Shugaban jam'iyyar da ke mulki a Najeriya watau All Progressives Congress (APC) watau Cif John Odigie-Oyegun ya yi ikirarin cewa yanzu kam a Najeriya ba sauran cin hanci da rashawa domin kuwa shugaba Muhammadu Buhari ya murkushe dukkan bilbishin ta.
Cif Oyegun ya bayyana hakan ne jiya a ofishin sa dake garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya yayin da ya anshi bakuncin shugabannin kwalijin kimiyya da fasaha ta garin Bida karkashin jagorancin shugaban ta Dakta Abubakar Dzukogi.
Jaridar Naij ta samu cewa shugabannin kwalejin sun ziyarcewa shi ne domin kai masa goron gayyata zuwa bikin yaye daliban su karo na 15 da kuma bayar da kyaututtuka da zai gudana a ranar Laraba mai zuwa.
Source :naij hausa
Title :
Buhari Ya Dakile Cin Hanci Da Rashawa A Kasarnan - Oyegun
Description : Shugaban jam'iyyar da ke mulki a Najeriya watau All Progressives Congress (APC) watau Cif John Odigie-Oyegun ya yi ikirarin cewa yanzu k...
Rating :
5