A ranar Alhamis din da ta gabata ne kasar Koriya ta Arewa ta yiwa Najeriya sabon albishir, na gudummawar taimakon dakarun sojin kasar wajen fafutikar su ta ganin karshen ta'addancin Boko Haram da ya yi kamari a yankin Arewa maso Gabashin kasar.
Babban jakadan kasar mai murabus, Mista Jong Yong Chol, shine ya bayyana hakan a yayin ziyarar bankwana da ya kaiwa Ministan harkokin kasashen na Najeriya, Mista Geoffrey Onyeama, inda ya kuma jinjinawa gwamnatin kasar kan kokarin ta na yakar ta'addanci.
Da yake cewa, a matsayin sa na wakilin kasar Koriya ta Arewa, yana mika sakon taya murna dangane da irin nasarorin da Najeriya ta samu wajen yaki da ta'addanci na Boko Haram.
Ya kuma bayyana albishir din sa ga gwamnatin Najeriya da cewar kasar sa za ta bayar da gudummuwar taimakon dakarun sojin kasar nan wajen kawo karshen ta'addanci.
Jakadan ya kuma mika godiyar sa ga gwamnatin Najeriya dangane da dankon zumunta da kuma kulalliyar abota dake tsakanin kasashen biyu tun a shekarar 1976 wajen habakar tattalin arziki, siyasa da kuma al'adu.
Source :naij hausa
Title :
Albishirin Koriya Ta Arewa Wa Nijeriya Akan Boko Haram
Description : A ranar Alhamis din da ta gabata ne kasar Koriya ta Arewa ta yiwa Najeriya sabon albishir, na gudummawar taimakon dakarun sojin kasar wajen ...
Rating :
5