Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa ba zai bayyana matsayinsa game da 2019 ba a wannan lokaci, inda yace yin hakan yayi wuri a yanzu, duba da cewa da sauran lokaci zuwa 2019, inji rahoton Daily Trust.
Buhari yace bayyana takararsa a wannan lokaci zai baiwa jam’iyyun adawa damar cin duddugen Najeriya ta kowanne bangare har na tsawon shekara guda, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.
Kaakakin shugaban kasa, Femi Adesina ne ya bayyana haka cikin wata hira da yayi a karshen mako, inda yace Buhari zai bayyana ra’ayinsa game da takarar 2019 a lokacin da yan adawa ba zasu iya yin masa wata barna na, ko kuma idan ma sun yi ba za tayi tasiri ba.
“Kun san irin kasarmu Najeriya, musamman idan shugaban kasa ya bayyana ra’ayinsa da wuri, za’a samu wadanda zasu soma yi masa bita da kulli, da kuma cin duddugi. Hakazalika kunji wasu ma sun fara yi masa kiranye kada ya tsaya, saboda sun san ko a lahira ba zasu iya kada shi zabe ba.
“Don haka idan a yanzu ya bayyana cewa zai tsaya takara, musamman yadda saura shekara guda da zabe, hakan na nufin ya basu damar cin duddugen gwamnatin Buhari kenan na tsawon shekara guda ta fannin siyasa, al’amura da ma tattalin arziki, kai babu abinda ba zasu yi ba don ganin sun hana shi takara.
“Don haka idan ka san dukkanin hakan, kaga kenan babu amfanin bayyana ra’ayi game da haka tun da wuri, sai ka bari sai lokaci yayi, lokacin da ko da zaka tsaya takara, ba zasu iya tafka maka wani barn aba.
” Inji shi.A watan da ya gabata ne dai shugaban kasa Muhammau Buhari ya sanar da gwamnonin jam’iyyar APC da su kara masa lokaci don yayi nazarin bukatar da suka mika masa na ganin ya sake tsayawa takarar shugaban kasa karo na biyu 2019.
Source :naij hausa
Title :
Dalilin Dayasa Bazan Bayyana Matsayina A 2019 Ba - Buhari
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa ba zai bayyana matsayinsa game da 2019 ba a wannan lokaci, inda yace yin hakan yay...
Rating :
5