Wani jigo na jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya damki tare da gurfanar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo domin ya tabbatar da gaskiyar sa kan yaki da rashawa.Tsohon gwamnan ya kalubalanci shugaba Buhari a yayin wani taro da aka gudanar a babban birnin tarayya mai taken tsarin gudanar da shugabanci nagari.
Yake cewa, al'ummar Najeriya ba za su tabbatar da muhimmanci tare da tsananin yaki da cin hanci da rashawa da Buhari ya sanya a gaba face ya damko tsohon shugaban kasa Obasanjo bisa laifukan kudaden wutar lantarki da suka yi layar zana a lokacin gwamnatin sa.
Kalu ya ci gaba da cewa, muddin shugaba Buhari bai aikata hakan ba to kuwa ba bu wani yakar rashawa da ake yi a kasar nan, inda ya hikaito dalar Amurka miliyan 16 da ta yi tsuntsunwa a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasar.
NAIJ hausa ta kuma ruwaito cewa, a daren ranar Litinin din da ta gabata kimanin rayuka sama da 20 ne suka salwanta a wani sabon harin makiyaya da ya afku a jihar Filato.
Source :naij hausa
Title :
Yakamata Buhari Ya Damke Obasanjo - Kalu
Description : Wani jigo na jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya damki t...
Rating :
5