Jami'an hukumar yaki da masu ta'amulli da miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Katsina sun damke mutane shida wanda ake zargi suna da hannu cikin safarar kwallaben kodin 24,000 da aka kama cikin wata Trela.
Sai dai hukumar ta NDLEA ta ambacci sunayen mutane biyu ne kawai, Christain Chukwuma wanda aka bayyana cewa dillali ne da kuma Obiora Chukwuma, Manajan Sunglow Equity Nigeria Ltd.
A sanarwan da ya bayar, kwamandan hukumar, Maryam Sani ta ce jami'an tsaro na hadin gwiwa ne suka kama kwallaben kodin din a wata gidan ajiye kaya a Dutsenreme kusa da Funtua bayan an kawo kayan daga Onistsha.
Sai dai, Christian Chukwuma ya ce bashi ne mai kayan ba 'Kayan ba nawa bane, nima an aiko ni ne in taimaka wajen karbo sakon''Ainihin mai kayan sunan sa Sunday Chibota kuma mazaunin jihar Kebbi ne, muna zama a Funtua ne, an aiko kayan ne daga Ogini kuma ya kira ni mu taimaka masa kuma ban san cewa kodin ne ke cikin motan ba, inji shi.
Source :naij hausa
Title :
Ankama Wata Tirela Shake Da Kwalaben Kodin A Katsina
Description : Jami'an hukumar yaki da masu ta'amulli da miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Katsina sun damke mutane shida wanda ake zargi suna d...
Rating :
5