Alkali Ahmed Mohammed na babban Kotun Tarayya da ke birnin Tarayya Abuja yace Majalisa ta cire kan ta daga maganar sauya tsarin zabe. Yanzu haka dai ‘Yan Majalisar sun kawo kudirin da zai canza yanayin zabe a kasar.
A jiya Laraba Kotu ta yanke hukuncin cewa Majalisa ta dakata da yunkurin da ta ke yi na yi wa tsarin zaben Najeriya garambawul. Alkali mai shari’a Ahmed Mohammed yace a bar wannan maganar har sai Kotu ta zauna a makon gobe.
Jam’iyyar Accord ce ta shigar da kara gaban Kotu inda ta ke nema ayi mata bayani game da batun. Majalisa dai ta nemi ta canza yadda ake gabatar da zabe a kasar amma Shugaban kasar yace wannan aikin Hukumar zabe ne ba su ba.
Idan har Shugaban kasa bai amince da wani kudiri na Majalisa ba, ana iya amfani da wani sashen dokar kasa da ya bar ‘Yan Majalisar damar aiki da karfin su wajen tabbatar da aniyar su. Kotu dai za ta karasa raba wannan gardama a Ranar Talata.
Source :naij hausa
Title :
Kotu Taja Kunnen Yan Majalisa Kan Canza Tsarin Zabe
Description : Alkali Ahmed Mohammed na babban Kotun Tarayya da ke birnin Tarayya Abuja yace Majalisa ta cire kan ta daga maganar sauya tsarin zabe. Yanzu ...
Rating :
5