Hukumar EFCC mai yaki da masu yi tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta garkame asusun banki akalla 30 da kuma wasu gidaje kimanin hakan daga hannun tsohuwar Shugabar Hukumar NSITF.
An samu wadannan makudan dukiya ne wajen Ngozi Olojeme wanda tayi wa Jonathan hidima a matsayin Mataimakiyar Darektar kudi wajen yakin neman zaben 2015. Yanzu haka dai an damke Darektan na NSITF da wasu Ma’aikata.
Ana zargin Ngozi Olojeme wanda ta rike Ma’aikatar ta NSITF daga 2009 zuwa 2015 da karkatar da kusan Dala Miliyan 50 wanda ya kai Naira Biliyan 68. Wannan mata tana da akawun sama da 20 a Bankin First Bank da kuma GTB ban da tarin dukiya.
Yanzu dai ana ta bincike inda wannan Baiwar Allah ta musa cewa akwai hannun ta wajen satar wadannan kudi. An dai karbe gidaje da dama a Abuja da manyan Garuruwa irin su Bayelsa da Delta da kuma manyan filaye daga hannun ta.
Source :naij hausa
Title :
EFCC Ta Bankado Wani Gagarumin Satan Da Akayi A Mulkin Jonathan
Description : Hukumar EFCC mai yaki da masu yi tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta garkame asusun banki akalla 30 da kuma wasu gidaje kimanin hakan daga h...
Rating :
5