Shugaban rukunin kamfanonin nan mallakin gwamnatin tarayyar Najeriya dake kula da albarkatun man fetur din kasar watau National Petroleum Corporation (NNPC) a takaice mai suna Dakta Maikanti Baru ya daukar wa 'yan Najeriya alkawarin cewa ba za'a kara yin wahalar mai ba.
Dakta Maikanti Baru yayi wannan alkawarin ne a yayin da yake karbar wata kyautar karramawa na 'Fitaccen mutum na shekara' da kamfanin yada labarai na NewsDirect ya bashi ya kuma bayyana cewa hakika sun koyi darasi sosai daga matsalar man da aka samu a 'yan kwanakin baya.
Jaridar naij ta samu cewa Dakta Maikanti Baru ya kara da cewa kadan daga cikin darussan da suka samu shine na cewa kada su kuskura su bari mai ya tsinke masu a tankunan ajiyar su.
A wani labarin kuma, Yanzu haka dai zazzafar muhawara na cigaba da wanzuwa a tsakanin gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya da ma ita kanta gwamnatin bisa zargin wawushe makudan kudaden da suka kai Naira biliyan 30 da ma'aikata a gidauniyar tallafawa al'ummar kasar watau Nigerian Social Insurance Trust Fund, NSITF a takaice ake zargin sun yi.
Su dai gamayyar kungiyoyin kwadagon kamar yadda muka samu tuni har sun sanar da gwamnatin tarayyar cewa dole ne ta dauki mataki kwakkwara domin ganin an hukunta masu laifin ko kuma su shiga yajin aikin gama gari nan ba da dadewa ba.
Source :naij hausa
Title :
Baza'a Kara Wahalar Mai A Nijeriya Ba - Mai Kanti Baru
Description : Shugaban rukunin kamfanonin nan mallakin gwamnatin tarayyar Najeriya dake kula da albarkatun man fetur din kasar watau National Petroleum Co...
Rating :
5