Mun samu labari cewa 'Yan Majalisar Dattawa sun yi wa wani Dan uwan su Sanata Ben Murray Bruce na Yankin Jihar Bayelsa taron dangi ne lokacin da ya nemi a rage albashin su kwanaki. Yanzu haka dai ya bayyana yadda yake rabar da kudin na sa.
Kun ji cewa albashin Shugaban kasar Amurka Donald Trump a shekara shi ne $400,000 wanda a Najeriya kuwa Sanatoci na tashi da $492, 000 a duk shekarar kuma ba su son ji wata maganar da za ta sa ace an rage wannan albashin na su.
Sanata Ben Murray Bruce ya bayyana cewa ya taba tashi a Majalisa yace idan har albashin Sanatocin Najeriya ya fi na Kasashe irin su Ingila, to ya kamata ace albashin Ma'aikatan kasar ma ya zarce na masu aiki a Kasar ta Birtaniya da Amurka.
Babban Dan Majalisar yace tun ranar sa na farko a Majalisa yayi wannan kira amma 'Yan uwan sa su ka taka masa burki. Tun daga lokacin Sanatan yake kashe miliyoyin albashin na sa tare da zaurawa da sauran mata marasa karfi a Yankin sa.
Source :naij hausa
Title :
Shin Kunsan Dan Majalisan Dake Kashe Albashinsa Akan Zaurawa?
Description : Mun samu labari cewa 'Yan Majalisar Dattawa sun yi wa wani Dan uwan su Sanata Ben Murray Bruce na Yankin Jihar Bayelsa taron dangi ne lo...
Rating :
5