Dan majalisar dattijan Najeriya daga jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin harkokin noma Sanata Abdullahi Adamu a jiya ya bayyana cewa shi fa ba bu wani kalar razanarwa daga abokan aikin sa da za ta sa ya dena goyon bayan shugaba Buhari.
Haka kuma Sanatan wanda ke zaman tsohon gwamnan jihar ta Nasarawa ya kuma bayyana cewa hakika abun takaici ne yadda yawacin 'yan majalisar jam'iyyar APC mai mulki suke munafuntar gwamnatin shugaba Buhari duk kuwa da zaman su a jam'iyya daya.
Jaridar naij dai ta samu cewa Sanatan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya inda kuma ya karyata zarge-zargen da ake yi masa na cewa wai yana so ya kawo hargitsi a zauren tare kuma da tsige shugaban majalisar.
A wani labarin kuma, Wani matashi wanda yake da ra'ayin fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2019 mai suna Adamu Garba II ya fito ya bayyana cewa yanzu dai kam ta tabbata cewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ba ke mulkar Najeriya.
Source :naij hausa
Title :
Akwai Yan Majalisar APC Dake Munafuntar Buhari - Sanata Adamu
Description : Dan majalisar dattijan Najeriya daga jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin harkokin noma Sanata Abdullahi Adamu a jiya ya bayyana cewa shi f...
Rating :
5