A yau dinnan ne za a fito da sakamakon mutane sama da Miliyan 1 da su ka rubuta jarrabawar JAMB a Ranar Asabar din ta wuce. Wani babban Jami’in Hukumar Dr. Fabian Benjamin ya bayyanawa manema labarai wannan jiya.
Hukumar ta sanar da cewa a yau Litinin za a saki sakamakon mutane miliyan 1.3 bayan an tabbatar da cewa babu wani ha’inci a jarrabawar. A wasu dakunan jarrabawar an karbi kudin ‘dalibai domin a taimaka masu da satar amsa a jarrabawar.
JAMB dai za ta rike sakamakon wadanda su ka tafka rashin gaskiya a dakunan jarrabawar. Akwai ma dai inda aka yi barazana ga rayukan wadanda su ka je sa-ido a jarrabawar don haka su kayi tsit yayin da ake ta buga satar amsa a dakin gwajin.
An dai soke jarrabawar wanda aka samu tsamo-tsamo da laifin satar amsa a shekarar bana da na'urar hoto. Wadanda dai aka yi ta barna a dakin jarrabawar su amma ba su shiga ciki ba za su sake rubuta jarrabawar a nan gaba kadan a wasu dakunan dabam.
Source :naij hausa
Title :
Ansoke Jarabawar Wadanda Aka Kama Da Satar Amsa A Jarabawar Jamb
Description : A yau dinnan ne za a fito da sakamakon mutane sama da Miliyan 1 da su ka rubuta jarrabawar JAMB a Ranar Asabar din ta wuce. Wani babban Jami...
Rating :
5