Bisa dukkan alamu dai Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sallama wajen gyara matatun man fetur nan kusa. Watakila dai sai an kammala aikin kamfanin ‘Dangote sannan za a samu saukin mai a NajeriyaKaramin Ministan harkokin man fetur na Najeriya Ibe Kachikwu yace Gwamnatin Najeriya ba ta da kudin da za ta gyara matatun ta na mai.
Ministan ya bayyana wannan ne bayan taron Ministoci na mako-mako da aka yi jiya a fadar Shugaban kasa.
Dr. Emmanuel Ibe Kachikwu yace sun samu kan su ne a lokacin da ake fama da rashin kudi a kasar. Karamin Ministan yace su na kokarin neman kudin da za a gyara matatun kasar amma sai dai hakan zai dauki lokaci saboda ka’idar aiki da Kamfanin NNPC.
Duk da dai ana shirin kafa wasu kananan matatu da za su fara aiki a kasar, sai dai abin da za su tace a rana ba zai wuce ganga 2000 zuwa 10000 ba. A kowace rana ta Allah dai ana shan sama da lita 630, 000 a Najeriya inji karamin Ministan kasar na harkar man fetur.
Source :naij hausa
Title :
Bamuda Kudin Gyara Matatun Mai - Ministan Man Fetur
Description : Bisa dukkan alamu dai Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sallama wajen gyara matatun man fetur nan kusa. Watakila dai sai an kammal...
Rating :
5