Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba yace gwamnatinsa zata zuba kudade a bangaren Soji don a rusa Ta’addacin Boko Haram a kasa.
Shugaban Kasar wanda ya kai ziyarar jaje ga iyayen ‘yan matan makarantar Dapchi, a makarantar ta Kimiyya da Fasaha, yace ‘yan ta’addan zasu fuskanci mummunan sakamako na ‘yan matan makarantar Chibok da aka sace a shekarar 2014, dana Dapchi.
Yace, ya karanta rahoton da aka kawo masa na abunda Gwamnatin Tarayya keyi don ceto yaran cikin koshin lafiya, kuma an tura ‘yan Sanda da Sojoji da sauran matakan tsaro don cigaba da bincike. Yace, bazamu daga ma Boko Haram ba. Zamuyi amfani da karfin Soji mu rusa su kuma mu samar da zaman lafiya na har abada a kasa.
Mukarraban Shugaban Kasar sun hada da Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed; Ministan Ilimi, Adamu Adamu; Ministan cikin gida, Abdurrahman Dambazau; Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung da kuma Gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima.
Source :naij hausa
Title :
Da Karfin Soja Zamu Tarwatsa Boko Haram - Buhari
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba yace gwamnatinsa zata zuba kudade a bangaren Soji don a rusa Ta’addacin Boko Haram a kasa. Sh...
Rating :
5