1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog
  • Home
  • Arewa
  • News
  • Kannywood
  • Music
  • Videos
  • Islamic
  • Sport
» Hausa Novels » Al'ajabi Part 19

Al'ajabi Part 19

By Abdul Mk
Add Comment
Thursday, 14 April 2016


A maimakon na iya cika umarnin da daddy ke bani sai na tsaya ina binshi da kallo kawai, idan na dubeshi sai kuma na juya na dubi faruk dake tsaye ya kasa cewa komai na tbbtr kunnuwansa a bude suke yaji abnd zan iya yi.

Alkawarin dana daukarwa kaina na kasancewa da faruk a duk yanayin da yake ciki yasa duk wani tsoro yakau daga zcyta, ni ban wuce na tafi kmr yadda daddy ke cewa ba kuma bance komai ba har sai daya kara buga min tsawa a karona biyu.

“Ki wuce mu tafi nace“.

Maganar ta daki kwakwalwata, yaune karon farko da daddy ke daka min tsawa kai tsaye haka amma maimakon na firgita sai na kara gyara tsayuwa ma na tsaya kyam nace “daddy! ka dubi grmn Allah da manzonsa karkayiwa faruk haka, ka 2na sanda ya taimakemu ya rufa maka asiri kai kanka dani daduk danginmu, me yasa yanzu mu kuma ba zamu saka masa ba??

Idan wai don ni kakeyi don ka samar min da farin ciki ka rabani da wahala, to ka barni kawai sbd ni farin cikina anan gdn yake, faruk mijina ne har gobe kuma zan iya zama dashi a kowanne yanayi.“

Daddy ya zaromin ido yace “gsky na yarda baki da hankali, banda haukanki ina ke ina zama da nakasashshe makaho??

Abin kunyane ma ace kmr ni y‘ata mijinta makaho ne, abnd yayi mana a baya ya wuce mu gaba muke hange idan ke baki da 2nani mu muna dashi kuma bazamu bari wahala ta kasheki a banza ba, ki wuce nace!!“

Fuskata ta canja ma2ka naja da baya nace “Ina me baka hakurin cewa wlh ba inda zanje ba yadda za‘ai na tafi nabar gdn mijina wanda yaso ni sanda kowa ya gujeni yake kyamatata, kuma ba akan wani dalili ba.“

Cikin tsananin AL‘AJABI daddy ya bini da kallo yace “Ni kike gayawa haka??“

Ba tare da tsoro ba nace “Kayi hakuri amma ya zama dole in fadi hakan sbd kokoluwar butulci ne abnd kake so kuma banyi halacci ba idan nayi haka, na zabi na zauna anan har mu2wa tazo ta riskeni.“

Kin zabi wannan makahon akan mu iyayenki??

Daddy ya fada yana me nuno ni.

Na gyada kai nace “Eh! haka nake nufi sbd mijina ne ko a wajen Allah hakkinsa a yanzu yafi naku.
Hakanan dady yajuya yatafi tare da gargadin bani basu..
********************
faruk ne xaune abakin gado  yana tatunanin dani kaina bansan me yake tunawaba..
Gyaran murya yayi alamun yanason yace wani abu  naisaurin dago dakaina..yace HUMAIRAH.!! Nace na'am yace kishirya gobe zamuje gidanku."!
Yinme? natan bayeshi..zamuje muba dady haquri akan abin daya faru..
Da SAFE WAJEN KARFE 10;00 ranar asabr.....
Tsawon min2na talatin muka dauka sannan muka gama shirye-shiryen tafiya, abinda ya bani mamaki yadda faruk keyi tamkar zamu inda ba zamu dawo ba.

Bayan mun gama kuma yace na rufe duk wasu kofofin gidan na ko‘ina, cikin rashin fahimta nace “wai faruk ina zamu ne??

Ina tsammanin cewa kayi gdnmu zamu mu dawo??

Meye kuma na sai mun garkame kofofi??

Faruk yadan hade fuska yace “ba gdnku zamu ba siyar dake zanje inyi.“

Duk da yanayin da nake ciki sai da nayi dariya na kada kai tare da cewa “Ba haka nake nufi ba faruk abin ne kawai ke bani mamaki,“Na dan taka daga gbnsa izuwa kan kujerar da hijabina yake, na kara yin dariya a karona biyu nace “wai ka siyar dani, ashema zaka iya siyar da kanka kenan??“

Naja sandarsa muka wuce kai tsaye izuwa waje tare da cgb da hira har muka fito izuwa harabar gdn muka zarce izuwa inda motar faruk take, na budewa faruk kofar ya shiga na mayar na rufe tare da zagayawa na shiga na tuka motar muka tafi.

Ckn nishadi muke tafiya ina sanar dashi duk wani wuri da muka gifta ko wani abu daya faru dai-dai sanda zamu gifta, a haka har muka iso tsaleliyar katafariyar unguwar, SARAUNIYA STREET!!

makeken Allon dake kafe yayi mana maraba. 2n daga nan fuskata ta fara canjawa shekara daya curr kenan rabona da mahaifata na fara tuno rayuwar data faru dani a baya, na fara 2no lokutan baya sanda a wannan hanyar ake tukani a tsaleliyar mota, sanda nake takama ina fankama, nake ji da kaina.

Ba yanzu da rayuwa ta canja ni ta karfin tsiya ba. A hankali muka cgb da ratsa kyawawan gine-ginen dake hamshakiyar unguwar da duk wanda ka gani a cknta to ya wuce raini, har muka iso tsalelen gdn namu.

hmm... birki naci kawai a gbn gidan ina kallonsa, da ace wani zaizo wucewa yaga motar danake cknta da yadda na koma idan zanyi rantsuwa nan gdnmu ne bazai yarda ba.

A hankali na danna worn har sau uku a hankali karamar kofar ta bude me bude gate din yabi motarmu da wani wulakantaccen kallo naji sanda kasa-kasa yake cewa “Bafa kowanne talaka ke shiga gdn nan ba.“

Waye ne??

Ya tambaya.

Na sauke glass din motar a hnkl na leko da kaina waje, 2n kafin nace komai yaja da baya adan tsorace ‘ranki ya dade!!‘

Ya juya da sauri ya koma, jim kadan tafkeken gate din ya fara budewa.

Naja motar izuwa harabar gdn nayi parking tare da fitowa ina me bin harabar gdn da kll sashe zuwa sashe.

Abubuwa da yawa suka fara dawo min, duk inda na kalla sai wani abu ya fado min wanda faru a dai-dai wajen.

Idona ya ciko da kwalla.

Dai-dai lkcn ne faruk ya fito daga ckn motar wanda hakan ya dawo da hankalina gareshi na tako naja sandarsa muka nufi ckn gdn.

Ma‘aikatan gdn kuwa sunyi dandazo sai gaisheni suke duk wanda na gifta ta kusa dashi, wasu ma harna fara manta sunansu.

Da sallamarmu muka shigo tafkeken kayataccen falon, ba kowa sai hafsa y‘ar aiki tsaye a gbn plasma dake kafe tana y‘an goge-goge.

Ta amsa sllmr tare da juyowa muna hada ido ta dafe kirji, LAH! aunty humaira!.

Hajiya! Hajiya!!

Ga humaira tazo.

Da sauri momi tare da daddy suka fito, momi ta dubeta tace “meye??“

hafsa tayi nuni damu.

Dukkansu sukai turus suna kllnmu, momi ta dubi hafsa tace “To na gansu jeki.“

Hafsa ta ajiye duster dake hannunta ta juya tare dan dago min hannu tana murmushi, na gyada mata kai kawai ta fice.

Daddy wanda ya kllmu ya dauke kai yaci gaba da gyara maballin rigarsa lkc guda ya dago kai ckn tsawa yace “uban me kuka zo yimin a gd??

Meya kawo ku??“

Na dan kara matsawa gaf da faruk nace “ka fada masa abnd kace kazo ka sanar masa kawai mu tafi.“

Faruk ya gyara tsayuwa yace “Zuwa nayi don na sanar dakai abnd nasan dole sai kayi dariya, abnd nasan shi kake so kaji kuma shi kake so ya faru.

Insha-Allahu daga yau ka daina tsanata kuma komai yazo karshe.“

Faruk yaja hannuna izuwa kan kujera muka zauna.

Momi da daddy ma suka zauna kunnuwanmu duk a bude so muke kawai muji me faruk zai fada.

faruk yace “Alhaji na sani duk duniya ba wanda kake so kamar y‘arka guda daya wato humaira, sannan kuma ba wanda ka tsana kmr ni faruk sbd dalilai da yawa, musamman yanzu da dalili me karfi ya karu akan nada.

Banga laifinka ba don kana son kwatowa y‘arka yanci donta rayu ckn rayuwa me dadi da nayi 2nani ma sai naga hakika kafini gsky.

Nayi iya nazarin da zanyi na gano cewa zamana da humaira babu komai a ciki face takaici da damuwa....“

Na katseshi da karfi nace “FARUK!!“

ya daga min hannu da fadin ‘ HUMAIRA! minti daya.‘

ya dora da cewa “akwai cutarwa kwarai kmr yadda kake fada idan naci gaba da zama da humaira a haka kuma nima bazan so ta rayu har ta mu2 da bakin ciki ba don haka gata na dawo maka da ita har gida kmr yadda ka nema kuma zan tafi na.....“

Nayi saurin mikewa tsaye nayi dawurwura a guri daya naja da baya da sauri na fizgo wata sharbebiyar wuka na dan yanki hannuna kadan jini yayi tsartuwa kai tsaye na wuce da ita wuyana.

daddy da momi suka mike da sauri tare da zaro ido, momi tadanyi kara da fadin “iohhh!!!!! humai...“

Faruk ya mike tare da cewa “humaira me kika dauka??“

Ba tare da tsoro ba nace “WUKA!! wuka ce faruk! kuma zan kashe kaina idan har ka tafi ka barni.“

Ya tako izuwa inda yake jin motsina ya tsaya cak a gabana yace “Karkiyi haka!! duk tsananin tashin hankali da ukuba kada kiyi yunkurin kashe kanki domin tashin hankalin da zaki tarar yafi wannan, zaifi ki nemi wata mafitar amma ba wannan ba.

Ya miko hannunsa tare da cewa “bani wukar.“

Nabi fuskarsa da kallo wadda keda tasirin saurin sani ko hanani da kallo na saki wuka kasa na rike hannunsa nace “Karkayimin haka??

Nice fa humaira koka manta ne??

Kace ba zaka tafi ba don Allah kaji??

Kace da wasa kake faruk!!

Ya banbare hannuna daga nasa yaja da baya yace “bakin alkalami ya bushe ba yadda muka iya, don kin rabu dani ba yana nufin shikenan ba.

Kece dai humairar nan ta baya zaki samu wanda yafini kiyi rayuwar farin ciki.

Ki manta da ba2na kawai ki dauka baki sanni ba a rywrki ki shimfida sbwr ryw, nina tafi.“

Ya kai karshen maganar ya juya ya nufi hanyar fita...
Natausayama faruq..!
Koya rayuwanshi xata kasance..? Ko yararuwan ita humaira zekasance...? Sekucigaba da binmu
Dan samun sauran labarin.  sekashiga blue rubutunnan kayi like(y)

Facebook Twitter Google+ Pinterest Linkedin Whatsapp
Posted by Abdul Mk at 00:37
In Hausa Novels
Al'ajabi Part 19 Title : Al'ajabi Part 19
Description : A maimakon na iya cika umarnin da daddy ke bani sai na tsaya ina binshi da kallo kawai, idan na dubeshi sai kuma na juya na dubi faruk dake...
Rating : 5
Related Posts: Hausa Novels

LOVED WHAT YOU READ?! THEN DON'T MISS ANY NEW POST! STAY UP TO DATE! SUBSCRIBE NOW!
Join our Subscribers Today and Receive Updates by Mail. We totally hate spam. Your email address will not be sold or shared with anyone else.

Delivered by FeedBurner

0 Response to "Al'ajabi Part 19"

Post a Comment

← Newer Post Older Post ⇒ Home
Subscribe to: Post Comments (Atom)

Video Of Day

Popular Posts

  • Yanda Na Kama Mata Na Aisha Da Nafisa Suna Madigo
    INNALLILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. A cikin wani hali na takaici da al’ajabi wani magidanci, mai suna Abban Umma ya bayyana yadda ya ...
  • Download Music Komai wuya by Nura M Inuwa
    Click To Download Download
  • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
       Shahararriyar Jaruma fim din Hausa Aisha Aliyu Tsamiya ta sake sabin hotuna dan sabuwar shigan ta, a shafin ta na Twitter da instagram ...
  • Photos: Sabin Hotuna Nafisa Abdullahi
    shahararriyar Jaruma fim din kannywood Nafisah Abdullahi ta sanya sabin hotuna a shafin ta na Instagram
  • Mijinta Yana Kallon Hotunan Batsa (BLUE FILMS)
    Assalamu alaikum! mallam tambayace daga wata baiwar ALLAH take cewa: mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun ...
  • YAYANA MIJINA Part 1
    Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara kar...
  • ZURFIN CIKI BOOK 4**6
    Ta kyalkyale da dariya, ya Abba yayi santin ruwa, yyi murmushi, naji ne kman kinsa zuma, ya cire takalmashi tre ddora kafafuwanshi akan da...
  • Haramun Ne Mutane Su Kashe Wanda Ya Zagi Annabi - Malam Kabiru Gombe
    Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma shahararren mai wa'azin nan, Malam Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa Allah da faɗi Annabi Muhamm...
  • Ya Kamata Kowane Ma'aikaci Ya Auri Bazawara Daya - Shugabar Zaurawan Nigeria
    YA KAMATA KOWANE MA'AIKACI YA AURI BAZAWARA DAYA .....Inji shugabar Zaurawan Nigeria Shugabar kungiyar mata ZAURAWA ta Nigeria Hajiya ...

Facebook Page

ads 1

Ads 2

Powered by Blogger.
  • Home

Subscribe to 1Arewa TV



Like Our Facebook Page

Report Abuse

Search This Blog

Blog Archive

  • ►  2024 (11)
    • ►  August (5)
    • ►  June (2)
    • ►  April (4)
  • ►  2022 (2)
    • ►  March (2)
  • ►  2020 (28)
    • ►  August (9)
    • ►  July (14)
    • ►  May (2)
    • ►  March (1)
    • ►  February (2)
  • ►  2019 (4)
    • ►  November (3)
    • ►  October (1)
  • ►  2018 (762)
    • ►  September (2)
    • ►  August (2)
    • ►  June (70)
    • ►  May (98)
    • ►  April (48)
    • ►  March (408)
    • ►  February (127)
    • ►  January (7)
  • ►  2017 (1438)
    • ►  December (129)
    • ►  November (97)
    • ►  October (258)
    • ►  September (167)
    • ►  August (338)
    • ►  July (223)
    • ►  June (80)
    • ►  May (54)
    • ►  April (12)
    • ►  March (14)
    • ►  February (10)
    • ►  January (56)
  • ▼  2016 (1350)
    • ►  December (82)
    • ►  November (108)
    • ►  October (197)
    • ►  September (199)
    • ►  August (118)
    • ►  July (43)
    • ►  June (74)
    • ►  May (70)
    • ▼  April (89)
      • Photos: Ga Abunda Yafaru Da Shi Bayan Yazagi Buhari
      • Photos: Dogara, Amaechi, Da Wasu Gwamnoni A Bikin...
      • Ina Bala'in Sonki
      • Photos: Matsalar Man Fetur: Bature A Cikin Bas
      • Labarin Wani Saurayi Mai Chatin Da Wata Budurwa
      • Photos: Sabin Hotuna Maryam Booth
      • Stella Oduah Ta Saci Naira Bilyan 3.6 - EFCC
      • Photos: Maciji Da Na Kashe A Kofar Gidan Mu
      • Photos: Yayin Da Biri Ya Ga Kyakkyawan Yarinya
      • Photos: Sarkin Kano Da Yar Shi
      • Photos: Sojoji Sun Kama Wasu Shugabannin Boko Haram
      • Dole Ne Yuguda Ya Bi Ka'idojin Jam'iyyar APC Idan ...
      • Babu Sanatan Da ya Rako Saraki Zuwa Kotun CCT A Yau
      • Me Ke Faruwa Tsakanin Tiwa Savage Da Mijinta
      • Photos: Aisha Buhari Ta Ziyarci Jihar Ibadan
      • Daga Hamsin Zuwa Biyu: Sanatoci Biyu Ne Suka Rako ...
      • EFCC Ta Gano Dala Bilyan 12.9 Na Makamai
      • Photos: Sojoji Na Ci Gaba Da Kakkabe Sansanin 'Yan...
      • Photos: Sabin Hotuna Adama Indimi
      • Uwar Gida Marigayi Mamman Shata Ta Rasu
      • Photos: Sabin Hotuna Zainab Indomie
      • Graphic Photos: Hmm..Wata Macce ta yakewa Mijinta ...
      • Za A Hana Bara A Jihar Sokoto
      • Zafin So Part 1
      • Mahassada Ne Ke Neman Bata Mini Suna - Sani Danja
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 6
      • Photos: Sabin Selfie Na Zahra Buhari
      • Photos: Sabuwar Shigar Aisha Aliyu Tsamiya
      • Wasu Al'ummar Nijeriya Sun Soma Kira Da A Rufe Maj...
      • Matar Shugaban Hukumar Shige Da Fice Ta Kasa Ta Wa...
      • Yan Daba Sun Yi Yunkurin Halaka Wani Matashi A Kano
      • Adesola Amosun Ya Dawo Da Naira Bilyan Biyu - EFCC
      • Graphic Photos: Masu Safarar Kaya Sun Illata Wasu ...
      • Video: Matasa Sun Jefi Sanata Isa Hamma A Garin Ni...
      • Photos: Sabin Hotuna Fatima Yola
      • Yan Danfara Na Amfani Da Suna Ali Nuhu
      • Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Ma'aikacin Mata...
      • Photos: Atiku Tare Da Matarsa A Wajen Bikin Dan Sa
      • Amurka Zata Maido Da Kudaden Abacha Najeriya
      • Amurka Zata Maido Da Kudaden Abacha Najeriya
      • Photos: Dan Atiku Abubakar Ya Auri Yar Ghana
      • Photos: Daga Wajen Bikin Littafin Aisha Buhari
      • As-Sheikh Muhammad Ayyub Limamim Masallacin Annabi...
      • Jihar Nassarawa Na Cigiyar Gwamnansu
      • Photos: Aisha Buhari Ta Ziyarci Jihar Borno
      • Sabon Hanyoyin Dan Yan Boko Haram Suke Kai Hari
      • Babu Laifi A Bashin Da Buhari Zai Ciwo - Garba Shehu
      • Yan Sandan Kaduna Sun Bindige Wani Matashi Dan Bun...
      • Goron Jumma'a Daga Mai Martaba Sarkin Bauchi (Dr) ...
      • Photos: Gwamna Jihar Bauchi Ya Ziyarci Shugaban St...
      • Hukuncin Zuwa Wajen Yan Duba
      • Abubuwa Da Kan Haifar Da Cutar Bugun Zuciya
      • Al'ajabi Part 23 {Karshe}
      • Al'ajabi Part 22
      • Al'ajabi Part 21
      • Al'ajabi Part 20
      • Al'ajabi Part 19
      • Photos: Boko Haram Sun Sake Sabin Hotuna Yan Mata ...
      • Daga Jama'a: Yau Na Gamu Da Abin Al'ajabi
      • Gajeren Tarihin Sheikh Jafaar Mahmoud Adam
      • Wacce Irin Nasiha Kike Wa Yar Ki Lokacin Aurenta
      • Sheikh El Zakzaky Da Zeenatu Suna Cikin Mawuyacin ...
      • Photos:Sabin Hotuna Yar Osinbajo Kiki
      • Photos: Buhari Ya Gana Da Yan Najeriya A China
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 11
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 13
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 12
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 10
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 9
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 7
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 4
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 5
      • Akwai Kyakkyawar Makoma Game Da Hadin Gwiwa Tsakan...
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 3
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 2
      • Allah Ya Isa Ban Yafe Ba Part 1
      • Majalisar Jihar Nassarawa Ta Tsige Membobinta Guda...
      • Photos:Buhari A Kasar China
      • Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Tabbatar Da Mutuwar Muta...
      • Fati Nijar Tayi Wakoki Wa Janar Burutai
      • Photos:Bayan Kwana Biyar A Amurka, Buhari Ya Iso N...
      • Al'ajabi Part 5
      • Mawaki Sani Aliyu Dandawo Ya Rasu
      • Real Madrid Ta Doke Barcelona Da 2-1
      • Azal Part 8
      • An Rantsar Da Muhammadou Issoufou
      • Azal Part 7
      • Kiran A Saki Zakzakiy Rashin Kishin Qasa Ne - Baba...
      • Photos: Faston Da Ya Binne Mutum A Tushen Gininsa ...
    • ►  March (128)
    • ►  February (149)
    • ►  January (93)
  • ►  2015 (2312)
    • ►  December (182)
    • ►  November (308)
    • ►  October (389)
    • ►  September (198)
    • ►  August (182)
    • ►  July (211)
    • ►  June (216)
    • ►  May (239)
    • ►  April (187)
    • ►  March (116)
    • ►  February (54)
    • ►  January (30)
  • ►  2014 (7)
    • ►  December (6)
    • ►  January (1)

Labels

  • Al'ajabi
  • Arewa
  • Bollywood
  • Daga Jama'a
  • English News
  • Fadakarwa
  • Fadakarwa Labarai
  • family
  • Family related
  • Fasaha
  • Gida Nijeriya
  • Girke-girke
  • Hausa
  • Hausa Article
  • Hausa Film
  • Hausa HipHop
  • Hausa HipHop Music
  • Hausa Musi
  • Hausa Music
  • Hausa Novels
  • HipHop Music
  • Hollywood
  • Islamic
  • Kan
  • Kannywood
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai :
  • Labarai kannywood
  • Labari
  • Labari Al'ajabi
  • Labari. Gida Nijeriya
  • Labarin Siyasa
  • Labarin Wasanni
  • Labarun Duniya
  • Mu Sha Dariya
  • News
  • Nollywood
  • Photos
  • Rariya
  • Rayuwar Duniya
  • Sadarwa
  • Siyasa
  • Slider
  • Sports
  • Tafsir
  • Tarihi
  • Video

Main

  • Home

Populars

  • See How Every Premier League Teams Home Kit For 2024/25 Ranked
      The Premier League is not just a showcase of world-class football talent; it's also a platform for some of the most iconic and stylish...
  • Fatima Mai Zogale - Sabuwar Waka Rarara Ya Jawo Cece-Kuce
    Sabuwar Waka Rarara Me Taken Fatima Mai Zogale ya jawo Cece-Kuce a industry Kannywood Kalli wanna bidiyo domin Cikakken Bayanai Ga Bidiyon  ...
  • Suspect - Episode 1 ( Dj Giggs ft J Prince ft Nabs Kid) Hausa HipHop Ser...
  • Innalillahi wainna illaihin rajiun - Allah Yayi Wa Mawaki Aliyu Sharba R...
  • Abubuwa Goma Da Sadiya Haruna Ta Fada Akan Gfresh A Hiran Da Tayi Hadiza...
  • (New Music) Reason By Peevibes
      PeeVibes - Reason Williams Akinsola Precious Popularly known as peevibes has returned again with this mind blowing song tagged “Reason”. T...
  • Barrister Aysha Ahmad - Kira Da Babban Muryan ( Akan Fyade Da Cin Zarafi...
  • Yadda Kotu Ta Daure Bobrisky Watanni Shida Ba Tare Da Zabin Biyan Tara Ba
    Kotu ta daure Bobrisky watanni 6 ba tare da zabin biyan tara ba Babbar kotu a jihar Lagos ta yanke hukunci ga Idris Okuneye da a...
  • Bullying in Elite Educational Institutions: A Case Study from Abuja
    In the heart of Nigeria’s capital, Abuja, lies a stark contrast between the city’s opulent infrastructure and the troubling issu...
  • Bikin Aure Abubakar Bashir Maishadda Da Hassana Mohammad
     Ana Shirin Auren Furodusa Abubakar Bashir Maishadda da jarumar kannywood Hassana Mohammad Ga Zafafafa Hotunan Bikin youtubeem...

Navigation

social Media

Categories

Al'ajabi Arewa Bollywood Daga Jama'a English News Fadakarwa Fadakarwa Labarai family Family related Fasaha Gida Nijeriya Girke-girke Hausa Hausa Article Hausa Film Hausa HipHop Hausa HipHop Music Hausa Musi Hausa Music Hausa Novels HipHop Music Hollywood Islamic Kan Kannywood Kiwon Lafiya Labarai Labarai : Labarai kannywood Labari Labari Al'ajabi Labari. Gida Nijeriya Labarin Siyasa Labarin Wasanni Labarun Duniya Mu Sha Dariya News Nollywood Photos Rariya Rayuwar Duniya Sadarwa Siyasa Slider Sports Tafsir Tarihi Video
Copyright 2012 1Arewa || Hausa Entertainment and News Blog - All Rights Reserved
Design by Abdul Mk
Powered by Blogger