Dakarun Birgade 23 na Operation Lafiya Dole sun kama wani dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, Bubayi Isa daga kauyen Panama, yankin Gundam, karamar hukumar Biu dake jihar Borno a jiya.
A wata sanarwa dauke das a hannun Birgediya Janar Texas Chukwu, daraktan labaran rundunar sojim ya bayyana cewa kamun ya biyo bayan wani farmaki.
Chukwu ya kara da cewa bincike ya tabbatar da cewa Bubayi ya kasance daya daga cikin yan ta’addan Boko Haram 37 da rundunar soji ta buga sunayensu.
Sauran da aka kama tare das hi sune Muhammad Buba da kuma Abdullahi Abubakar daga yankin yayinda Yakubu Abdullahi ya fito daga Sabon Gari Gado a karamar hukumar Bayo shima a jihar Borno.
An kama yan ta’addan ne a kauyen Kalaa dake karamar hukumar Hong na jihar Adamawa.
Yan ta’addan sun amshi bakin cewa su yan kungiyar Boko Haram ne sannan sun bayyana irin ta’assar da sukayi bayan bincike da rundunar sojin ta gudanar.
A halin yanzu, gwamnatin jihar Borno ta bayar da umurnin rufe dukannin makarantun sakadare na kwana da ke wajen garin Maiduguri.
Source :naij hausa
Title :
Sojin Sama Sun Kama Wani Babban Da Boko Haram Da Aka Jima Ana Nema Ruwa A Jallo
Description : Dakarun Birgade 23 na Operation Lafiya Dole sun kama wani dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, Bubayi Isa daga kauyen Panama, yankin Gun...
Rating :
5