Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci ma’aikatu da hukumomin gwamnati dasu gabatar da bayanin kasafin kudinsu na shekarar 2018, ga majalisar dokoki.
Shugaban kasar a bayaninsa ya bawa kungiyoyin wa’adin kwanaki biyu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.Yace, dole ne a gabatar da kasafin ga majalisar dokokin kafin ranar 23, ga watan Maris. Umurnin shugaban kasar ya fito ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.
Shugaban kasar yayi barazanar cewa zai kori Daraktoci da shuwagabannin hukumomi saboda rashin mayar hankali a kan gabatar da kasafin kudi na 2018.
Bacin Ran shugaban kasar ya biyo bayan da Majalisar Dokoki ta bayyana masa cewa a cikin kungiyoyin hukumomi da ma'aikatun gwamnati 60 da muke dasu, 10 ne kadai suka kare kasafin kudinsu.
Source :naij hausa
Title :
Wa'adin Kwana Biyu Ya Rage Wa Ma'aikata Don Gabatar Da Kasafin Kudaden Su Ga Majalisa - Buhari
Description : Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci ma’aikatu da hukumomin gwamnati dasu gabatar da bayanin kasafin kudinsu na shekarar 2018, ga majalisar do...
Rating :
5