Motar ta kamfanin Uber tana cikin yanayin saiti na tuki da kanta, tare da Direba a ciki, lokacin data buge wata mata tana tafiya a gefen hanya, a garin Tempe da yammacin ranar Lahadi, cewar kamfanin dake a garin na San Francisco na kasar Amurka.
Matar ta kwanta a asibiti, kafin daga baya ta mutu sakamakon raunukan da ta samu. Kamfanin na Uber ya dakatarda yin amfani da mota mai tuka kanta, don gwaji ko tuka abokan kasuwanci a garuruwan Tempe, Pittsburgh, Toronto, da San Francisco kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Tempe, na daya daga cikin garuruwa na hanyar Pittsburgh, inda kamfanin motar ke amfani da motar mai tuka kanta don safarar mutane zuwa wuraren harkokinsu na yau da kullun.
Mai kula da motar wanda ke zaune a kujerar direba, shi kadai ne a cikin motar lokacin da wannan al’amari ya auku, inji kamfanin na Uber.
Motar tana hannun ‘yan sanda a ranar Litinin. Hatsarin na ranar Lahadi, shine karo na farko da motar mai tuka kanta ta samu da masu tafiya a gefen hanya.
Hatsari na farko da mota mai tuka kanta tayi a shine a tsakiyar shekarar 2016, kuma ya shafi mota mai kirar Tesla.
Source :naij hausa
Title :
Mota Mai Tuka Kanta Ya Hallaka Wata Mata A Tempe
Description : Motar ta kamfanin Uber tana cikin yanayin saiti na tuki da kanta, tare da Direba a ciki, lokacin data buge wata mata tana tafiya a gefen han...
Rating :
5