Gwamnatin Rwanda ta haramta wa dukkanin masallatan kasar yin amfani da lasifika domin kiran sallah.
Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne saboda yadda kiran sallan ke damun mutanen da ke makwabtaka da masallatan.
Kungiyar al'ummar musulmin Rwanda ta soki matakin, inda daya daga cikin shugabannin kungiyar ya ce wannan ba shi ne matakin da ya kamata gwamnati ta dauka ba.
A cewarsa, kamata ya yi gwamnati ta amince a dinga rage karar lasifika a lokacin kiran Sallan.
A kwanan baya ma gwamnatin Rwanda ta rufe coci sama da 700 saboda dalilai na tsaro da kiwon lafiya.
Sannan an kame malaman coci da dama.
Rwanda ta kafa wata sabuwar doka da za ta kula da lamurran gudanar da addini a kasar.
Source :bbc hausa
Title :
Mun Haramta Kiran Sallah Da Lasfika- Gwamnatin Rwanda
Description : Gwamnatin Rwanda ta haramta wa dukkanin masallatan kasar yin amfani da lasifika domin kiran sallah. Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne sab...
Rating :
5