Shahararren dan wasan Real Madrid dinnan, Christiano Ronaldo, yana cigaba da iya bakin kokarin sa da bada tallafi domin sharewa al'ummar kasar Siriya hawayen su, kasar data share shekaru da yawa suna cikin tashin hankali.
Dan wasan, dan asalin kasar Portugal, Christiano Ronaldo ya jima yana tallafa wata kungiya mai kare hakkokin yara mai suna "Save the Children", yayi Allah wadai da irin yadda ake azabtar da yaran kasar Siriya, inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya ce: "Mutum ya zama mai karfin hali, sannan ya zama mai imani, kar mutum ya sake ya yanke kauna da samun rahamar ubangiji", inda daga bisa ni ya saka hotunan hare-haren da ake kaiwa al'ummar gabashin Guta na kasar Sham a watan Fabrairun wannan shekarar.
Dama dai shi Christiano Ronaldo din, ya jima yana bada tallafi ga al'ummar da suke cikin irin wannan rikici musamman ma yara kanana, inda yake basu tallafin kayayyakin masarufi, tufafi da magunguna.
Source :naij hausa
Title :
Allah Wadan Irin Azabar Da Ake Wa Mutanen Siriya - Cristiano Ronaldo
Description : Shahararren dan wasan Real Madrid dinnan, Christiano Ronaldo, yana cigaba da iya bakin kokarin sa da bada tallafi domin sharewa al'ummar...
Rating :
5