Hukumar yan sandan Najeriya a ayu Litinin ta damke yan daba 2 wadanda ke yiwa sanata mai wakiltan mazabar Kogi ta yamma a majalisan dattawa, Dino Melaye, domin kawo rikici lokacin zaben 2019.
Kakakin hukumar yan sandan, Jimoh Moshood, ya bayyana yan barandan masu suna Kabiru Saidu wanda akafi sani da Osama da Nuhu Salish, da jami’an SARS suka damke a jihar Kogi ranan 19 ga watan Junairu 2018 a Ogujeje, karamar hukumar Dekina na jihar Kogi.
Ya ce yan barandan sun bayyana da bakunansu cewa su mambobin wata kungiyar masu garkuwa da mutane ne kuma sunawa yan siyasa banga a jihar.A yayin bincike, Saidu ya kasance dan bangan siyasa ga Mohammed wanda ya hada shi da Sanata Dino Melaye kuma suka hadu a Abuja.
Kakakin hukumar ya sanda yace: “ Yan barandan sun bayyana da bakunansu cewa Dino Melaye ya fada musu cewa su fara masa aikin bangan siyasa kuma su nemi abokansu domin yi masa aiki a zaben 2019.”
Source :naij hausa
Title :
Ankama Masu Garkuwa Da Mutane Dake Aiki Wa Dino Melaye
Description : Hukumar yan sandan Najeriya a ayu Litinin ta damke yan daba 2 wadanda ke yiwa sanata mai wakiltan mazabar Kogi ta yamma a majalisan dattawa,...
Rating :
5