Wata ganawar sirri da aka ruwaito ya gudana a tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta cigaba da tayar da kura a farfajiyar siyasar Najeriya.
Sai dai a sakamakon cece kucen daya dabaibaye batun, jaridar Daily Trust ta tuntubi wata hadimar Kwankwaso, Hajya Binta Sipikin, inda ta musanta wannan batu, indsa tace Kwankwaso na cikin garin Kaduna.
“Kwankwaso bai yi wata ganawa da Obasanjo ba a jihar Legas, ina tabbatar muku da cewa Kwankwaso na jihar Kaduna, inda yake ganawa da masu ruwa da tsaki na kungiyar Kwankwasiyya, don haka duka yamadidin da ake yawada game da haka kanzon kurege ne.” Inji ta.
Sai dai majiyar jaridar naij ta ruwaito Sipikin tana cewa tsananin kauna ce tasa yan Najeriya, musamman masu bukatar ganin canji na hakika ke neman jin inda Kwankwaso ya fuskanta, don yayi musu jagora, suna biye da shi a baya.
Hakazalika, shima wani na hannun daman Kwankwaso,Dakta Yunusa Dangwani yace basu san daga ina labarin nan ya fito ba, inda yace su kansu a shafukan jaridu suka karanta.
“Bamu boye boye a al’amuranmu na siyasa, duk abinda zamu yi mukan sanar da yan jaridu, don haka a jaridu muka karanta.” Inji shi.
Source :naij hausa
Title :
Bamu Gana Da Obasanjo Ba - Kwankwaso
Description : Wata ganawar sirri da aka ruwaito ya gudana a tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon shugaban kasa Oluseg...
Rating :
5