Jaridar Rariya ta yi kicibus da wani hazikin dalibi dan asalin jihar Jigawa mai suna Aliyu Muhammad Sani Kaugama, wanda yafi kowa samun sakamako mai kyau a jarabawar JAMB da ya gudana.
Majiyar NAIJ ta ruwaito Aliyu, dalibi a makarantar yara masu hazaka dake garin Bamaina ne ya samu maki 311 cikin maki 400 daya kunshi darussa guda hudu ya zamo dalibin da yafi maki a jihar Jigawa gaba daya.
Sai dai majiyar ta yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta jajirce wajen daukan nauyin wannan dalibi don cigaba da karatunsa a duk kasar data kamata, don al’ummar jihar Jigawa su amfane shi.
A ranar Talata 13 ga watan Maris ne dai hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari na Najeriya, JAMB ta sanar da fitar da sakamakon jarabawar dake gudana a yanzu, inda ta fara sakin sakamakon daliban da suka zauna jarabawar.
Source :naij hausa
Title :
Dalibin Dayafi Kowa Cin Maki A Jarabawar Jamb
Description : Jaridar Rariya ta yi kicibus da wani hazikin dalibi dan asalin jihar Jigawa mai suna Aliyu Muhammad Sani Kaugama, wanda yafi kowa samun saka...
Rating :
5