- Manyan kafofin yada labarai na kasar Amurka sun rawaito cewar shugaba Donald Trump ya nemi tallafin kudi zunzurutu har dala biliyan hudu daga wurin gwamnatin kasar Saudiyya, domin ya gina kasashen yankin kasar Siriya wanda gwamnatin Bashar Al Asad tare da mataimakan sa Iran da Rasha suka lalata.
Manyan kafofin yada labarai na kasar Amurka sun ruwaito cewar shugaban kasar Amurka Donald Trump ya nemi kasar Saudiyya data tallafa masa da kudi zunzurutu har dala biliyan hudu, domin ya sake gina kasar Siriya, bayan ta kubutar da ita daga hannun gwamnatin Bashar Al Asad da mataimakan sa kasar Rasha da Iran.A bayanin daya daga cikin kafofin yada labaran Amurkan, "Washington Post", ta rawaito cewar a watan Disamba na shekarar data gabata, shugaba Donald Trump sunyi magana da sarkin Saudiyya, inda Trump ya bukaci kasar Saudiyyan data tallafa masa da kudin domin gabatar da kudurin na sa na gina kasar Siriya.
Har ya zuwa yanzu dai ofishin jakadancin kasar Saudiyyan dake Amurka bai ce komai ba akan batun, sai dai kuma fadar shugaban kasa ta White House ta tabbatar da cewa shugaba Donald Trump ya nemi taimakon kudi daga wurin kasashen gabas ta tsakiya domin ya sake gina kasashen yankin Siriya, wanda ake kokarin kwatowa daga hannun kungiyar DAESH.
Jaridar Washington Post ta kara da cewar, a shekarar data gabata ma kasar ta Amurka ta kashe kimanin dala miliyan 200 a yunkurin da take na ganin ta kubutar da yankin Siriya daga hannun Bashar Al Asad da mukaraban sa.Wani daga cikin manyan gwamnatin kasar Amurka ya gana da kafar yada labarai ta "Washington Post" ya ce, akwai yiwu war ayi amfani da wani kaso na wannan kudin da za a karba domin gina gidan kurkuku wanda za a dinga kulle 'yan ta'addar DAESH da aka kama.
A wani bangaren kuma Yariman Kasar Saudiyyan mai jiran gado, Muhammed bin Salman zai kai ziyara birnin Washington a yau domin ganawa da shugaba Donald Trump na kasar Amurka.
Source :naij hausa
Title :
Trump Yanemi Tallafin Kudi A Gun Kasar Saudiyya
Description : - Manyan kafofin yada labarai na kasar Amurka sun rawaito cewar shugaba Donald Trump ya nemi tallafin kudi zunzurutu har dala biliyan hudu d...
Rating :
5