Kwanakin baya aka yi ta surutu game da sinadaran da ke cikin lemun Fanta da Sprite. Yanzu dai ‘Yan Majalisar Kasar sun gindaya kamfanin na Coca-Cola da ke wannan lemu wasu sharadi. An kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kara tashi tsaye.
Da farko dai an nemi Hukumar NAFDAC da ke kula da magunguna da abin ci da sha a Najeriya su tursasawa kamfuna su bayyana sinadaran da ke cikin lemun na su. A cikin sinadaran dai akwai wanda zai iya bada matsala idan aka sha da Bitamin C.
‘Yan Majalisar Tarayya sun nemi masu yin lemun a Najeriya su gargadi duk wanda ya saye kayan su ta hanyar bayyana sunayen irin abubuwan da yake kwankwada. Wannan dai zai sa jama’a su cire shakka sannan kuma an yi adalci wajen kasuwanci.
Shugaban masu rinjaye a Majalisar Femi Gbajiamilla yayi bincike game da wannan lamarin inda jama’a su koka da cewa akwai abubuwa masu illa a lemun Fanta da Sprite. Masu yin lemun kan sa wasu sinadaran fiye da kima a lemun kasar nan.
Source :naij hausa
Title :
Yan Majalisa Sun Gindaya Wa Kamfanin Coca Cola Sharuda
Description : Kwanakin baya aka yi ta surutu game da sinadaran da ke cikin lemun Fanta da Sprite. Yanzu dai ‘Yan Majalisar Kasar sun gindaya kamfanin na C...
Rating :
5