Wata Kungiyar Musulmai mai suna MURIC tayi kaca-kaca da Gwamnonin Arewa na Gwamnatin Shugaban kasa Buhari inda tace ba su da niyyar kawo karshen Almajiranci a Yankin wanda sai an kauda su za a ga karshen Boko Haram.
Shugaban Kungiyar MURIC Farfesa Ishaq Akintola ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar inda yake mai yabawa Gwamnatin tsohon Shugaba Jonathan na kokarin kawo karshen Almajiranci ta hanyar gina makarantun Al-majirai a Yankin.
Yanzu dai wadannan makarantu da Jonathan ya bude sun kama hanyar lalacewa don haka aka nemi Gwamnatin Shugaba Buhari tayi wani abu kan batun almajirai wanda su ka haura Miliyan 10 kuma ana amfani da wasu wajen aikin assha a kasar.
An dai samo asalin Almajirai ne tun daga lokacin da Manzon tsira Annabi Muhammad SAW yayi hijira. Sai dai a Najeriya an maida abin hanyar bara inda iyaye ke jefar da yaran su da sunan karatu a kan titi cikin yunwa da ruwan sama da kazanta.
Source :naij hausa
Title :
Wata Kungiyar Musulmai Tayi Allah Wadai Da Gwamnatin Buhari
Description : Wata Kungiyar Musulmai mai suna MURIC tayi kaca-kaca da Gwamnonin Arewa na Gwamnatin Shugaban kasa Buhari inda tace ba su da niyyar kawo kar...
Rating :
5