Sabon kwamishinan zaben hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa na jihar Ondo Dakta Rufus Akeju ya bayyana cewa hukumar ta zabe watau Independent National Electoral Commission (INEC) tana nan ta na shirin kona dukkan katin zaben da ba'a karba ba kafin zaben 2019 mai zuwa.
Mista Akeju yayi wannan kwarmaton ne a yayin da yake fira da manema labarai a garin Akure, jiya Litinin inda ya bayyana cewa tuni da hukumar ta dukufa wajen ganin ta wayar wa da mutane kai don su je su anshi katin zaben su.
Jaridar Naij ta samu cewa kwamishin zaben ya kuma bayyana cewa duk da wannan kokarin na hukumar har yanzu a kwai wadanda ba su je suka anshi na su ba don haka ne ma ya ce hukumar ka iya kone su domin magance yiwuwar anfani da su wajen magudin zabe.
Source :naij hausa
Title :
Zamu Kona Duk Katin Da Ba'a Karba Ba Kafin 2019 - INEC
Description : Sabon kwamishinan zaben hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa na jihar Ondo Dakta Rufus Akeju ya bayyana cewa hukumar ta zabe watau Independe...
Rating :
5