Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, yace mutuwa ce kadai zata iya hana ci mulkin kasar Saudiyya.
Yarima Mohammed bin Salman, ya bayyana haka ne a wata hirar da yayi da manema labarun gidan Talabijin din CBS a washe garin ranar ziyarar sa ta farko zuwa kasar Amurka.
“Allah na kadai yasan wanda zai dade a duniya, amma idan abubuwa suka tafi kamar yadda aka tsara su, tabbas zan zama shugaban kasar Saudiya,” inji Mohammed bin Salman Salman.Da aka tambaye shi cewa, mai yake ganin zai iya hana shi zama shugaban kasar Saudiya, sai yace, Mutuwa.
Tunda Mohammaed Bin Salman, ya samu mukamin yarima mai jiran gado ya fara kawo sauye-sauye al’adu kasar Saudiyya.Manyan kasashen duniya musamman na turawa suna daukan Mohammaed Bin Salman, a matsayin mutimun da ya kawo wa kasar Saudiyya canji.
Source :naij hausa
Title :
Mutuwace Kadai Zata Hanani Mulkan Saudiyya - Mohammed Bin Salman
Description : Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, yace mutuwa ce kadai zata iya hana ci mulkin kasar Saudiyya. Yarima Mohammed bin Salman, ya bay...
Rating :
5