Hukumar EFCC ta yi ram da Aliyu Usman wani na-kusa da tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro a Najeriya Sambo Dasuki. Yanzu dai an bada belin sa kan kudi Miliyan 150. Yanzu an dage shari’ar har sai cikin Watan Mayun wannan shekarar.
EFCC ta kama Aliyu Usman ne kuma ta maka shi a gaban Alkali mai shari’a John Tsohon na babban Kotun Tarayya da ke Maitama a Birnin Tarayya a makon nan inda ake zargin sa da yin gaba da wasu kudi da su ka haura Naira Miliyan 600.
A baya dai an shiga Kotu da Usman tare da wani Nuru Yahaya da wasu kamfani biyu da ake zargi da awon-gaba da makudan miliyoyi na kudi. Wadannan Bayin Allah sun karbi kwangila ne daga hannun Sambo Dasuki lokacin yana ofishin NSA.
An dai dage karar yanzu inda ake zargin cewa an yi amfani da kamfanin Leaderettehe Nigeria Limited da Nordeen Global Resources wajen sace wasu kudi da su ka kusa Naira Miliyan 900 a lokacin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Source :naij hausa
Title :
An Sake Damke Wani Na Hanun Daman Sambo Dasuki
Description : Hukumar EFCC ta yi ram da Aliyu Usman wani na-kusa da tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro a Najeriya Sambo Dasuki. Yanzu dai an bada ...
Rating :
5