1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Uncategories » Allah Ya ISA Ban Yafe Ba Part 14

Allah Ya ISA Ban Yafe Ba Part 14

By Abdul Mk
Add Comment
Wednesday, 23 March 2016


.
"Ka yi qoqari, ai ba duka masu kudi suke yin abubuwa da kansu ba" in ji Jummai daga nan ta duqar da kai qasa ba ta sake cewa komai ba, ganin haka YM Bello ya dan damu, har ya tambaye ta, ita kuma ta ce masa ba komai, amma da ya matsa mata da tambaya sai ta ce "Ka san tun haduwarmu da kai har yau dinnan ba mu tattauna wani abu mai mahimmanci ba, alhali akwai wasu abubuwa masu matuqar mahimmancin gaske da nake so mu dan tattauna da kai domin dauwamar wannan soyayyar da ganin dorewarta, to amma ban san ta yadda zan fito musu ba, ina so ne na yi maka bayani filla-filla cikin 'yan kalmomi qalilan ba masu yawa ba"
.
YM Bello bai san irin tambayar da za a yi masa ba, ko tun farko ya nuna ba ya son tattaunawa kan maganar aure, ya ce soyayyarsu jaririya ce a bar ta ta dan girma tukun, da yake yanzu ta matsa tana son yin magana sai ya ce "Ki daure ki taqaita, sannan ban da karin magana, kin san ban fahimtar sarqaqqiyar magana, gwara dai Turanci, don in kin cire yawan zuwa qasashen Turai da mutum yake yi, galibin maganata duk da Turancin ne" "Tabdijan" inji Mari "Ashe Larabci ma har da na zubarwa kenan, ko ba ka zuwa qasashen Larabawa ne?"
.
To da yake YM Bello bai da haske ta wannan bangaren, kuma yana da tabbacin cewa galibin 'yammata suna suna yawan zuwa Islamiyya sai ya ce "Ina dai da yara masu zuwa qasashen Larabawa, ni ban cika zuwa ba, don yanzu duniya ta rikice gaba daya, in ka cika yawan zuwa wadannan qasashen yanzu sai a zarge ka da ta'addanci, ko a ce kana sufurin makamai, so Turanci kawai, ko ba komai mutum zai samu zama lafiya" Maganar ta so ta ba wa Mari mamaki, wato dai akwai yuwuwar ko zama a qasar ba zai yi ba nan gaba.
.
Jummai kuwa kallonsa ta yi da gefan ido ta yi wani dan murmushi mai daukan rai ta ce "Allah ya jiqan Baban Manar ba don ya mutu ba, wallahi kullum na tuna waqarsa ta Hausa sai na ji qaunar harshen ta dada kurdawa cikin zuciyata, na ji ba harshen da yake da hikima da fasaha kamar Hausa, shi ba Larabci ba ne amma yana qumshe da wasu abubuwa wadan da ba in da za ka same su sai a cikinta, akwai mawaqa da yawa a wannan qasar tamu, kamar su Aliyu Namangi Zaria, Aliyu Aqilu, Mudi Sipaka, Yusuf Aliy Tudun Maliki da sauransu"
.
Mari ta fara zungurinta da gwiwar hannu, tana nufin ta yi shuru, sai dai rashin sa'ar da aka yi YM Bello ya riga ya gani, sai ya tsaya kai da fata sai Jummai ta rera masa waqar, ita kuma ta qi, nan fa ya bata rai "To wa ma ya sani ko alaqar da take tsakaninku ta wuce ta waqa da jin dadinta? Ni ba ma wannan ba, shin waqar kike bege ko mai waqar?" Mari ta kalle ta da gefen ido kan cewa ta waske, to amma Jummai ba ta gani ba, ba ta ma gano cewa YM fa kishi yake ba, don haka ba wani abin da ya dame ta bare ta yi maganar ba shi haquri, tunaninta kawai ba ta iya rera waqa ba.
.
Ta dan juyo ta kalle shi "Idan na rera maka za ka ga kamar da kai nake yi, kuma wallahi literature ce kawai, ka san ni Hausa na karanta" YM ya girgiza kai "No! No!! Kwantar da hankalinki my dear, ni ban da wannan dabi'ar, sau nawa ina halartar Poets' Conference a Wales ta UK? Ba ki da mafita, sai kin karanto min waqar Baban Manar a kan Hausa don ban gama gamsuwa da abin da ta qumsa ba" Jummai ta sunkuyar da kai ta fara rerewa:-
.
"Gali da Galiya ku zan dora fadinta
Hausa a ko'ina ka je za ka ishe ta
Bar su American da Chech har su Jakarta
Ba bu qasar da za ka ce ba a fadinta
Sai ko mai fadinta ne ba a kulawa.
.
Rana ta fito duhu sai ya kwaranye
Kai mai gardaman hakan dole ka janye
Ko banza Sule Biyar ya dara ganye
In ka hada da sannu za mu yi rinjaye
Ruwa da wuta ku san da dai ba a hadawa.
.
Hausa a ko'ina na je ke na fi qauna
Don kin zarce harsuna kab a wurina
Dan maraqina ya fi garke na wanina
Dan kowa a ko'ina bai wuce dana
Haka harshen gari da dai bai wuce nawa.
.
Ya qi gida ku ce da shi "ka zama wawa"
Sai qauna kake ka zam dan Turawa
Ka bar salsalarka ma ba ka tunawa
Kai kullum fadi kake ban komawa
Ko an kai ni tabbatar ban zaunawa.
.
Hausa uwa, uba wurin masu fadinta
Kalmomin cikinta duk masu nagarta
Kai da jiyota za ka san babu irinta
Ni zan so ka zam cikin masu iyata
Ko an tashi hargitsi ba ka macewa."
.
"Iyakanta kenan?" In jishi, ta girgiza kai "A'a da saura, na dai karanto maka dalilin da ya sa nake qaunar waqan ne, don gaskiya yana da kyau mutum ya san martabar harshensa, kuma ya iya, tun da shi ya haife shi kuma har abada ba zai sami kamarsa ba" Mari dai ba ta iya cewa komai ba, don a ganinta bai dace Jummai ta karanto wadannan baitocin ba matuqar tana son alaqarta ta yi qarfi sosai da YM Bello, masamman yadda ta ga kamar ransa ya dan baci, Mari ta gama karantar YM sosai, shi Nigeriar gaba daya ba ta yi masa ba, to bare kuma wata Hausa.
.
"YM ka san maganar da nake so mu yi kuwa?" Inji Jummai, ya kamata a ce ta sami lokacin da ya fi wannan dacewa, to amma rashin kula bai bar ta ba, shi dai ya ba ta amsa da cewa "No!" Ta ce "Ina so ne mu dan juya wannan zancen ya koma wurin da ya fi dacewa, don wallahi ana min fada a gida, wai don me nake barin qofar  gidammu zuwa wani wuri, sannan na zauna da wani saurayi? Ko last week ma da kazo sai da mamanmu ta ce na gaya maka tana son ta gan ka don ku tattauna wasu abubuwa masu matuqar mahimmanci wadan da suka shafi alaqarmu, kawai na kasa gaya maka ne"
.
YM ya dan yi murmushi "Da ni da Baban Manar din zamu tafi ko ni daya?" Mari da Jummai suka hada ido kowa ta bude baki, a lokacin ne ma Jummai ta fara gano cewa ta fa yi subutar baki, a daidai wannan gabar lamarin ya kasu mata zuwa gida biyu, shin za ta tsaya ba shi haquri ne, ko za ta share ne ta koma maganar ganawarsa da mahaifanta? YM zai iya yin amfani da wannan damar wajen kawar da batun da ake ciki, ita kuma Jummai babu wata alamar wasa a tare da ita.

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 09:06
Title : Allah Ya ISA Ban Yafe Ba Part 14
Description : . "Ka yi qoqari, ai ba duka masu kudi suke yin abubuwa da kansu ba" in ji Jummai daga nan ta duqar da kai qasa ba ta sake cewa k...
Rating : 5
Related Posts:

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Allah Ya ISA Ban Yafe Ba Part 14"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ▼  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ►  April (89)
    • ▼  March (128)
      • Photos: Musulmi Ya Koma Haushin Kare Bayan Ya Je C...
      • Azal Part 6
      • Azal Part 5
      • Ana Sharrin Tsige Shugaba Kasar Afirka Ta Kudu
      • Photos: Buhari Ya Isa Birnin Washington
      • Photos: Daga Wajen Jana'izar Kanal Suma'ila Inusa
      • Ko Mahaifina Ya Zagi Buhari Sai Na Zage Shi - Wan...
      • Photos: Yan Shi'a Sama Da Dubu Goma Sunyi Zanga-Za...
      • Sojojin Najeriya Sun Hana 'Yan Shi'a Yin Taro A Ka...
      • Gwamnatin Kano Ta Shiga Batun Farashin Ruwan Leda
      • Gobara A Kasuwar Ikom Dake Jihar Cross River
      • Yanda Zaka Sace Zuciyan Yarinya.
      • Anyi Taron Marubuta Litattafan Hausa A Kano
      • Kachikwu Ya Ba Yan Nijeriya Hakuri Akan Matsalar M...
      • Photos: Atiku Abubakar Yayin Ci Abinci Da Yan Gudu...
      • Graphic Photos: Sojoji Sun Katse Harin 'Yan Boko H...
      • An Kashe Hafsan Sojan Da Aka Sace
      • Gaskiya Buhari Ya Yi Matukar Taka Rawar Gani Wajen...
      • Photos: Obasanjo Ya Ziyarci Jihar Borno
      • Bola Tinubu Ya Caccaki Ibe Kachikwu Akan Matsalar Mai
      • Wata Budurwa Ta Sa An Kashe Wani Dan Acaba
      • Photos: Daga Wajen Bikin Producer Kannywood Abdul ...
      • Photos: Sabin Hotuna Rahma Sadau
      • A Daina Sa Wa Gwamnatin Bubari Ido - IBB
      • Photos: Ganduje Ya Ziyarci Kasuwar Sabon Gari
      • El-Rufa'i Da Mataimakin Sa Sunyi Mare-Mare
      • Sheik Sani Yahaya Jingir Na Raye Bai Mutu Ba
      • Gobara Ta Tashi A Kasuwar Sabon Gari A Jihar Kano
      • Photos: Sojojin Najeriya Sun kashe Yan Boko Haram ...
      • Matsayain Zawarawa Da 'Yan Mata A Gwamnatin Ganduje
      • Photos: El-Rufai Ya Gana Da Yan Wasan Super Eagles
      • Boko Haram Sun Sace Mata 16 A Garin Madagali
      • An Daure Adam Johnson Shekara Shida
      • Photos: Anyi Hukunci Ma Wasu Mazinata Uku A Kasar ...
      • Video: Abubakar Shekau Ya Mika Wuya
      • Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Kwamitin Da Za Ta Bin...
      • Hukumar Kwastan Ta Sake Hana Shigo Da Shinkafa
      • Allah Yana Fushi Da Buhari - Fayose
      • Majalisa ta zartar da kasafin kudin 2016
      • Gwamnatin Tarayya Za Ta Sanya Naira Bilyan 350 A F...
      • Allah Ya ISA Ban Yafe Ba Part 14
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 15
      • An Zargi Gwamnatin Jihar Bauchi Da Karbar Na Goro ...
      • Video: Sasanta Ganduje Da Kwankwaso
      • A Gaban Idona Sojoji Suka Hallaka 'Yan Uwana Uku, ...
      • Buhari Ya Bukaci Bankuna Su Baiwa Manoma Rance Dom...
      • Sojojin Najeriya Sun Kashe Yan Boko Haram 58 A Kau...
      • Gwamnatin Buhari Ta Kwace Kadororin Tsofin Gwamnon...
      • Hukunci Wanda Ya Kashe Dan Fashi
      • Graphic Photos: Barayin Shanu Sun Kashe Mutane 20 ...
      • Photos:Gwamnonin Arewa Maso Yamma Sun Daidaita Tsa...
      • Photos:Gwamnonin Arewa Maso Yamma Sun Daidaita Tsa...
      • Yan Shi'a Sun Gurfanar Da Sojojin Najeriya Gaban K...
      • Majalisar ASA Na Shirin Yin Fito Na Fito Da Buhari
      • Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamna Jihar Bauchi
      • Ali Nuhu ya mika kyautar Tijjani Ibrahim
      • Wayar Sakataren Majalisar Musulunci Ta Duniya Ta Y...
      • Izala ta Karyata Jita-Jitar Sace Wayar Shaihun Mal...
      • Photos:Gwamna Jihar Kogi Tare Da Matan Sa Uku
      • Abu Daya Ya BamBanta Mulki Buhari Da Na Fir'una - ...
      • Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Kwamishina Na J...
      • Yan Bindiga Sun Halaka Mutane Da Dama A Jihar Zamfara
      • Gwamnatian Jihar Borno Ta Rushe Kantomomin Kananan...
      • Gwamnatin Kano Ta Sake Baiwa Wata 'Yar Fim Din Hau...
      • Azal Part 1
      • Azal Part 2
      • Azal Part 3
      • Azal Part 4
      • Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Yi Afuwa Ga Fursunoni 56
      • Ganduje Ya Caccaki Kwankwaso
      • Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutane 22 A Wani Ma...
      • An Gano Ma'aikatan Bogi Dubu 22 A Jihar Bauchi
      • Photos: Buhari Ya Isa Kasar Equatorial Guinea
      • Kasar Masar Ta Tsige Ministanta Kan Batanci Ga Ann...
      • Photos: Daga Wajen Bikin Kannywood Award
      • Bama-Bamai Sun Tashi A Cameroun
      • Kungiyar Matasa Magoya Bayan Buhari Sun Karrama Ba...
      • Ganduje Na Shirin Kai Kwankwaso Gaban EFCC
      • Harin Bam Din Kunar Bakin Wake Ya Raunata Sojoji U...
      • An Dawo Da Ruwan Sha Na Dauri A Jihar Sokoto
      • Yar Amana Part 15 (Karshe)
      • Graphic Photos: Mutane 18 Sun Rasa Ransu Sakamakon...
      • Ana Musayar Wuta Tsakanin Sojoji Da 'Yan Boko Hara...
      • Yar Amana Part 14
      • Na Karbowa Faruk Lawan Dala Dubu 100 Daga Wurin Ot...
      • Yar Amana Part 13
      • Aljanu Basu Son Azkar Din Safe
      • Photos: An Kashe 'Yan Boko Haram Da Dama A Jihar B...
      • Ina Sane Da Mawuyacin Halin Da Ake Ciki A Kasar Na...
      • Photos: Ministan Kwadago James Ocholi Ya Mutu A Ha...
      • Yanda Zaka Saya 1GB Da 3GB Akan N200 Da N500 A Lay...
      • Yar Amana Part 12
      • Hukumar SSS Ta Kama Masu Yi Wa Boko Haram Safarar ...
      • Yunwa Da Matsin Lamba Ta Soma Sanya 'Yan Boko Hara...
      • An Gano Iyayen Yarinyar Da Ta Bace A Tsakanin Kadu...
      • Maganin Matsalar Ciwon Fitsari
      • Yar Amana Part 11
      • **AL‘AJABI part 20*
      • Al'ajabi Part 19
      • Gwamna Ganduje Na Kano Ya Yi Rashin Mahaifiyarsa
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger