Malam Bala Usman, shugban kwamitin shirin ciyar da daliban makarantar Frimare da gwamnatin tarayya ta kaddamar (HGSPF) ya gargadi malamai akan cinye wa dalibai abincin su.
Usman Bala, yayi wannan gargadi ne a wata hira da yayi manema labaru a ranar Talata.
Source :naij hausa
Jaridar naij ta samu rahoton cewa, masu dafawa dalibai abincin sun yi korafin cewa, mallaman makaranta suna raba abincin dalibai a tsakanin su.
Mallam Usman, ya ce za su dauki tsatsauran mataki akan duk mallamin da aka kama da laifin cin abincin dalibai.
Usman ya kara da cewa za su ja hankalin masu dafawa dalibai abincin akan bai wa dalibai kadai abinci, sannan idan suka yi wani abu sabanin haka, za a hukunta su.
Title :
An Gargadi Malamai Akan Cin Abincin Dalibai
Description : Malam Bala Usman, shugban kwamitin shirin ciyar da daliban makarantar Frimare da gwamnatin tarayya ta kaddamar (HGSPF) ya gargadi malamai ak...
Rating :
5