Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa wasu sun ja kunnen tsohon Shugaban kasa Obasanjo na kokarin sa na siyasantar da rikicin da ke faruwa a irin su Yankin Benuwe domin ganin Jam’iyyar APC ba ta kai labari a 2019 ba.
Kungiyar VDDN sun soki tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo naziyararda ya kai Jihar Benuwe inda su kace ba jaje ya kai sa ba. Kungiyar tace Obasanjo na kokari ne na ganin ya batawa Gwamnatin Buhari suna ganin zabe ya zo.
Shugabar Kungiyar Sharon Faliya Cham ta bayyana wannan inda ta zanta da manema a labarai a Garin Abuja. Kungiyar tace idan Obasanjo da gaske yake yi, ya fara lekawa Garin Zaki-Biam inda aka kashe jama’a a lokacin yana mulki.
Faliya Cham ta kuma ce ya kamata ne Shugaban kasar ya fara zuwa yi wa mutanen Taraba da aka murkushe sama da mutum 1000 tun kwanaki jaje, idan dai ba wata manufa gare sa ba, ko kuma ya leka Kaduna ko irin su Filato da aka yi kashe-kashe.
Source :naij hausa
Title :
Makarkashiyar Da Obasanjo Ke Kulla Wa Buhari Ta Bayyana
Description : Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa wasu sun ja kunnen tsohon Shugaban kasa Obasanjo na kokarin sa na siyasantar da rikicin da ke ...
Rating :
5