1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 3

Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 3

By Abdul Mk
Add Comment
Tuesday, 12 April 2016

ALLAH YA ISA BAN YAFE BA! // 3
.
"Don tsayanan" cikin tsawa "Kar ki jiqa min carpet a banza, yanzu sai ki sa dakin mutum ya kama wari, ban da rashin sanin ciwon kai duk da irin wannan katafaren hadari amma mutum ya yi zamansa a waje har ruwa ya same shi, duk da haka ya kasa fakewa ga irin wannan uban ruwa da ake shantabawa har da qanqara amma ki kamo hanya tsamo-tsamo don gobe ki kwanta min ki ce ba ki da lafiya, to wallahi na gaji da zuwa Kyamis wannan karon sai dai ubanki ya biya
kudin magani!"

.
Mari ta koma gefe guda tana rawar dari, ganin haka sai Tala ta yi wuf ta miqe, tana cewa "Amshi wannan zanin koma can gefe ki cire wadannan sai ki rataye su a wayan jikin baranda, albashi gobe a matse su" ta dawo kusa da Fatu tana cewa "Ke ai dan yau ba a masa haka, ko ni da nake da 'ya'ya maza ban taba yi musu fadan fakewa a wani wuri ba bare 'ya mace, daga irin fakewannan ce ake farke mutum, tun ma ba mace da take da hanyoyin da za a cutar da ita da dama ba"

.
Fati ta tabe baki, maganar Tala ba ta shige ta ba, ta dubi Mari da ta shigo yanzu "To wuce uwar daka ki ba mu wuri, in kuma ba zuba mana ido za ki yi ba" ta juyo kan Tala "Wannan ai ta wuce yarinya, ni fa irin tadodin tsofaffinnan ba ruwana da su, don ko tun muna 'yammata mu ba a matsa mana ba, bare kuma yanzu da wayewa ta dada bazuwa a ko ina, Mari ai ba yarinya ba ce, in ma ta yi sakaci ai jiki magayi budurci tsada ce da shi ta san haka, wace duk ta yi asararsa shi kenan har abada, ba wani abu ne da za a ce za a ga likita a kansa ba".
.
Tala dai ba ta ji dadin zancen Fatu ba, don haka ta share maganar gaba daya ta dauki littafin da ke kusa da ita tana dubawa "'Yan talla sunansa? Na ji ana ta cewa Hajiannan za ta fito da wani littafi mai matuqar mahimmanci, ana ta tallansa kafin ya fito wai shi (Dominki da Mijinki)"

.
Fatu ta waiwayo "Ok na Rabi Yusuf Maitama ko? A
gaskiya tana qoqari, da wuya ki ga ta yi littafi maras ma'ana, dubi dai wannan, ai wancan yana fitowa zan sa Mu'azzam Funtuwa ya turo min, ko wata likita sunanta Marnaf, ita ma tana da qoqari in dai abu ne na addini ... ya maganar auren malam da gaske din ne ko wasa? Don na ji maganar ta yi shuru ne"
.
Tala ta ajiye littafin gefe guda ta miqe tsaye tana gyara daurin zane "Ni ina ruwana? Ke ce amarya, in ya so ya auro Biyun ma gaba daya, na san dai ko waye ya auro dole dai ta dafa abin da zai ishe mu ni da 'ya'yana" Fatu ba ta gamsu da amsar da Tala ta ba ta ba, sai dai wannan bai baqanta mata rai ba don tana da tabbacin ita ma kishin ne gare ta, ba tsiyar da ba a kwasa ba lokacin da take amarya, kusan kullum sai an raba su dambe.
.
"Kai! Amma namiji ba dan goyo ba ne wallahi, sai ya gama kwande ka ya ce ka tsufa ya je ya dauko maka tsarar 'yarka, in ta zo ta kama daddaga maka kai ... amma ba komai ni wallahi zan iya zama da kowace shegeyar yarinya, don ba zan yarda a riqa ci min kashi a ka ba" in ji Fatu.

.
"Iye!"
"Qwarai kuwa"
"Kika ce qwarai"
"Tabbas"
"To da wa za ki yi?"
"Da kowa ma"
Fatu tana magana tana kallon fuskarta a dogon yaro "In mutum ya ce shi muganci ya sa a gaba ai kuwa shi ma ya san ba za a zauna lafiya ba"
.
Tala ta dawo ta zauna tana kallon Fatu tana dariyar qeta a ciki "Dan yayyafa mata ruwa" in jita, Fatu ta ba ta amsa "Au, ni fa na san abin da nake yi, ba wata wutar kishi da take cin zuciyata mutumin na ki ne bai da rahama a zuciyarsa ko kadan, yanzu in ban da muganci ba ki dubi yarinyannan yadda ta girma, ba don ma na tsaya sai ta gama karatu ba da yanzu an fara maganar aurenta, a zuwa yanzu kin taba ganin ya kawo wani abu wai don ya kusa aurar da ita?"
.
"Tabdijan!" In ji Tala "Ke kika san abin da yake yi? Wani namijiji ne zai nuna miki aljuhunsa? Kina ina zai rantse mana da Allah wai ba shi da ko sisi daga baya su Auwalu su ce mana sun gan shi yana cin indomie da qwai a wajen mai shayi? Ai namiji duk in da yake ki bar shi kawai"
.
Fatu ta fara fada tana daga
murya "Wallahi abin ma da rainin hankali a ciki, ta ya mutum kullun kana mana qaryar babu-babu muna haqura, sannan daga baya muji wai ka fara neman wata 'yar kucilar yarinya sa'ar 'ya'yanka? Ni wallahi ban ma san yarinyar ba ne, amma wallahi da na sa yara sun nakada mata dukan tsiya ko ma ni na tunkare ta da kaina, muga kuma me zai yi? Kulle ni zai sa a yi ko daukan mata fansa?"
.
Tala ta yi murmushi tana magana a hankali "Akwai yara fa a daki, ga Mari can ta shigo yanzu kuma kina sane, kibar wannan hirar kawai" ta miqe ta leqa waje ta kallo baranda, ta dawo ta zauna "Kin san yanzu maza ma sun lalace, su suke gulma da maqe, gogan naki yana iya fakewa da ruwannan ya tsaya a baranda yana jin
maganganummu, masamman ma namiji in ya so aure.
.
Fatu dai ba ta ce uffan ba, Tala ce take ta maganganunta ita kadai " Shawarata ki qyale shi kawai, duk bala'in da za ki yi wallahi kallon ki kawai zai yi, amma sai ya yi kayansa, ni ba wani da namiji da zai ce min wai ya yi alkawarin ba zai sake yin aure ba na yarda, wallahi ko dan sarkin Madina ne kuwa, ina ce qarshen imani dai kenan?"
.
Ban da yatsine ba abin da Fatu take yi, in dai za a tabo maganar kishiya, ko na maqwabta ta dinga fada kenan, to bare kuma a ce tata ce, Tala na yin shuru suka ji Malam Salisu yana kira, Tala ta miqe ta fita da gudu da hannu riqe da dankwali tana qoqarin sake daurawa.

Daga Muhammad Alkasim

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 19:46
In Hausa Novels
Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 3 Title : Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 3
Description : ALLAH YA ISA BAN YAFE BA! // 3 . "Don tsayanan" cikin tsawa "Kar ki jiqa min carpet a banza, yanzu sai ki sa dakin mutum ya...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 3"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ▼  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ▼  April (89)
      • Photos: Ga Abunda Yafaru Da Shi Bayan Yazagi Buhari
      • Photos: Dogara, Amaechi, Da Wasu Gwamnoni A Bikin...
      • Ina Bala'in Sonki
      • Photos: Matsalar Man Fetur: Bature A Cikin Bas
      • Labarin Wani Saurayi Mai Chatin Da Wata Budurwa
      • Photos: Sabin Hotuna Maryam Booth
      • Stella Oduah Ta Saci Naira Bilyan 3.6 - EFCC
      • Photos: Maciji Da Na Kashe A Kofar Gidan Mu
      • Photos: Yayin Da Biri Ya Ga Kyakkyawan Yarinya
      • Photos: Sarkin Kano Da Yar Shi
      • Photos: Sojoji Sun Kama Wasu Shugabannin Boko Haram
      • Dole Ne Yuguda Ya Bi Ka'idojin Jam'iyyar APC Idan ...
      • Babu Sanatan Da ya Rako Saraki Zuwa Kotun CCT A Yau
      • Me Ke Faruwa Tsakanin Tiwa Savage Da Mijinta
      • Photos: Aisha Buhari Ta Ziyarci Jihar Ibadan
      • Daga Hamsin Zuwa Biyu: Sanatoci Biyu Ne Suka Rako ...
      • EFCC Ta Gano Dala Bilyan 12.9 Na Makamai
      • Photos: Sojoji Na Ci Gaba Da Kakkabe Sansanin 'Yan...
      • Photos: Sabin Hotuna Adama Indimi
      • Uwar Gida Marigayi Mamman Shata Ta Rasu
      • Photos: Sabin Hotuna Zainab Indomie
      • Graphic Photos: Hmm..Wata Macce ta yakewa Mijinta ...
      • Za A Hana Bara A Jihar Sokoto
      • Zafin So Part 1
      • Mahassada Ne Ke Neman Bata Mini Suna - Sani Danja
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 6
      • Photos: Sabin Selfie Na Zahra Buhari
      • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
      • Wasu Al'ummar Nijeriya Sun Soma Kira Da A Rufe Maj...
      • Matar Shugaban Hukumar Shige Da Fice Ta Kasa Ta Wa...
      • Yan Daba Sun Yi Yunkurin Halaka Wani Matashi A Kano
      • Adesola Amosun Ya Dawo Da Naira Bilyan Biyu - EFCC
      • Graphic Photos: Masu Safarar Kaya Sun Illata Wasu ...
      • Video: Matasa Sun Jefi Sanata Isa Hamma A Garin Ni...
      • Photos: Sabin Hotuna Fatima Yola
      • Yan Danfara Na Amfani Da Suna Ali Nuhu
      • Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Ma'aikacin Mata...
      • Photos: Atiku Tare Da Matarsa A Wajen Bikin Dan Sa
      • Amurka Zata Maido Da Kudaden Abacha Najeriya
      • Amurka Zata Maido Da Kudaden Abacha Najeriya
      • Photos: Dan Atiku Abubakar Ya Auri Yar Ghana
      • Photos: Daga Wajen Bikin Littafin Aisha Buhari
      • As-Sheikh Muhammad Ayyub Limamim Masallacin Annabi...
      • Jihar Nassarawa Na Cigiyar Gwamnansu
      • Photos: Aisha Buhari Ta Ziyarci Jihar Borno
      • Sabon Hanyoyin Dan Yan Boko Haram Suke Kai Hari
      • Babu Laifi A Bashin Da Buhari Zai Ciwo - Garba Shehu
      • Yan Sandan Kaduna Sun Bindige Wani Matashi Dan Bun...
      • Goron Jumma'a Daga Mai Martaba Sarkin Bauchi (Dr) ...
      • Photos: Gwamna Jihar Bauchi Ya Ziyarci Shugaban St...
      • Hukuncin Zuwa Wajen Yan Duba
      • Abubuwa Da Kan Haifar Da Cutar Bugun Zuciya
      • Al'ajabi Part 23 {Karshe}
      • Al'ajabi Part 22
      • Al'ajabi Part 21
      • Al'ajabi Part 20
      • Al'ajabi Part 19
      • Photos: Boko Haram Sun Sake Sabin Hotuna Yan Mata ...
      • Daga Jama'a: Yau Na Gamu Da Abin Al'ajabi
      • Gajeren Tarihin Sheikh Jafaar Mahmoud Adam
      • Wacce Irin Nasiha Kike Wa Yar Ki Lokacin Aurenta
      • Sheikh El Zakzaky Da Zeenatu Suna Cikin Mawuyacin ...
      • Photos:Sabin Hotuna Yar Osinbajo Kiki
      • Photos: Buhari Ya Gana Da Yan Najeriya A China
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 11
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 13
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 12
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 10
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 9
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 7
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 4
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 5
      • Akwai Kyakkyawar Makoma Game Da Hadin Gwiwa Tsakan...
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 3
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 2
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 1
      • Majalisar Jihar Nassarawa Ta Tsige Membobinta Guda...
      • Photos:Buhari A Kasar China
      • Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Tabbatar Da Mutuwar Muta...
      • Fati Nijar Tayi Wakoki Wa Janar Burutai
      • Photos:Bayan Kwana Biyar A Amurka, Buhari Ya Iso N...
      • Al'ajabi Part 5
      • Mawaki Sani Aliyu Dandawo Ya Rasu
      • Real Madrid Ta Doke Barcelona Da 2-1
      • Azal Part 8
      • An Rantsar Da Muhammadou Issoufou
      • Azal Part 7
      • Kiran A Saki Zakzakiy Rashin Kishin Qasa Ne - Baba...
      • Photos: Faston Da Ya Binne Mutum A Tushen Gininsa ...
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger