Manajan Manchester United Jose Mourinho ya ce fitar da kulub din daga gasar Zakarun Turai "ba sabon abu ne."
Dan wasan Sevilla Wissam Ben Yedder ne ya ci kwallaye biyu a ragar Manchester United a Old Trafford inda aka tashi wasan ci 2-1.
Tun doke ta a wasan karshe a 2011, sau daya Manchester United ta tsallaka zuwa zagayen kwata fainal, lokacin da Bayern Munich ta doke ta a 2014.
Mourinho wanda karo na hudu ke nan yana shan kashi a zagayen kungiyoyi 16, ya ce " Ba zan ce ba mu taka rawar gani ba."
Sannan ya ce bai yi nadama ba. " Na yi iya kokari na, 'yan wasa ma sun iya nasu kokarin, mun yi kokari amma ba mu yi nasara ba, kuma dama kwallo ta gadi haka," a cewar Mourinho.
Sau daya ne dai Manchester United ta samu nasara a wasanni tara da ta buga a baya a irin wannan zagayen, kuma sau biyu ke nan ana fitar da kulub din a karawa uku.
Source :bbc hausa
Title :
Banyi Nadamar Fitar Man United A Champions League Ba - Mourinho
Description : Manajan Manchester United Jose Mourinho ya ce fitar da kulub din daga gasar Zakarun Turai "ba sabon abu ne." Dan wasan Sevilla Wi...
Rating :
5