining Rufaida ta mike tsaye taje dining tabude kulolin ta maida tarufe batacema Lidya komi ba tawuce kitchen indomie biyu ta dauko da kwai biyu sai bake beans tahada tadafa indomie. Tana gamawa ta juye a karaman bowl mai kyau nacin abinci tadau fork tafito daga kitchen din tana rera yar waka tana tafiya tanakuma kokarin debo indomie da fork taci, tsayawa tayi agaban dining tabama dining baya ta zuba abakinta tahadiye murmushi tayi ahankali tace”yummy ” ta maida fork din cikin indomie  tayi hanyar dakinta. “Baby” dataji an kira ahankali yasa ta waigowa,ganin Barraq yana zaune a dining yana mata wani sassanyar kallo dauke da murmushi yasa jikinta yafara rawa ta zaro ido tana kallonshi. Ahankali yasa hannu yature abincin gabanshi ya mike tsaye yafara tafiya ahankali harya iso gabanta ya tsaya yana kare mata kallo daga sama har kasa. indomie hanunta tasaki ya bare a kafarta ihu tasaki saboda zafi ta rikeshi tana kuka.
Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 16:13
In Hausa Novels
Kaine Sirri Na Part 11 Title : Kaine Sirri Na Part 11
Description :                     Fitowa sukayi daga cikin motar Amma ta rike hannu Rufaida datake shirin kuka tana kallon Mum, Mum ta girgiza mata kai a...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Kaine Sirri Na Part 11"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ▼  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ▼  September (199)
      • Graphic Photos: Sojoji Sun Ceto Wasu Mata Da Aka Y...
      • An Damke Mahaifi Da Yima Diyar Sa Fyade
      • Mijin Haya Part 18
      • Photos: Sunlight Laraba's World Tv Drama Series Hu...
      • Photos: Sheik Isa Aliyu Pantami Ya Shiga Ofis A Yau
      • Buhari Ya Taya Zababben Gwamnan Edo Murna
      • Photos: Jami’an Tsaro Sun Kulle Ofishin Abdulmumin...
      • Dan Takarar Gwamnan Na APC A Jihar Edo Ya Lashe Zabe
      • Photos: An Haifi Wani Jariri Mai Kama Da Tsoho
      • Photos: Mutane Shida Sun Rasa Ransu A Wani Gidan K...
      • Abdulmumini Jibrin Ya Kai Kara Majalisa Wakilai Kotu
      • MIjin Haya Part 17
      • Majalisar Wakilai Ta Dakatar Da Abdulmumini Jibrin...
      • Kaine Sirri Na Part 23{END}
      • Photos: El Rufai Ya Sanya Danshi A Makarantar Gwam...
      • Al'ajabi: An haifi Jariri Mai Iyaye 3 A Kasar Mexico
      • Wani Yaro Dan Shekara 11 Yayi Fyade A Kasar Ingila
      • Mijim Haya Part 16
      • Buhari Ya Umarci Tambuwal Ya Sulhunta Tinibu Da O...
      • Kaine Sirri Na Part 22
      • Bankin Afirka Zai Tallafa Wa Najeriya Da $10b
      • Video: I LOVE YOU By CLASSIQ FT AVALA starring Rah...
      • Mijin Haya Part 15
      • Ban Yi Tsufa Da Auren Zahra Buhari Ba - Gwamnan Za...
      • Wani Kurma Ya Yi Fyade Wa 'Yar Wata Shida A Yobe
      • Na Hakura Da Mukamin Shugaba A Jam'iyyar APC. Bana...
      • Kaine Sirri Na Part 21
      • Kaine Sirri Na Part 20
      • Photos: Hanun Wani Matashi Ya Makale A Jikin Kur'a...
      • Photos: Sojojin Nijeriya Sun Kashe 'Yan Boko Haram...
      • Mijin Haya Part 14
      • Video: Rahma Sadau Ta Ziyarci India
      • Ina Nan Garau Da Raina - Abubakar Shekau
      • An Kashe Marubuci Da Yayi Ridda' a Jordan
      • Photos: Aisha Buhari Ta Ziyarci Ingila
      • Kaine Sirri Na Part 19
      • Wani Ma'aikacin EFCC Ya Karbi Cin Hancin Miliyan 15
      • MIjin Haya Part 13
      • Kaine Sirri Na Part 18
      • Photos:Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Wa Yarsa F...
      • Tsagerun Niger Delta Sun Kai Hari A Garin Bonny
      • Mijin Haya Part 12
      • [Daga Jama'a] Dalilai Goma (10) Da Yasa Nake Son A...
      • Kaine Sirri Na Part 17
      • ISIS Sun Hana Yan Kasar Iraqi Sa Rigar Kwallon Kaf...
      • Naga Rayuwa Part 2
      • Naga Rayuwa Part 1
      • Yar Amana Part 3
      • Yar Amana Part 2
      • Wani Lauya Yakai Karan BuhariI A Kotu
      • [New Music] KU TARE BURGU YA GUDU By RARARA
      • Gwamnoni Da Ministoci Sun Amince Da Sayar Da Kadar...
      • Mijin Haya Part 11
      • Photos: Sabin Hotunan Nafisat Abdullahi
      • Zan Siya Kungiyar Kwallon Kafan Arsenal Nan Da She...
      • Kaine Sirri Na Part 16
      • Wani Dan Aikin Turai Yar’adua Ya Sace Mata Naira M...
      • Sabuwar Girgizar Kasa Ta Sake Faruwa A Kaduna
      • Mijin Haya Part 10
      • Kaine Sirri Na Part 15
      • Photos:An Kama Wani Tsohon Na Shirin Lalata Da Wat...
      • Photos: Barayin Shanu Sunyi Hadari Da Shanun Da Su...
      • Mafarki A Lokacin Jinin Haila
      • Yar Amana part 1
      • MIjin Haya Part 9
      • Photos: Sarkin Kano Ya Halarci Taron Sulhu Na Duni...
      • Kaine Sirri Na Part 14
      • Photos: Aisha Yayin Bada Lacca A New York
      • Mijin Haya Part 8
      • Photos: Sabin Hotunan Sadiya Gyale
      • Photos: Yan Bindiga Sun Sace Wata Malama Makaranta...
      • Photos: Yau Ranar Murna Haihuwa Yar Sarkin Kano Sa...
      • Kaine Sirri Na Part 13
      • Buhari Ne Matsalar Kasar Najeriya - Ayo Fayose
      • Mijin Haya Part 7
      • Photos: An Nada Wata Budurwa A Matsayi Shugaban Ka...
      • Photos: Sabin Hotunan Jaruma Nollywood Tonto Dikeh
      • Ya Kamata A Haramtawa Barayin Gwamnati Shiga Harka...
      • 'Yar Najeriya Saheela Ibrahim Ta Shiga Sahun Matas...
      • Kaine Sirri Na Part 12
      • Graphic Photos:Anyi Rikici Tsakanin Matasa Da Yan ...
      • Photos: Halima Da Zahra Buhari Sun Halicci Wani Bi...
      • MIjin Haya Part 6
      • Ibrahim Shema Ya Mika Kansa Wa EFFC
      • Kaine Sirri Na Part 11
      • Saeed Nagudu Na Shirin Waka Da Wizkid
      • Fatima Part 1
      • Fatima Part 2
      • Photos: Sojojin Najeriaya Sun Mika Iyalan Boko Har...
      • Sojojin Nijar Da na Chadi Sunyi Nasara Akan Boko H...
      • Photos: Dangote Da Yarsa Halima A Bikin Ranar Murn...
      • Mijin Haya Part 5
      • Photos: Halima Atete Da Fati Nijar A Makka
      • Za A Yi Afuwa Da Tsagerun Niger Delta Sama Da Dubu...
      • Kaine Sirri Na Part 10
      • Photos: Ku Ga Babba Maciji Da Wani Mutum Ya Kashe ...
      • Mijin Haya Part 4
      • Photos: Yan Sanda Sun Cafke Yan Fashin Da Suka Yi ...
      • An Dakatar Da Limamin Masallacin Juma'a Na Sultan ...
      • Kaine Sirri Na Part 9
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • Zuwa Da Budurwa Yawon Duniya ( Kalli Kaci Dariya)
  • Rikicin Tsakanin Hadiza Gabon Da Zaharadeen Sani ( Bayanai Da Rahoto) S...
  • The Missing seven-year-old boy found dead in Kano
    Seven-year-old Khalifa Saminu Saleh was tragically found deceased six days after he was reported missing in the Kuruma community...
  • Sadiya Gombe Ft Al'ameen Bauchi (Ra'ayin Ki Ne Nawa) Sabuwar Waka
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Zanga-zanga A Bauchi-Gwamnatin Ta Saka Dokar Hana Fita Da Zirga-Zirga Ac...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger