Kwanan nan ne Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai yayi wata magana kan harkar ilmi wanda ba a sallama ma masa ba don kuwa kusan ta tabbata ba gaskiya bane. Kwanaki ma dai Gwamnan ya taba yin irin wannan inda aka gano karya ne.
Gwamnan a wani jawabi da ya fito daga bakin sa yace kaf Kasar Amurka ko da su ke kusan sun fi kowa bin tsarin guruguzu babu makarantar Firamare ta ‘Yan kasuwa. A cewar Gwamnan makarantun Firamare a Amurka duk na Gwamnati ne.
Gwamnan yayi wannan jawabi ne lokacin da ake wani taro na Kungiyar ZEDA a Garin Zaria game da yunkurin da su ke yi na gyara harkar ilmi. Sai dai jim kadan bayan yayi wannan jawabi wata ‘Yar jarida a Amurka Jamila Fagge tayi masa raddi.
Fagge wanda ta ke aiki a Gidan Rediyon VOA na Amurka ta bayyana cewa a Maryland kurum akwai makarantun Firamare 847 wanda duk na ‘yan kasuwa ne kuma nan ta ke kai yaron ta. Jihar Maryland dai tana cikin mafi kankanta a kaf Amurka.
Source :naij hausa
Title :
Anakama El Rufai Na Fesa Karya A Gaban Jama'a
Description : Kwanan nan ne Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai yayi wata magana kan harkar ilmi wanda ba a sallama ma masa ba don kuwa kusan ta tab...
Rating :
5