Wata daliba da ta zana jarabawan JAMB mai suna Loveth ta hallaka kanta a garin Ekiugbo, karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta.
An tsinci gawar Loveth, wacce ta samu maki 163 a jarabawan ne ranan Laraba da safiya.Dalibar wacce ke son karantan ilimin Likita a jami’a ta kwankwadi gwalban guba uku.
Game da cewar majiya, Loveth ta koma gida bayan ta duba sakamakon jarabawanta ranan Talata inda ta ga cewa bata samu makin da zai taimaka mata wajen samun shiga jami’a ba. Kawai sai ta bar wurin cikin hawaye.
A bangare guda, jami’an yan sanda sun damke mahaukacin da ya kasha daliban makaranta 2 a jihar Ogun.Wannan mumunan abu ya faru ne ranan Litinin inda ya hallaka daliban masu suna Obituyi Alabi da Kalesanwo Ibrahim.
Source :naij hausa
Title :
Wata Daliba Ta Kashe Kanta Saboda Bata Ci Jarabawar Jamb Ba
Description : Wata daliba da ta zana jarabawan JAMB mai suna Loveth ta hallaka kanta a garin Ekiugbo, karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta. An ...
Rating :
5