Labari ya zo mana cewa mai girma Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya hana shiga da fita daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe. An sa dokar ne dai bayan da aka hallaka wasu Sojoji a Garin Bokkos da Bassa a cikin Jihar.
Gwamna Simon Lalong ya sa dokar hana yawo a wasu bangarori na Jihar ne bayan mutuwar wasu Sojoji 2 da kuma wani ‘Dan sanda. Bayan nan kuma dai an kashe wasu Bayin Allah duk a cikin karamar Hukumar Bassa kwanan nan.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Gwamnan yayi wa jama’an Jihar jawabi bayan aukuwar wannan abu a Mianga inda ya kafa dokar hana yawo a jiya da dare. Gwamnan ya bayyana irin kokarin da yake yi na kawo zaman lafiya a Jihar Filato.
Bayan aukuwar wannan barna dai Gwamnan ya kira taro na gaggawa inda yace wasu makiyan Jihar na kokarin kawo masu cikas. Gwamnan ya jajantawa jama’an da su kayi rashi inda yace zai dage matuka wajen hukunta masu laifin.
Source :naij hausa
Title :
Ansa Dokan Ba Shiga Ba Fita A Jihar Filato
Description : Labari ya zo mana cewa mai girma Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya hana shiga da fita daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe. An sa ...
Rating :
5