Babbar kotun jihar Minnesota ta kasar Amurka ta fara zaman shari'ar wasu mutane hudu da ake zargin su da kai harin bam a masallacin Juma'a a watan Agustan shekarar 2017 data gabata.
Sanarwar shari'ar ta fito daga Ofishin gabatar da kara na jihar ta Minnesota ya ce, an gurfanar da mutane hudun saboda kamasu da aka yi da manyan bindigogi masu sarrafa kansu.Ofishin ya bayyana cewa, a ranar 5 ga watan Agustan shekarar 2017 ne kafin a shiga Sallar Asuba mutanen suka kai harin bam din a masallacin juma'a na Darul Farook da ke a jihar ta Minnesota inda hakan ya janyo matsala a ofishin limamin masallacin.
Bayan haka kuma mutanen sun kara kai wani hari a watan Nuwamban shekarar 2017 a wani babban asibitin zubar da ciki da ke jihar.
Bayan sun kai harin na biyun ne hukumar jihar ta fara gudanar da bincike tare da kama mutanen da ake zargi din.
Source :naij hausa
Title :
An Gurfanar Da Mutanen Da Dasuka Kai Hari Masallacin Juma'a A Kotu
Description : Babbar kotun jihar Minnesota ta kasar Amurka ta fara zaman shari'ar wasu mutane hudu da ake zargin su da kai harin bam a masallacin Juma...
Rating :
5