Hukumar sojin 23 Brigade na Operation LAFIYA DOLE sun cika hannu da babban dan Kungiyar Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, Bubayi Isa, dan garin Panama, karamar hukumar Biu na jihar Borno a jiya Talata 20 ga watan Maris, 2018.
An damke shi ne tare wasu yaransa yan Boko Haram a kauyen Kalaa, karamar hukumar Hong a jihar Adamawa. Sauran sun bayyana cewa su mambobin kungiyar ne kuma suna da hannu cikin ayyukan kungiyar.
Binicke ya nua cewa Bubayi Isa na ne lamba 37 a cikin jerin yan Boko Haram din da ake nema wanda hedkwatan hukumar soji ta wallafa. Wadanda aka kama tare da shi sune Muhammad Buba, Abdullahi Abubakar da Yakubu Abdullahi.
Source :naij hausa
Title :
Sojoji Sun Damke Wani Babban Dan Boko Haram
Description : Hukumar sojin 23 Brigade na Operation LAFIYA DOLE sun cika hannu da babban dan Kungiyar Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, Bubayi Isa, dan...
Rating :
5