Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da cin hanci da rashawa ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a turance a jiya Litinin ta gayyaci tsohon shugaban jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Alhaji Ali Modu Sheriff.
Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa a jiyan an ga Alhaji Ali Modu yana shiga a ofishin hukumar ta EFCC inda kuma bai fito ba sai da aka dauki awonni.
Jaridar naij haka zalika ta samu daga mai magana da yawun hukumar ta EFCC Mista Wilson Uwajaren wanda ya tabbatar da hakan inda ya kuma bayyana cewa sun gayyace shi domin ya ansa wasu tambayoyi.
Source :naij hausa
Title :
Hukumar EFCC Ta Titsiye Ali Modu Sherrif
Description : Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da cin hanci da rashawa ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a turance a jiya Litin...
Rating :
5