Rahotanni sun kawo cewa hukumar leken asirin kasar Jamus ta bayyana wani sabon al’amari akan nukiliyar kasar Koriya ta Arewa wanda ya kuma razana kasashen Turai.
Bisa rahotanni daga daya daga cikin jaridun na Jamus wato Bild, a lokacin wata ganawar sirri da ya gudanar tare da yan majalisar dokoki na kasarsa, shugaban BND Ole Diehl, ya bada tabbacin cewa makaman Koriya ta Arewa na iya cimma kasashen Turai a cikin kiftar ido.'Yan majalisar dokokin Jamus, wadanda labarin ya razana su ne suka fallasa wannan sirrin har 'yan jarida n Bild suka ji.
An tabbatar da cewa makaman Koriya ta Arewa na iya zuwa daga wata nahiya ya zuwa wani bangaren duniya cikin kankanen lokaci.
A baya jaridar naij ta rahoto cewa tsohon shugaban kasar Faransawa Nicolas Sarkozy na tsare sakamako bincike da ake kan cewa ya karbi miliyoyin kudaden euro ba bisa doka ba daga marigayi Moammar Gadhafi.
Source :naij hausa
Title :
Kim Jong Un Yasake Razana Turai
Description : Rahotanni sun kawo cewa hukumar leken asirin kasar Jamus ta bayyana wani sabon al’amari akan nukiliyar kasar Koriya ta Arewa wanda ya kuma r...
Rating :
5