Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zaman ta a unguwar Jabi, a jiya ta nuna rashin jin dadin ta zuwa ga lauyan dake kare mahaifiyar matar nan da ake zargi da kashe mijin ta Bilyaminu watau Maryam Sanda mai suna Maimuna Aliyu bisa raina mata wayau.
Mun samu dai cewa ita dai Maryam Aliyu hukumar nan dake yaki da masu laifukan cin hanci da rashawa ne mai zaman kanta wata ICPC ta shigar da ita kara bisa laifuka 3 ciki hadda zamba cikin aminci da damfara da kuma sayar da kadarorin da ba na ta ba.
Jaridar naij ta samu cewa sai dai alkalin kotun ya nuna matukar bacin ran sa bayan da lauyan da ke kare ta mai suna Osuobeni Akponimisingha ya shaida masa cewa bai samu damar kawo dukkan shaidun sa 11 ba kamar yadda yayi alkawin inda kuma alkalin ya umuci a ci shi tara.
Source :naij hausa
Title :
Mahaifiyar Maryam Sanda Tasake Shiga Cikin Wata Masifa
Description : Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zaman ta a unguwar Jabi, a jiya ta nuna rashin jin dadin ta zuwa ga lauyan dake kare mahaifiyar ma...
Rating :
5