Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar Borno ta bayar da umurnin rufe dukannin makarantun sakadare na kwana da ke wajen garin Maiduguri.Hakan ya biyo bayan sace yan matan makarantar Dapchi da yan ta’addan Boko Haram suka yi a jihar Yobe.
Kwamishinan ayyukan cikin gida, yada labarai da al’adun gargajiya na jihar, Muhammed Bulama ne ya bayyana da hakan a ranar Laraba inda ya kara da cewa gwamnati ta dauki wannan matakin tare da wasu matakan inganta zamantakewar mutanen jihar tun a wani zama da kwamitin tsaro da ya hada da jami’an tsaro, sarakunan gargajiyya da wakilan gwamnatin suka fara yi ranar 15 watan Maris.
Sauran matakan inganta rayuwar mutane da gwamnati ta dauka sun hada da:
1. Samar da tsaro a kananan hukumomin Bama, Gwoza da Dikwa kafin a fara dawowa da ‘yan gudun hijira dake zama a garuruwan.
2. Bude hanyar Maiduguri – Bama – Banki wanda ta yi shekaru uku a rufe.
3. Hukunta duk wanda aka kama yana taimaka wa Boko Haram baya.
4. Bude wuraren rajista da na’ura wa maniyata aikin hajjin bana, da dai sauran su.
A halin da ake ciki mahaifin dalibar Dapchi da ta rage a hannun yan ta'addan Boko Haram ya bayyana cewa ya ji dadi da yarsa batayi ridda daga addinin Kirista zuwa Musulunci ba.
Source :naij hausa
Title :
Anrufe Makarantun Kwana A Jihar Borno
Description : Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar Borno ta bayar da umurnin rufe dukannin makarantun sakadare na kwana da ke wajen garin Maiduguri.Hak...
Rating :
5