Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar zata gudanar da jarrabawar gwaji a kan malaman makarantun sakandire.
Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na Tuwita a jiya, Lahadi.A cewar sa, gwamnatin jihar ta dukufa wajen dawo da martabar ilimi da kuma koyarwa.Kazalika ya bayyana shirin jihar na biyan malaman makarantun sakandire fiye da ragowar ma'aikatan jihar sannan kuma kafin kowanne ma'aikaci.
"Muna iyakar kokarinmu domin dawo da martabar ilimi da kuma koyarwa. Mun kammala jarrabawar gwajin malaman makarantun firamare saura kuma Jarrabawar gwajin malaman makarantun sakandire ya rage yanzu," a cewar El-Rufa'i.
Jarrabawar gwajin malaman makarantun firamare a jihar Kaduna ta jawo cece-kuce da ma zanga-zanga bayan gwamnatin jihar ta bayyana sallamar malamai fiye da 20,000 da su ka gaza cin jarrabawar.
Abin jira a gani shine yadda jarrabawar gwajin malaman makarantun sakandire zata kare.
Source :naij hausa
Title :
Za'a Fara Gwajin Malaman Sakandiri Nan Tafe - El Rufai
Description : Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar zata gudanar da jarrabawar gwaji a kan malaman mak...
Rating :
5