Ba mamaki dai Gwamnan Jihar Kaduna watau Malam Nasir El-Rufai ya dauko aikin da ya fi karfin sa inda yanzu haka an daina ba yaran makaranta abinci kamar yadda aka fara da farko kafa Gwamnati.
A farkon 2016 Gwamnatin El-Rufai ta rika ba ‘Daliban da ke aji 4-6 wanda sun haura miliyan 1.5 abinci a wajen karatu. Wannan dai ya sa an samu karuwar ‘dalibai a makaranta sai kuma daga baya Gwamnatin ta janye hannu.
A wancan lokaci dai tsohon Kwamishinan ilmi na Jihar Marigayi Farfesa Andrew Nok yabayyana cewa sun kashe Naira Biliyan 8 cikin watanni 8 da aka yi ana ciyar da ‘yan makarantan Firamare da ke aji 4 zuwa 6 a Jihar.Gwamna El-Rufai yayi alkawarin cigaba da bada abinci a makarantar a 2017 amma har yau ba a cigaba ba.
Daily Trust ta rahoto cewa an yi yarjejeniya ne da Gwamnatin Tarayya na cewa za ta ciyar da yaran da ke aji 1 zuwa 3.Gwamnatin Jihar Kaduna tace ta na jiran Gwamnatin Tarayya ne ta biya ta ragowar kudin da ake bukata.
Wani Kwamishinan Jihar yace an bada kashi 50% wanda ya haura Naira biliyan 3 don haka yanzu ana jiran kashi 50% ne.
Source :naij hausa
Title :
El Rufai Ya Dauko Aikin Da Bazai Iya Ba
Description : Ba mamaki dai Gwamnan Jihar Kaduna watau Malam Nasir El-Rufai ya dauko aikin da ya fi karfin sa inda yanzu haka an daina ba yaran makaranta ...
Rating :
5