Wani alkalin babbar kotun tarayya dake zaman ta a garin Legas a unguwar Igbosere mai suna mai shari'a Oluwatoyin Ipaye a yau din nan ya yanke wa wani dillalin gidaje mai suna Babatunde Habeeb hukuncin daurin shekaru 1,230 a gidan yari.
Alkalin da ya ke yanke hukunci akan mai laifin ya gano cewa Mista Babatunde Habeeb ya damfari wasu mutane ne su 101 kudaden da suka kai darajar Naira miliyan 28 da sunan zai samar masu gidan zama.
A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a bangaren tattara bayanan sirri na shiyyar jihar Ribas sun sanar da samun nasarar kashe kasurgumin hatsabibin tsageren Neja Delta bayan ba-ta-kashi na tsawon lokaci da suka yi dashi.
Tsageran mai suna Prosper David 'yan sandan sun ce sai da suka ji ma sa ciwo a lokacin da yake kokarin tserewa kafin daga bisani ya mutu sakamakon ciwon da aka ji masa.
Source :naij hausa
Title :
Anyanke Ma Wani Dillalin Gidaje Daurin Shekaru 1, 230 A Gidan Yari
Description : Wani alkalin babbar kotun tarayya dake zaman ta a garin Legas a unguwar Igbosere mai suna mai shari'a Oluwatoyin Ipaye a yau din nan ya ...
Rating :
5