Yanzu haka dai zazzafar muhawara na cigaba da wanzuwa a tsakanin gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya da ma ita kanta gwamnatin bisa zargin wawushe makudan kudaden da suka kai Naira biliyan 30 da ma'aikata a gidauniyar tallafawa al'ummar kasar watau Nigerian Social Insurance Trust Fund, NSITF a takaice ake zargin sun yi.
Su dai gamayyar kungiyoyin kwadagon kamar yadda muka samu tuni har sun sanar da gwamnatin tarayyar cewa dole ne ta dauki mataki kwakkwara domin ganin an hukunta masu laifin ko kuma su shiga yajin aikin gama gari nan ba da dadewa ba.
Jaridar naij ta samu cewa dai a baya maganar bahallatsar ta bulla ne biyo bayan wata takardar koke da wani ma'aikaci ya aike wa da hukumar EFCC inda ya kwarmata masu yadda shugabannin ma'aikatar suka yi facaka da kudaden al'umma daga shekarar 2012 zuwa 2015.
A wani labarin kuma, Shugaban rukunin kamfanonin nan mallakin gwamnatin tarayyar Najeriya dake kula da albarkatun man fetur din kasar watau National Petroleum Corporation (NNPC) a takaice mai suna Dakta Maikanti Baru ya daukar wa 'yan Najeriya alkawarin cewa ba za'a kara yin wahalar mai ba.
Dakta Maikanti Baru yayi wannan alkawarin ne a yayin da yake karbar wata kyautar karramawa na 'Fitaccen mutum na shekara' da kamfanin yada labarai na NewsDirect ya bashi ya kuma bayyana cewa hakika sun koyi darasi sosai daga matsalar man da aka samu a 'yan kwanakin baya.
Source :naij hausa
Title :
Kungiyar Kwadago Na shirin Tafiya Yajin Aikin Gama Gari
Description : Yanzu haka dai zazzafar muhawara na cigaba da wanzuwa a tsakanin gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya da ma ita kanta gwamnatin bisa zargin...
Rating :
5