Karamin Minitsan harkan kiwon lafiya, Dr Ehanire Osagie, ya ce gwamnatin tarayya zata inganta fannin kiwon lafiyar Najeriya saboda kawo karshen jinya da ‘yan kasar ke yi a asibitocin kasashen waje.
Dr Ehanire Osagie, ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da ayyukan da Cibiyar kiwon lafiya na gwamnatin tarayya a jihar Nasarawa (FMC) ta yi.Ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya mayar da hankali wajen inganta cibiyoyin kiwon lafiya a Najeriya.
A jawabin sa ya ce ‘yan Najeriyan dake zuwa kasashen Indiya, Masar, Amurka da sauran su jinya gannin za su mutu idan suka je asibitocin Najeriya.
“Shi yasa gwamnatin tarayya take kokarin inganta cibiyoyin kiwon lafiya a kasar saboda 'yan Najeriya su daina zuwa kasashen ketare jinya,” Inji shi.
Source :naij hausa
Title :
Zamu Kawo Karshen Jinya A Kasashen Waje- Ministan Lafiya
Description : Karamin Minitsan harkan kiwon lafiya, Dr Ehanire Osagie, ya ce gwamnatin tarayya zata inganta fannin kiwon lafiyar Najeriya saboda kawo kars...
Rating :
5